Chapter Twenty -Five

529 57 0
                                    

Samha jikinta ne yayi sanyi da jin kalamansa nan take kuma maganganun data fada mishi, da kuma yanda suka rabu a baya suka soma dawo mata. Tayi shiru tunani kala kala na mata yawo a haka. Ta juyo tana kallonsa daga bisani ta bude baki ta soma fadin " Amjad ai ban cancanci haka daga gareka ba, ko ka manta abubuwan dana fada maka can baya? I hurt you". Ta karasa maganar tana sunkuyar da kanta cike da nadama.

Amjad shiru yayi bai ce komai ba daga bisani ya bude baki ya soma tambayar ta "yanzu kina nadamar sonshi ne?"

Cikin sauri Samha ta dago tana dubansa, zata bashi ansa kenan Amjad ya katseta yana fadin " To be honest Samha, ban san meyasa kike sonshi ba. Amma a yanzu na fahimci dalilin dayasa kika zabeshi".

Murmushi Samha ta dan sake sa'anan tace " Har ga Allah Amjad, ni kaina ban san meyasa na zabi Sabah akan ka ba, kayi hakuri".

Amjad ya dan nesa sa'anan yace " it's okay, babu damuwa. Amma ki sani saboda shi na rasa ki so ni dashi baza mu taba wani shiri ba amma duk da hakan na kasa tsintar kaina da tsanar Sabah" Amjad ya karasa maganar yana tuno fadan da sukayi shi da Sabah a cikin gym, don yasan Sabah ya kawo kanshi ne don shi Amjad din ya duka, ya kuma huce takaicin rashin Samha akan shi.

Amjad ya dan nesa sa'anan ya cigaba da fadin "Ni sai yanzu na fuskanci yanayin Sabah, shi wani irin mutum ne mai cike da jin tausayin dan Adam kuma yanada nasa hanya da tsarin da yake taimakawa mutum, shiyasa har yanzu kika kasa gane kanshi. Ace mutum da irin shekarunsa amma yanada irin wanan tunani da hankalin? Abun yana bani mamaki sosai".

Samha tayi shiru tana nazarin abunda ya gama fadi.
Amjad ne ya dubeta yace " muje na dan taka miki".
Haka suka soma tafiya suna hira tsakaninsu.
Amjad ne ya lura da yanayinta kamar bata cikin walwala ya bude baki ya soma fadin "c'mon cheer up, naga har yanzu kina bata rai, Ni kuma in ce me?" kin manta ke kika ci game din da muka gama bugawa? Bayan haka gashi kin gano cewa kinada saurayi mai hankali".

"Wa kenan?" Samha ta tambayeshi.

Sabah mana, da waye. Ko kin manta yanzu ni dake we are just friends".

Samha ta juyo tana dubanshi sa'anan ta bashi ansa da "Amjad kenan, karka damu insha Allah kaima zaka samu budurwa mai kirki da hankali wace zata kawar maka da duk wata damuwa dake cikin rayuwarka".

Amjad ya dan murmusa sa'anan ya bata ansa da "na sani". Sai kuma yayi shiru yana nazari nan da nan kuma ya tuno da khady da kuma fitan daya kamata suyi shi da ita.

Gabansa ne ya fadi don gabadaya ya manta shap, yasan yanzu kilan ta gaji da jiranshi ta tafi abunta. Cikin sauri ya juyo yana duban samha ya soma fadin "Samha ni zan wuce yanzu, wlh nayi mantuwa, i have to go". Cikin sauri sukayi sallama ya juya ya tafi ya barta a wurin.

Samha ta bi bayanshi da kallon mamaki, ajiyar zuciya ta sake sa'anan ta cigaba da tafiyarta ita kadai tana tunanin zuci. Tana tunanin Sabah da kuma Aliyah da kuma yanda abubuwa zasu kasance tsakaninsu nan gaba. Wata zuciyar ce ta soma tambayarta da anya kuwa zaki iya? Ga Aliyah data kudiri niyan ganin bayan duk wanda zai zo ya tsaya a tsakaninta da Sabah. Wata zuciyar ce ta bata ansa da "Gwanda ma ki dage karki taba bari Aliyah ta samu nasara akanki. Da wanan tunanin ne hankalinta ya dan kwanta ta kudiri niyan itama zata tashi ta mike tsaye akan abunda takeso.

Bangaren khady kam har ta gaji da jira, ta mike daga inda take zaune, jiki a sanyaye ta soma tafiya kamar zatayi kuka, wani irin tausayin kanta takeji tana tafiya tana matse matsen kwalla har tazo ta karya kwana ta shiga wata layi, sai ya zamana da daidai lokacin da shima Amjad ya karaso suka samu sabani, yazo yanata faman waige waige bai ganta ba.

Cikin sauri ya zira hanunsa cikin aljihu ya ciro wayarsa ya soma neman layinta. Sai da kiran ya kusan tsinkewa tukuna ta daga.

Amjad yana jin ta daga nan da nan ya soma bata hakuri yana fadin "Hello khadija, dan Allah kiyi hakuri kinga na sake yin late yau ban zo da wuri ba, na barki kinata jirana. I'm so so sorry please".

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now