Chapter sixty-Nine

422 55 1
                                    

Zatayi magana, sukaji muryan Sabah ya fito yana fadin "Samha bake kika daura ruwan zafi a wuta yanata tafarfasa?"

Cikin sauri Samha tace "Ammi Allah ya kiyaye hanya kuma ya saukeku lafiya, zan kiraku idan kun isa, bari naje na duba abunda na daura a wuta".

Ammi cike da sanyin jiki tace "toh, ki kula".

Daga mata hannu Samha tayi sa'anan suka karasa cikin mota itada Abba, driver yaja suka tafi.

Cikin sauri Samha ta koma cikin gidan, ta karasa cikin kitchen Sabah na biye da ita a baya.

Tunda su Anty Fanneh suka bar gidan ta kasa samun nutsuwa a cikin zuciyarta gabadaya hankalinta a tashe yake, Abba ne ya lura da yanayinta yace "yadai Fanneh? Ya na jiki shiru tunda muka baro gida ko bakida lafiya ne?"

Murmushi Anty Fanneh ta kirkiro tace mishi babu komai.

Bangarensu Samha kuwa, tsaye take cikin kitchen sai faman yanke yanke takeyi.

Sabah na zaune a parlour yana kallon wani tasha a Tv, shiru parlourn babu abunda kakeji sai sanyin Ac dake tashi a parlourn.

Jin shirun yayi yawa ne yasa ya waiga ya hangota cikin kitchen ya soma kwada mata kira yace "keh... wai me kikeyi cikin kitchen dinan ne tun dazu?"

"Dinner nake kokarin hadawa". Ta bashi ansa kai tsaye sa'anan ta cigaba da abunda takeyi.

Juyawa yayi ya kalli agogon bango yaga sha biyu saura. Remote din dake hannunsa ya jefar a gefe sa'anan ya mike ya karaso cikin kitchen din, yana isa ya kamota ya juyo da ita yana nuna mata agogo yace "duba lokaci, it's just 12pm and you're making dinner?"

Harara ta dan watsa mishi hade da tureshi gefe tace "ni ka rabu dani, yanzu nakeso na hada dinner din". Juyawa tayi ta cigaba da yanke yanken nata.

Ajiyar zuciya ya sake ya juya ya soma tafiya hade da fadin "zo nan"

"Mene?" Ta tambayeshi.

"Cewa nayi kizo! ko baki jine?"

Tsaki ta buga sa'anan ta ajiye wukar ta biyo bayanshi suka shigo cikin parlourn tana watsawa bayanshi harara.

"Ki zauna" ya fada mata.

Har ta bude baki Zatayi musu taji ya fizgo hannunta ya jefar da ita kan kujeran. "Bacci nakeso nayi, anjima munada long journey". ya fada sa'anan ya mike kan kujeran ya daura kansa bisa cinyarta yana ajiyar numfashi.

Zaro ido Samha tayi tana kallonsa kirjinta na harbawa tace "meye haka Sabah?" Muryanta tamkar zatayi kuka.

"Elephant leg-pillow" ya fada mata yana dariya hade da gyara kwanciyarsa kan cinyar nata.

Marairaice masa fuska tayi hade da kai masa bugun wasa a kafada "waye mai kafar elephant?"

"Naki mana... it's so comfortable".

Turo baki tayi hade da fadin "you're so childish wlh".

"Allah yasa baza'ayi ruwa gobe ba" ya fada hade da lumshe idanunsa.

Juyawa Samha tayi ta daga labulen window dake bayansu taga hasken rana na kokarin fitowa. Jin yayi shiru ne yasa ta da'an sunkuya tana leka fuskarsa taga har bacci yayi awon gaba dashi yana ajiyar numfashi tamkar wani baby. Ashe da gaske baccin yakeji. Murmushi ta da'an sake tana girgiza kai tana karewa kyaywar fuskarsa kallo tana jin wani irin sanyin a ranta hade da zazzafar kaunarsa na kara shigan mata rai.

**********************

Bangaren su Anty fanneh kuwa, har sukayi boarding jirgin ya tashi ta gagara samun nutsuwa cikin ranta.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now