Chapter Eighty- one

782 54 0
                                    

Ranar monday da yamma Samha tana zaune a parlour ta kunna tashar discovery world tana kallo don tashan yana birgeta sosai. Ko ina shiru in banda karar makeken tv dake parlorn da kuma sanyin Ac dake tashi ba abunda akeji. Ammi tana sama a dakinta tana kwance.

Sosai Samha tayi zurfi cikin kallon from nowhere taji saukan hannun na yawo bisa wuyanta. A firgice ta da'go zata sake yar' kara idanunta sukayi ido hu'du da Sabah wanda ke tsaye a bayan kujeranta ya kura mata ido yana kallonta. Kallonsa take tamkar a mafarki tana jin yanda kirjinta ke tsananta bugu saboda firgitan datayi. Bai ma kirata a waya ya sanar da ita zuwansa ba.

Wani irin farin ciki ne taji ya lulubeta Cikin sauri ta mike ta zagayo tazo ta rungume shi tsam a jikinta tana ajiyar numfashi. Shima kara matsota jikinsa yayi sosai yana jin dumin jikinta da daddaden kamshin jikinta na ratsa jikinsa. Sunfi 5 mins a hakan suna jin yanda bugun kirjinsu ke karuwa cike da matsanancin son junansu.

A hankali ya da'ago yana karewa kyakyawar fuskarta kallo, tun daga manyan idanunta zuwaga dan madaidaicin hancinta sa'anan ya gangaro zuwa ga karamin bakinta yana kare mata kallo. Zatayi magana taji ya hade bakinsu wuri da'ya ya shiga kissing lips dinta, ya kamo lips dinta na kasa yana tsotsa. Sunfi 5 mins suna tsotsan lips din junansu har tsayuwa ya soma neman gagarasu, A hankali Sabah ya ware lips dinsa daga nata ya bude idanunsa ya zubesu cikin nata sa'anan ya hade goshinsu wuri da'ya  suna ajiyar numfashi a tare. Muryansa kasa kasa yace "you don't know how i've missed you.. missed kissing you". Ya karasa maganar yana kai mata kiss a wuya.

"I've missed you too" ta fada mishi hade da lumshe idanunta.

A hankali taga ya shafo cikinta yana murmushi yace "and how's my princess doing... da fatan dai kina kulan mun da ita ana bata abunda takeso?"

Dariya Samha tayi tace "eh mana...yau kuwa coldstone takeson sha".

"Toh an gama.. bari aje a karbo mata".

Suna dariya suka karasa three seatern tare  suka zauna. Sabah ya soma tambayarta Anty Fanneh. Tace tana can sama dakinta tana bacci yace toh idan ta tashi zaije su gaisa.

"Bari na kawo maka ruwa kasha". Ta fada hade da mikewa tayi hanyar kitchen. Shi kuwa ya bita da kallo, yanda take karya kugunta kamar ba mai ciki ba yasa ya shagala da kallonta har taje ta kawo masa ruwan ya karba yana binta da wani irin mayattacen kallo cike da zallar sha'awarta.

A hankali ta shiga janshi da hira, ya soma zolayarta kamar yanda ya saba ita kuwa sai faman zuba mishi shagwaba take. Suna zaune, ya ciro wayarsa ya shiga musu ordern icecream din datace tana kwadayin sha. Within 30 mins delivery guy din yazo ya tsaya a gate, Sabah ya aika da'ya daga cikin securities din suka karbo.

Katuwar roba manya manya guda uku ya diresu a gabanta. Samha miyau har tsinke mata yake cike da murna ta mike ta shige kitchen ta debo madaran garri a cikin plate. Sabah yana zaune yana kallon ikon Allah yaga ta debo icecream din ta kwaba da madaran ta soma sha tana wani irin lumshe ido cike da tsansar jin dadi.

Matsowa tayi kusa dashi ta debo kwaben nata tana kokarin kai masa baki yaja da  baya hade da girgiza mata kansa yace bazai sha ba.

Tabe baki tayi tace "tab..ka bar dadi yasin".

Haka ta cigaba da shan icecream dinta tana lumshe ido tana sumbatu cikin kankanin lokaci har ta tashi da roba da'ya.

A haka Anty Fanneh ta sauko ta samesu tana ganin Sabah tace "a'a Sabah yaushe ka shigo?"

"Ban jima da shigowa ba Anty. Ina wuni Ya karfin jiki?"

" lfy kalau Sabah Jiki alhamdulillah". ta fada hade da samun wuri ta zauna. A lokacin ne idanunta suka sauka kan Samha dake zaune a gefe da robobin ice cream jere a gabanta. Sallati Anty fanneh ta shiga yi tana fadin "na shiga uku..yanzu Samha abunda kikeyi kin kyautawa kanki kenan? Kiyita dirkawa cikinki Kayan zaki da sanyi? Kai kuma Sabah kake biye mata ko?"

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now