Chapter sixty

459 53 0
                                    

Suna shiga cikin motar ya tayar, wani irin sanyin kamshi ne taji ya bugi hancinta.

Sabah ya dubeta yace "kisa seat belt dinki."

Babu musu ta janyo seat belt din ta makala sa'anan yaja suka soma tafiya.

Kwatancen gidansu ta soma yi masa sai yaga ma basuda nisa da juna don avenue daya ce ta rabasu. Bai sake ce da ita komai ba kawai gani tayi yabi dasu hanyar awolowo road. Can island suka nufa ya kaisu wata babbar creamery inda ake siyar da kayan makulashe don ya lura da ita tana son kayan zaqi sosai.

Kokarin jansa da hira takeyi, tun baya bata ansa har yazo ya soma da'an sakin jiki da ita suna hira harda dariya.

Gabadaya Sabah yaji company dinta is not boring kamar yanda yake tunani. Yaga she's a very free person batada matsala sai dai yaranta dayake da'an damunta.

Don tana ganin wani wuri da ake siyar da Ice cream tasa tsalle tana tafi kamar wata yar karamar yarinya tana fadin"wow Sabah kaga wancen ice cream din? Ban taba ganin ice cream mai tsawo irin wanan ba. Ko a sudan ban taba gani irinta ba".

Dariya kawai Sabah yayi sa'anan suka karasa inda ake siyar da ice cream din yayi musu order suka samu wuri suka zauna suka soma sha suna hira.

Suna gama shan ice cream din, Sabah ya dubeta yace "kin taba zuwa bakin ruwa?"

Madina ta girgiza masa kanta tace "rabona da bakin ruwa tun ina karama".

Sabah ya mike yace "toh taso muje."

Mikewa tayi tabi bayansa suka shiga mota ya kaisu zuwa bakin ruwan.

Madina tana saukowa daga motar a guje ta soma karasawa wurin ruwan, iskan wurin na ratsa ko ina na jikinta.

Har tayi nisa sai kuma ta sake dawowa ta kamo hannun Sabah ta soma janshi suna gudu tanai masa dariya don Allah Allah takeyi taje bakin ruwan.

Dab da bakin ruwan suka tsaya, ita kam sai faman bin ko ina takeyi da kallo tana murmushi.

Shikam Sabah shiru yayi yaje ya nema wuri a gefe ya zauna ya kura mata ido yana kallonta.

Takai kusan 10mins a hakan tana kallon ruwan da kuma jiragen da suke yawo akai. Juyowa tayi ta gansa zaune a gefe, cikin sauri ta karaso inda yake ta soma fadin "Sabah, larabci na ya soma kwari yanzu bari kaji. Lumshe idanunta tayi a hankali sa'anan ta soma fadin "qalbi yurid sabah wa'yurid 'an 'akun maeah 'iilaa al'abad"

Sabah shiru yayi ya tsura mata ido yana kallonta, don ya gane sarai abunda take nufi don tun suna kanana mahaifiyarsu take musu larabci amma yayi fuska yace "me kenan kike nufi? Ban gane ba. Nifa bahaushe ne, gwanda kimun da hausa yanda zanfi ganewa".

Madina tayi murmushi tace "ina nufin zuciyata tana son Sabah kuma tana son ta kasance tare dashi har Abada".

Murmushi kawai Sabah yayi yana Girgiza kansa.

Madinah tace "kaga na iya kunshi, wanan ma ni nayi da kaina". Ta fada tana nuna masa kunshin hanunta.

Sabah ya tabe baki yace "na gani, kin da'anyi kokari".

Madina ta turo baki tace "toh girki fa? Kaga na iya abinci kala kala. I know how to cook coconut fried rice with seasoned beef. Kai wane ka iya?" Ta tambayeshi tana dariya.

Sabah yace "oho nidai ci nakeyi. Ina ruwana da wani girki".

"Toh ko kanaso na girka maka? Me kake son ci?"

"Kin iya dafa fasolia baida?"

Madina tayi shiru tana nazari daga bisani tace "ai ban ma taba jin sunan ba".

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now