Chapter fourteen

629 64 0
                                    

samha ce ta dubi Amjad wanda duk yanayinsa ya canza da jin kalaman sabah tace mishi "Baby ka share shi kawai, karka bari kalaman sabah suyi tasiri akanka nasan yana fadin haka ne don kawai yaga ka tanka mishi amma kawai ka share shi kaji."

Amjad ajiyar zuciya yayi yace " babu komai, taho mu tafi". Haka suka karasa inda yayi parking motarsa suka shiga. Dayake rockview babu nisa daga makaranta, nan da nan suka isa. Amjad ya nuna tickets dinsu a gaban gate aka barsu suka shiga, suna shiga ciki dalubai suka tadda a cike cikin hall din. Daman tickets din da amjad ya siya na VIP ne, so a gaba shida samha suka samu wuri suka zauna, aka fara show din. Celebrities kala kala akayi inviting suka zo suna performing a gaban stage din. Cikinsu ma har da waenda samha bata taba ganinsu ba. Dalubai sai ihu sukeyi da ganin celebrities din. Samha ma ba karamin murna tayi ba dataga daya daga cikin mawakin da take yawan sauraronsa yana performing a stage. Funfair din dai ya hadu babu laifi.

Amjad mikewa yayi yace mata bari yaje ya siyo musu abunda zasu dan motsa baki dashi a stalls din dake baya. Tace mishi Toh shikenan. Yana barin wajen, samha na zaune ita kadai tana kallon performance din da akeyi a stage, sai taji kamar ana kallonta. Juyowar da zatayi kenan sai sukayi ido biyu da sabah wanda yake zaune a can gefen stage din tare da abokanansa, fararen idanun nan nasa masu matukar kyau ya kafeta dasu sai faman binta da kallo yake yi. Suna hada ido samha taji bugun zuciyarta ya karu, Itama kasa daine kallonsa tayi data ga irin kallon dayake mata koh kyaftawa baya yi.
Samha dana zuciyarta tayi tana kokarin kawo wa kanta nutsuwa game da yanda take ji a wanan lokacin. Sabah kashe mata ido daya yayi daga inda yake zaune ya daga mata hanunsa wanda yake daure da kyallen daya kwance daga jikin jakarta. Gashi duk kyallen ta bace da jini sai faman diga takeyi amma koh nuna alamun damuwa baiyi ba. Tabe baki tayi ta kawar da kanta gefe daga inda yake zaune. Bafi minti goma ba sai ga amjad ya dawo dasu lemu da cakes ya ajiye a kan table din dake gabansu.

"Sorry baby, kinga na jima koh? Ya tambayeta

Murmushi samha tayi sa'anan tace " koh kadan ai kuma naga kayi sauri".

Dariya amjad yayi ya bude musu lemun da cakes din suka fara ci. Haka suka cigaba da shakatawa a funfair din har akazo aka tashi. Bayan an tashi daga funfair din suka fito daga hall din sukaje inda amjad yayi parking motarsa, suka shiga amjad ya tayar da motar suka dau hanyar gida. Suna isa kofan gidansu amjad yayi parking. Samha ce ta dube shi fuskarta dauke da murmushi tace" gaskiya yau naji dadin fitan nan da mukayi tare ni da kai, na jima banzo funfair dauke da dimbin jamma'a ba irin wanan. Nagode baby" ta fada mishi tana dubansa.

Murmushi ya dan sakar mata sai kuma taga ya bata rai yana cewa " Nima naji dadin kasancewar mu tare a yau dinan amma akwai abunda nayi niyan na fada miki tun farko amma sai gashi sabah ya rigani" amjad ya fada mata yana dubanta.

"Me kenan?"ta tambayeshi.

" daman inaso na fada miki cewa kinyi kyau sosai yau dinan" ya fada mata.
Murmushi ta sakar mai sa'anan tace mishi "Nagode".
Murmushi shima ya sakar mata
Sa'anan yace "bayan haka akwai abu daya danake so na fada miki, dazun da kika zo kika tadda ni da sabah, ba abunda kike tunani bane ya faru. Ba wai yana cin zalin karamin yaron bane, a'a ya kama yaron yana abunda bai dace bane shiyasa kikaga yana mishi fada. A gabana komai ya faru". Amjad ya sanar da ita.

Nan take samha sai taji wani iri. "Dukda dai banso na fada miki ba saboda sanin halin sabah amma gani nayi ya kamata kisan Gaskiyar al'amarin." Amjad ya sake fada mata.

Shiru samha tayi tana nazari sa'anan ta danyi murmushi ta soma fadin "babu komai kuma Naji dadi daka sanar dani asalin abunda ya faru, kuma na gode. Ta fada mishi. Hira suka danyi a tsakaninsu sa'anan sukayi Sallama ta fita daga motar ta shiga cikin gidansu.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now