Chapter Seventy

568 53 5
                                    

Uncle dayaga duk tabi ta tayar da hankalinta ta rude ne yasa ya soma mata nasiha yana kokarin kwantar mata da hankali yace wanan kadai itace mafita garesu kuma Allah yasa shine yafi zama mafi alheri a wajensu.

Sosai ya dinga mata nasiha wanda yasa gabadaya jikinta yayi sanyi. Ita tunaninta daya Ammi. Da wani ido zata kalleta idan ta dawo? Ita a yanzu haka ma ta shirya aure ne? Gabadaya tunaninta a hargitse yake.

Uncle ne ya fadawa Sabah daya jata suje suyi magana a private. Dayan parlourn suka nufa shida Samha suka zauna ya soma kokarin kwantar mata da hankali. Ai bata san sanda ta fashe mishi da kuka ba tana fadin "Sabah me kakeso muce wa Su Ammi da Abbah? Wanan ai cin amana ne da wani ido kakeso mu kallesu idan sun dawo? Sabah aure fa? Aure fa ba abun wasa bane".

Ajiyar zuciya Sabah ya sake yace "nasan da haka Samha, amma ki duba ki gani. Wanan itace kadai mafita garemu. Uncle kawun Abba ne don haka bamuda matsala. Idan komai ya lafa daga baya za'a sanar dasu. Samha i love you, ina matukar sanki tamkar raina, banjin zan iya rayuwa da wata ya'mace inba ke ba. Mami bazata tsaya kan Madina ba, a shirya take ta hadani aure da duk yarinyar da zuciyarta ta raya mata. Ni kuma gaskiya bazan iya bari tayi controlling rayuwata haka ba. Ni yanzu haka a shirye nake da nayi komai indai zan mallakeki a matsayin matata ta sunnah, banki na ba'ta da kowa ba. ki yarda dani kanwata bazan taba cutar dake ba. Idan an daura mana auren yanzu zamu koma gida batare da sun san abunda ya faru ba, sai daga baya za'a sanar dasu. Please i need your support kanwata, let's achieve our dreams together. Ki amince zaki zama matata".

Hannu yasa ya soma share hawayen dake ta faman zubo mata. Sai faman sheshekar kuka takeyi tana tunanin Ita tasu kalar soyayyar kenan? Da irin wanan kaddarar tazo musu?

Kara maso da ita kusa dashi yayi yana cigaba da lalashinta yana bata baki har ya samu kukan nata ya lafa yace "babu abunda zai canza Kanwata, we'll return back to our normal lives idan an daura auren kinji? Bazamu taba bari su sani ba".

Da haka dai da siyasa ya cigaba da lalabata har ya samu ta tsayar da kukan nata. Ta dago tana dubansa, har cikin ranta takejin sonsa na kara huda tsokar dake makale bisa kirjinta. Ita kanta tasan tana ba'lain son Sabah, sonsa a jininta yake, bazata taba iya rayuwa babu shi ba. Kuma tasan irin halin data shiga lokacin da mami taso hadashi aure da Madinah.

"Me kikace kanwata? Kin amince?" Ya kafeta da mayattun idanunsa masu shegen kyau da haske yana kallonta.

Duk da tsoro da fargaban dake cinta hakan bai hanata daga mishi kanta ba tace "na amince, Amma bazamu taba nunar musu ba ko Sabah. Kadau alkawari?"

Farin ciki kuwa tamkar ya zuba ruwa a kasa yasha dayaji tace ta amince "na dau alkawari kanwata, kuma nagode kwarai da gaske da kika amince zaki zama matata. I love you so much my heartbeat".

Kallonshi kawai takeyi tana ganin yanda duk yabi ya rikice kamar wanda aka mai kyauta da gidan aljannah. Ita har yau mamakin yanda Sabah yake sonta takeyi don a ganinta, yafi karfinta don mata waenda suka fita class da komai bai sauraresu ba ya nace yace sai ita.

Before you know it, cikin ruwan sanyi akaje aka daura auren dasu uncle a masalaci bisa sadaki dubu dari biyu kacal da Sabah ya biya.

Ba karamin kudi Sabah ya bawa kawu modibbo ba ya sallameshi sai faman washe baki yakeyi don shi daman gaba ta kaishi. Sabah daya kira Samha kuwa ya sanar da ita an daura har karamar zazzabi tayi don taci kuka harta gode Allah. Anty Ummi ce taketa faman rarashinta dan gyaran jikin ma da takeso ta yiwa Samha da kyar Samha ta yarda tayi mata sai faman kuka takeyi.

Sabah yana dawowa Samha tasa shi a gaba tanai mishi kuka akan lallai sai sun koma gida don hankalinta kwata kwata baya jikinta.

Da uncle yaji labarin a ranar zasu koma shima ya goyi bayan dasu koma. Kayan lefen dai duk a gidan uncle aka bari ba taba ba. Godiya sosai Sabah ya yiwa uncle yaja amaryarsa sukayi gaba. Sai dai kuma kash suna isa airport suka tadda anyi canceling flight din nasu sai zuwa gobe. Samha tamkar ta kurma ihu ta daura hannunta aka tace "shikenan abunda naketa gudu kenan gashi zai faru. Mezan fadawa Ammi idan ta dawo bata tadda mu a gida ba?"

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now