Chapter five

681 81 1
                                    

Tunda ta je tayiwa sabah kashedi har yinin ranar bata sake jin duriyar sa ba.
Har ta fara tunanin ko ya dauki maganarta da gaske ne ya fita harkarta. Da wanan tunanin ta yini ranar tana farinciki har tagama lectures ta koma gida.

Washe gari da wuri ta shigo school da safe tana shiga ajinsu bata tadda kowa ba don ko su khadija basu iso ba.
Ta nema wuri ta zauna ta fara bude littatafanta tana nazari.

Bayan yan mintuna taji shigowar mutum cikin ajin, dagowa tayi taga amjad ne ya shigo. Suna hada ido, bata san sanda ta sakar masa murmushi ba shima ya mayar mata, haka ya karaso yazo ya zauna kusa ita suka gaisa.
Taji zuciyarta kamar ta narke jin amjad kusa da ita. Farin cikin rayuwarta.

" nazari kikeyi?" Taji Ya tambayeta.

Tace mishi "eh ina dan duba maths din dr kabir ne, kasan tests dinshi ya kusan matsowa."

Murmushi amjad yayi yace " ai kam test dinshi ya kusan matsowa, naji class rep yana cewa kamar cikin satin nan za ayi fixing".

Zaro ido samha tayi tace "cikin satin nan?, ai wlh ban gama iya solving din calculations din daya bamu ba. Tun jiya naketa fama".

"Ina yake baki matsala let me see if i can explain it to you" ya tambayeta.

Ciro lecture note dinta tayi daga cikin jakarta ta bude ta fara nuna mishi inda yake bata matsala. Nan ya fara mata bayani dalla dalla yanda zata fahimta. Dadi ta dinga ji yana ratsa ta don yanda yake mata bayanin yasa ta kara fahimtar course din sosai. Suna cikin haka su khady suka shigo cikin ajin suka tadda su.
Bude baki sukayi cikin mamaki da sukaga amjad da samha suna zaune tare. Samha ta musu allama da ido da suyi shiru su wuce karsu ce komai. Don ita bata son amjad ya fahimce komai.
Karasowa su khady sukayi suka gaisa da amjad din suka nima seat a bayansu samha suka zauna cike da mamaki.

Ba jima ba Lokacin lecture dinsu yayi, lecturer din ya shigo ya fara koyar dasu. kusan two hours suka dauka suna lecture din daga bisani lecturer din ya gama ya sallamesu aka tashi a ajin.

Amjad ne ya juyo ya tambayeta ko zata sauka kasa zuwa cafetaria. Jikinta na rawa tace mishi eh zata je. Yace mata toh bisimillah su tafi tare.
Ta juya inda su khady suke zaune a baya suna binsu da kallo ta ce musu ita da amjad zasu je cafeteria, suka ce mata toh su fara tafiya suma idan sun gama notes dinsu zasu taho.

Tare suka bar ajin ita da amjad suka fara sauka kasa. Dai dai wurin notice board taga dalubai sun tsatsaya ana kallon abun da aka mana a board, sai dariya kowa keyi. Tace wa amjad kamar fa akwai notice da aka manna suje su duba board din. Suna karasowa nan kallo ya dawo kansu, daluban suka fara nuna su da hannu suna dariya.

Abun ya daure wa samha kai don bata fahimce abunda sukewa dariya ba, haka ta kusa kai cikin jamma'ar taje ta ga wa idanunta abunda ke faruwa.

Mutuwar tsaye tayi data ci karo da abunda aka manna a board. Letter dinta ne qiriqiri tagani manne a jikin board din, harda hoton ta dana amjad an manna kowa na gani.
Amjad ma yazo ya tsaya kusa da ita a gaban board din.Ganin letter din dayayi da sunansa a rubuce harda hotunansu yasa kanshi ya daure ya juyo yana kallon samha cike da mamaki.

Samha kuwa tama rasa yanda zata yi, ji take kamar kasa ta bude ta shige don kunya. zuciya ce ta dibeta bata san sanda ta kwasa a guje ba, students din kuwa sai dariya suke ta faman yi mata. Amjad ganin ta kwasa a guje ya soma kwala mata kira yana kokarin binta amma inaaa ko sauraronsa batayi ba ta cigaba da gudu hawaye na gangaro mata a fuska.

Har su khady ta gani a hanya suna kokarin tsayar da ita, bangaje su tayi ta cigaba da gudu kamar wata zarariya.
Wuri daya tasa a rai da niyan zuwa kuma mutun daya zuciyarta ke hasko mata da taje ta tunkara. Tasan babu wanda zai mata wanan ta'asar in ba sabah ba.
Cikin yan mintuna sai gata a department dinsu, kai tsaya inda ya saba kebewa da abokananshi ta nufa, ai kuwa ta ci sa'a ta sameshi zaune yana hira dasu. Tana isowa bata tsaya watawata ba ta daga hannu ta sakar masa lafiyayun mari har guda biyu a fuska. Koh shakka bata ji ba.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now