Chapter fifteen

659 74 0
                                    

Suna shiga cikin dakin da aka kwantar da samha suka ganta kwance duk jikinta yayi weak. Karasowa sukayi ciki suna mata sanu, ita kam binsu da kallo takeyi daya bayan daya.
Alhaji muazzam ne ya matso kusa da ita yana tambayarta ya jiki " haba samha, yanzu duk kewar amminki ne haka? Ai da kin kirani a waya kince nazo na dauke ki" alhaji muazzam ya fada mata yana murmushi.

Samha binshi da kallo ta dinga yi bata ce komai ba don har yanzu bata gama dawowa cikin hayacin ta ba. Bacci ne ya sake debanta.
Alhaji muazzam ya kale likitan yace kace zamu iya tafiya da ita gida koh? Na fison ma mu wuce gida da ita, don nasan a gida zata fi samun ishashen hutu."

"Eh zaku iya tafiya, bari na kira nurse tazo ta duba mata drip din kuma ta bata alura. Yanzu zan shiga ciki na rubuta muku takardar sallama." Yana gama fadin haka ya fita ya barsu a dakin.

Wayar alhaji muazzam ne ya soma ringing, ya ciro wayar daga cikin aljihu yaga Anty fanneh ce ke kiransa, daga wayar yayi ya kara a kunansa. " ya ka samu ka isa gidan kuwa, tana cikin gidan?" Ta watso mai tambaya.
Ajiyar zuciya yayi ya soma mata bayanin abunda ya faru da yanda yaje ya riske ta, har ma suna asibiti amma ta farfado yanzu za sallamesu su wuce gida. Ba karamin tashin hankali anty fanneh ta shiga ba jin samha tana kwance a asibiti. Alhaji muazzam ne ya dinga kwantar mata da hankali yace ba wani serious abu bane kawai stress ne ya mata yawa. Amma yanzu zai tafi da ita gida, musamman zai sa family doctor dinsu ya zo yana dubata a gida. Ajiyar zuciya anty fanneh tayi data ji cewa samha ta farfado kuma ba wani serious abu bane don tasan samha batada wuyan suma. Tun tana karama Koh rashin lafiya take ta dinga faman suma kenan, saboda jikinta baya iya daukawa. Anty fanneh tace ma alhaji muazzam ya kaita gidansu kawai yana sa mata ido har zuwa ran da zata dawo don tana sa rai sai jibi bayan sadakan uku zata dawo gida. Alhaji muazzam yace babu matsala, kar ta samu damuwa ai samha tamkar yar shi ce zai kula da ita sosai. Godiya anty fanneh ta mishi sa'anan ya kashe wayar.
Koh da drip din ya kare, aka sallamesu, samha sai faman bacci takeyi cikin mota har suka isa gida. Lami ce ta taimaka aka kai samha daki aka kwantar da ita. Alhaji muazzam ya kira likitanshi dr fahad daya zo ya sake duba mishi ita. Dr fahad yazo har gida ya sake duba ta yace lafiyarta lau, idan ta tashi washe gari zata jita garau. Alhaji muazam ya mishi godiya sa'anan ya sallameshi.

Washe gari sai zuwa yamma samha ta farka, don ba karamin bacci tasha ba. Tana bude idanunta ta tsinci kanta cikin wata bakuwar daki. Mikewa tayi ta fara bin dakin da kallo, ko ina a dakin tsab tsab. Kana ganin yanayin dakin kasan ba na karamin gida bane. Saukowa tayi daga kan gadon tana kokarin tuno abubuwan da suka faru a jiyan. A ina nake kuma? Ta tambayi kanta. Karasawa tayi inda kofa yake ta bude a hankali ta fita daga cikin dakin. Taga wani hadadiyar matakala da zai kaita zuwa kasa. Bin matakalar tayi ta soma saukowa ahankali tana bin ko ina na gidan da kallo don kana ganin yanayin gidan kasan ba karamin kudi aka kashe wurin kayace ta ba. saukowa tayi ta karasa cikin fallon taga wani mutum zaune a kan kujera yana kallon tv.

Mutumin yana jin alamun shigowar mutum cikin fallon ya juyo yaga samha tsaye tana kallonsa. Samha kam data ga mahaifin sabah a zaune, zuciyarta ne ta fara bugu da karfi " kar dai gidansu sabah nake? Me ya kawoni gidansu kuma" ta tambayi kanta.

Alhaji muazzam yana ganin samha ya mike cikin sauri yazo ya tadda ita fuskarsa dauke da fara'a " samha har kin tashi? Ya jikin naki? Ya tambayeta.

Binshi da kallo da dingayi daga bisani ta bude baki ta soma fadin " da sauki, a ina nake?" Ta tambayeshi.

" au wai nan kike nufi? Kina cikin gidanku  ne mana. Daga yanzu ki dauka tamkar nan ma gidanku ne kina jina koh. Zaki iya shiga ciki ki dauki duk dakin da kikeso a cikin gidan nan babu matsala ?" Mahaifin sabah ya fada mata cike da dauki.

Zaro ido tayi tana fadin " Gaskiya a'a, ina ammina nidai gaskiya ka mayar dani gida wajen ammina " ta fada mishi tana kokarin neman hanyar waje.

"Haba samha meyasa kike haka,  ai Amminki ce tace na kawoki nan gidan tunda bakida lafiya kuma ita bata nan babu mai kula dake a can gidan naku." Nan ya zayane mata duk abunda ya faru jiyan. Ajiyar zuciya tayi itama abubuwan da suka faru jiya suka soma dawo mata.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now