Chapter fifty- four

396 47 0
                                    

Ajiyar zuciya ya sake sa'anan yace "toh me kikeso nace miki Aliyah, naga kamar har yanzu you've not gotten over Sabah. Har yanzu kina sonshi koh?"

Shiru Aliyah tayi ta kawar da fuskarta gefe, don bata san ansar da zata bashi ba. Tasan gaskiya ya fadi, don ita dai a baki ta hakura da Sabah amma can kasar zuciyarta tasan bazata taba daina sonshi ba.

Haka suka karasa sauran tafiyan, kowansansu yayi shiru da abunda yake masa yawo a zuci.

Samha dake zaune a gefe ta wurin window tayi zurfi cikin tunani, karan bike din Sabah taji dab da window dinsu, cikin sauri ta leko ta ganshi yana tafe dab dasu, idanunsu ne suka tsarku cikin junansu, ya kura mata kyawawan idanunsa yana kallonta har na dan tsawon minti biyu daga bisani ya karawa bike dinsa wuta, ya wuce su.

Jikin Samha ne ya kara yin sanyi, ta rasa ma inda zata sa kanta taji dadi don kwata kwata bata son hakan yana faruwa tsakaninta dashi.

Suna isa camp garden, inda zasuyi hiking dinsu. Daidai wurin gate din bus dinsu ya tsaya yayi parking, suka soma saukowa daya bayan daya.

Already Sabah shi ya rigada ya rigasu isa, don haka suna shiga ciki suka ci karo dashi.

Tsaye yake rataye ta jakansa a kafadarsa, Samha tana ganinshi taja birki ta tsaya tana kallonsa, shima ido ya kura mata.

Aliyah ce ta karaso inda yake tana murmushi tace mishi sauran yan team fa sun rigada sun fita har sun soma shirye shiryen workout din da zasu yi. Itama yanzu zata je tayi joining dinsu.

Sabah ya danyi shiru yana dubanta sa'anan yace "toh shikenan, ki jirani. Bari na shiga ciki na ajiye jakana tukuna".

Aliyah ta gyada masa kanta tace "toh".

Har ya soma takowa zai wuce ciki, Madina tazo ta tareshi tana murmushi tace "Sabah bari na tayaka rike jakanka".

Shiru yayi yana kallonta daga bisani ya dawo da dubansa ga Samha suka hado ido.

Ciro jakar yayi daga kafadansa, Madina har ta mika hannu zata karba taga ya mikawa Samha jakan yace "Samha, ungo shiga mun da wanan ciki".

Jiki babu kwari Samha tasa hannu ta karba, idanunta akan Madina wace taja jinin jikinta, Gabadaya Samha sai taji babu dadi.

Juyawa tayi ta soma kokarin shiga ciki taje ta ajiye mishi jakan.

Shi kuma ya juya tare da Aliyah suka soma tafiya.

Madina bata dadara ba, still tabi bayansu ta soma kwalawa Sabah kira.

Tsayawa yayi cak sa'anan ya juyo yana dubanta harta karaso.

Itama Samha tsayawa cak tayi jin ta kira sunan Sabah sa'anan ta juyo tana dubanta .

Madina fuskarta dauke da murmushi ta soma fadin "daman Sabah inaso nayi maka godiya akan yanda ka fada mun gaskiya ranan, naji dadi kuma nagode kwarai da gaske".

"Bakiji haushi ba kenan?"

Ta girgiza masa kanta tana murmushi tace "ko kadan. Ai duk laifi nane, bai kamata nazo na tareka da irin wanan maganar ba, kuma daga baya na zauna nayi dogon tunani akai kuma na gano wani abu".

"me kika gano?" Sabah ya tambayeta.

"Na gano cewa, idan har kana son mutum it's impossible to hide your feelings, dole zai bayana, haka zalika ma idan baka son mutum you can't pretend or force yourself to like that person, so rejecting me was the right thing to do. Thanks for not letting me have my way."

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now