Chapter fourty-one

422 45 5
                                    

Samha tafiya take ita kadai, tazo daidai wurin shiga department dinsu kenan taji ana kwada mata kira. "Samha! Samha!!..."

Tsayawa tayi ta waiga, Zack ta gani tafe cikin sauri yana kokarin karasowa inda take "Samha kizo da sauri, ga Sabah can ya jiwa kanshi ciwo" ya fada mata hankalinshi a matukar tashe.

Gaban Samha ne yayi wani irin mumunar faduwa ta dafe kirji tana fadin "innalillahi Ciwo kuma? Garin yaya?"

"Wlh nima ban sani ba, na ganshi hanunsa nata zubda jini, kuma nasan shine zai jiwa kansa wanan raunin".

"Akan me zai jiwa kansa rauni?" Samha ta tambayeshi hankalinta a tashe.

I don't know, but i think yana son ya dawo da halayensa nada ne, wanda tun muna high school. Babu wanda ya isa ya tunkareshi, ko muna tare dashi he always seems alone.... that withdrawn look....Samha idan hakan ta cigaba, Sabah will move farther and farther away from us". Ya karasa maganar cike
damuwa.

Samha itama cike da damuwa ta soma girgiza kai tace "ina Sabah bazai taba barinmu ba".

"Wlh Samha zai iya, nasan halinsa sarai and i'm really worried about him, bakisan yanda Sabah yake bane a da".

Hankali a matukar tashe Samha tace "toh yanzu ina yake?"

" yanzu na ganshi yayi hanyar staff quaters. Ina mishi magana ma ko tanka mun baiyi ba".

"Bari naje na same shi toh" cikin sauri ta bar wurin tayi hanyar staff quaters don neman Sabah.

Tana zuwa daidai wurin staff quaters, ta hangon shi tsaye shi kadai yayi zurfi cikin tunani. Gashi wurin yayi tsit babu kowa sai bishiyoyi da karan kukan tsuntsaye keta faman tashi.

Tsayawa tayi cak tana kare masa kallo, Hannunsa dake faman zubda jini ta kurawa ido, nan take taji hankalinta ya kara tashi.

A hankali ta tako har tazo ta tsaya dab da inda yake. Yana sensing presence dinta nan da nan jikinsa yayi tense.

A hankali ta kira sunanshi "Sabah..... daman kana nan?"

"Menene kuma....What is it?" Ya watso mata tambayar ko juyowa baiyi ba ya kalleta.

"I heard you were hurt". Ta fada mishi muryarta kasa kasa.

Tsaki yaja ya juyo a fusace yana fadin "so nawa zan fada miki ki daina maganata a bayana?! Eh?"

"Ba maganan ka nakeyi a bayanka ba, i'm just worried about you ne kuma bani kadai ba, harta su Zack kowa hankalinsa a tashe yake Sabah, everyone is worried about you"

Sabah ya katseta da "Ba wani ciwo naji sosai ba, kawai kujewa nayi a hanun". Ya fada yana kawar da kansa gefe.

"To mugani" ta fada tana kokarin kamo hanunsa daya ji ciwon.

Fizge hanunsa yayi daga rukon da take kokarin yi, ya watsa mata wani irin kallo sa'anan ya juya ya soma tafiya.

Nan take Samha taji wani iri game da  abunda yayi, amma still bata bari abun ya dameta ba ta juyo tana fadin " How can you mistreat your own hand Sabah?! Hanun dake buga basketball, hanun dake creating websites, hanun dake taimaka ma wasu, hanun dake share mun hawayena a duk sanda na riski kaina cikin kunci? How can you mistreat it?" Ta karasa maganar hawaye na zuba mata bisa kuncinta.

Sabah tsayawa yayi cak yana sauraronta. Samha ganin ya tsaya, bata san sanda ta karaso a guje tazo ta rungumeshi ta baya tana sheshekar kuka ba.

Sabah murmushi ya dan sake nan take yaji wani irin sanyi ya ratsa jikinsa, jinta manne a bayansa. Amma bai bari ta gano hakan ba yace "ki sake ni".

"Naki" ta fada a shagwabance tana kara matso shi jikinta.

"So kike a zo a ganmu a hakan?" Ya tambayeta.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now