Chapter Eleven

574 89 0
                                    

Samha ta zaro ido tana girgiza mata kanta alamun karta mata haka. Kwalla ya ciko mata idanunta. Murmushin mugunta Aliyah ta cigaba dayi. Ta kamo karshen gashin samha zata hada da lighter din kenan kamar daga sama sukaji an watso musu ruwa.
A firgice suka juyo sukaga wani mutum rike da bokiti da mop a hanunsa. Da alamun daya daga cikin masu sharan makaranta ne.

"Meye kuke haka?" Ya tambayesu yana kallonsu daya bayan daya.

Shiru sukayi basu ce komai. Aliyah sai faman galla masa harara takeyi. Kare musu kallo yayi sa'anan yace .

"Badai cin zali kukeyi ba. Me ta muku da zaku kamata ku daure haka?" Ya tambayesu.

Ya juyo ya dubi Aliyah sa'anan yace " keh kuma kyakyawar yarinya kamar ki amma zuciyar ki babu kyau? Konata zakiyi?"

Daya daga cikin yan matan ne tace " kai tsoho ina ruwanka. Bamu san surutu, ka wuce ka bamu wuri kaje ka cigaba da aikin sharanka. Ta fada mishi cike da fitsara.

"Ni kike ce ma tsoho, toh bari inje in kira daya daga cikin malaman naku suzo su ga abunda kuke aikatawa.

Aliyah ce ta juyo tana kallon samha sa'an ta fada cikin kakausar murya "kin ci sa'a yau dinan da kinga abunda zan miki. Amma next time zamu sake haduwa. Kuma haduwar tamu bazatayi kyau ba." Tana gama fadin haka tayiwa yanmatan alamu dasu bar wajen. Haka suka tafi suka kyale samha wace hawaye ne ke ta gangaro mata bisa kunci.

Nan da nan mutumin yazo ya kwance igiyar dasu aliyah suka daure ta dashi daga hanunta. Hakuri ya soma bata yana rarashinta. Kallon mutumin samha keyi gani takeyi kamar tasan fuskar a wani wuri. Godiya ta mishi ta share hawayenta. Suna cikin haka samha ta jiyo takun mutum aka zo aka tsaya a kansu. Dagowa tayi taga sabah fuskarsa a daure.

"Abba ya haka?" Samha taji ya tambaye mutumin. Cike da mamaki samha ta kalli sabah sa'anan ta sake dawo da dubanta ga mutumin.

"Haba baby boy dina, dan na danyi tafiya na kwana biyu kuma koh oyoyo baza ayi wa daddy ba" ya tambayeshi.

Sabah ya bata rai ya kawar da kansa gefe. Samha kam kallon kallo ta fara binsu dashi. Kardai wanan mutumin shine mahaifin sabah. Wanan tunanin na fado mata, da sauri ta juyo ta kura wa mutumin ido. Nan da nan kuma taga kamanin dake tsakaninsu. Shiyasa jikinta yayita bata kamar ta sanshi  a wani wajen. Ashe kamanine kawai. Mutumin kyakywa don daga ganinshi kasan yayi tashen kyau lokacin yana yaro. Komai nasu iri daya da sabah, haske ne kawai sabah ya fishi. Amma kana ganinsu tare, kasan mahaifinshi ne.

"kaine mahaifin sabah?" Samha ta tambayeshi. Gyada mata kai yayi fuskarsa dauke da murmushi.

Sabah ne ya dubeshi sa'anan yace " Abbah dan Allah wani irin shiga ne kayi yau. Yanzu wani ya ganka basai yazata kai cleaner din makarantar nan ne ba. Duba fa harda bokiti da mop ka ruko". Sabah ya tambayeshi cike da takaicin yanayi mahaifin nasa. Ya rasa gane meyasa yake abubuwa haka.

"Haba baby boy, meye acikin shigar danayi yau. Na jima banyi cleaning bane shiyasa nace bari na gwada yau."

" a cikin makaranta kuma abba zaka gwada?" Sabah ya tambayeshi.
Gyada mishi kai mutumin yayi yana murmushi. Duk wanan da sukeyi samha kallonsu kawai take ta faman yi cike da mamaki, musamman mahaifin sabah din. Anya mutumin nan nada lafiya kuwa, ta tambayi kanta. Yanzu wanan ne amminta zata aura? Jibi yanda yakeyi kamar wani yaro karami.ta tambayi kanta.
Tana cikin wanan tunanin taga wani mutumi sanye cikin suit ya karaso inda suke tsaye.

Cike da girmamawa ya dubi mahaifin sabah sa'anan yace " sir, tun dazu muke ta nemanka bamu ganka ba, har wayarka mun kira bata shiga, akwai meeting da za ayi yau a senate, don tun hazu har an taru  kai kawai ake jira" mutumin ya sanar dashi.

"Au kaga fa na manta da wani meeting da za ayi yau. Toh bari na shirya muje. Ka kira jubril a waya kace yaje mota ya ciro mun daya daga cikin sababin suit dinan ya kai mun office gani nan zuwa". Ya sanar da mutumin.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now