Chapter Thirty- seven

457 48 1
                                    

Sabah zaune yake a office din chief security officer. Chief security officer din ya tasa shi a gaba sai faman mishi tambayoyi yake. Ga dr Sageer nan tsaye a gefe yana jinsu.

"Sabah meyasa ka aikata hakan? Ko kana tunanin hakan zai saka kaci wanan scholarship din kai kadai ne?"

Sabah ya sake ajiyan zuciya sa'anan ya dago yana duban officer din yace " haba sir, sai kace banida hankali? i'm not that dumb ai dazanyi amfani da wanan method din".

"Kai ka iya bakinka, bar gani kamar kaine yaron VC din makarantar nan kana ganin kamar zaka iya karya doka a kyaleka. Kasan irin bad reputation da hakan zai janyo wa makarantar nan kuwa? Toh idan ba kaine ka aikata ba toh waye?"

" Ban sani ba, wanda yakeson yaga baya na ne zai aikata hakan". Sabah ya fada mishi kai tsaye.

Dr Sageer dake tsaye can gefe ya karaso fuskarsa dauke da wani irin shu'umin murmushi yace "toh wake son yaga bayanka Sabah?"

Wani irin kallo Sabah ya watsawa Dr Sageer sa'anan ya bashi ansa da "duk ma wanda yayi framing dina nasan yanzu yana can yana jin dadi don yana ganin bukatansa ya biya"

Dr Sageer ya jinjina masa kansa sa'anan yace "wato Saba har yanzu kana nan da girman kan nan naka dana sanka dashi baka canza ba".

Officer din ne ya juya yana duban dr Sageer sa'anan yace "dr, daman kasan yaron nan sosai ne?"

Dr Sageer ya dan nesa sa'anan ya bashi ansa da " yes, a da can baya kafun na fara lecturing, nine assistant din VC. Kuma ina yawan zuwa gidansu sosai. A idanuna Sabah ya girma, don komai na childhood dinsa duk na sani".

Sabah na jin abubuwan dayake fadi ya hada rai, ya kawar da kansa gefe kamar ba maganarsa akeyi ba.

Suna cikin haka, sai ga Alhaji Muazzam nan yayi sallama ya shigo cikin office din, chief security officer na ganinshi ya mike nan da nan suka gaisa ya soma fadin "sir, daman inaso nazo nayi reporting wanan case dinne muna gama investigation."

Alhaji Muazzam yace mishi "no don't worry, karka damu an rigada anyi briefing dina tun a office".

Officer din jiki na bari yayiwa Alhaji Muazzam nuni da kujera daya zauna. Alhaji Muazzam yaje ya zauna yana fuskantar dan' nashi.

Sabah na ganin ya shigo ya kara hada rai kamar hadari ya taso. Dr sageer ne ya matso inda Alhaji Muazzam yake zaune ya soma fadin "Sir, anyi deciding akan punishment din da za'ayi ne akan wanan case din?"

Alhaji Muazzam ya dago yana dubanshi sa'anan yace "ba kama mai laifi ba taya kuma za yanke hukunci har da purnishment?"

Dr Sageer yayi sauri ya hadiye abunda ya taso masa don yasan halin VC din sarai, da wuya yayi wani abu akai don kwata kwata baya san laifin dan' nasa. Wani irin kallo Dr Sageer ya watsawa Sabah, shima Sabah ya dago yana dubansa suka hada ido.

Alhaji Muazzam ya juyo yana duban Sabah sa'anan ya cigaba da fadin "karka damu Sabah, duk wanda ya aikata hakan bazai jima a boye ba. Za'a kamashi kaji koh".

Sabah ne ya sake dagowa yana duban Dr Sageer sa'anan yace "ai daman ban damu ba". Ya fada still idanunshi kyam akan dr Sageer.

Alhaji Muazzam ya juyo yana duban Dr Sageer da chief officer din yace "Dan Allah a kokarta, ayi hanzari a kama duk wanda ya aikata wanan laifin."

Babu yanda suka iya kuma bazasu iya musanta mishi ba suka bashi ansa da "okay sir"

Chief security officer dinne yace bari yaje yayi musu magana a investigation room. Yana fita Alhaji Muazzam ya juyo yana duban Sabah sa'anan yace "Sabah zaka iya komawa class ka cigaba da lectures dinka".

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now