Chapter seventy- four

657 54 3
                                    

Shiru Samha tayi bata sake cewa komai ba har suka gama Sabah ya kamo hannunta suka mike suka nufa inda yayi parking mota.

Driving yake amma mind dinsa baya tare dashi, tunanin abubuwa da dama ne suke masa yawo a ka. Yana cikin wanan tunanin wayarsa ta soma ringing ya duba yaga Abba ne ke kiransa. Da'ga kiran yayi ya kara a kunne da'yan hannunsa na bisa steering.

"Babyboy kana ina?"

"Ina hanya zuwa gida Abba"

"Kanwarka fa?"

"Muna tare gata nan kusa dani".

"Okay toh. Daman akwai magungunan da Amminku take bukata ne, inaso ka biya healthplus ka siyo mata".

Babu musu Sabah yace "toh Abbah ya sunan maganin".

"Bari nayi maka texting dinsu"

Bafi seconds biyi ba sai ga sakon sunan magungunan sun shigo. Healthplus pharmacy dake kingsway suka nufa Sabah yaje yayi parking sa'anan ya juyo yana duban Samha datayi lamoo akan seat tamkar bata cikin motar.

"Babe ina zuwa, bari na shiga ciki na dubowa Ammi magani".

Kai kawai ta da'ga mishi.

"Ko zaki bini ne muje?".

Nan ma ta sake da'ga masa kai.

Hannu yasa ya da'an shafo fuskarta yana murmushi sa'anan ya kamo hannunta cikin nashi yace "oya let's go"

Tare suka fito daga cikin motar suka karasa cikin pharmacy din. Kai tsaye wurin da'ya daga cikin pharmacists din Sabah ya nufa ya ciro wayarsa ya soma kokarin nuna mata sunan maganin da yake bukata. Da'agowan da pharmacist din zatayi idanunta suka sauka kansa, ta sake baki tana binshi da kallo , Tunda take bata taba ganin namiji da kallo da'ya ya tafi da imaninta haka ba. sosai ta shagala da kallon nasa har sai da ya sake maimaita abunda ya fadi tukuna ta dawo cikin hayacinta ta karba wayar daga hanunsa ta soma duba sunan maganin.

"Akwai" ta sanar dashi tana mika masa wayar hade aika masa da wani irin narkaken murmushi.Duk wanan dake wakana a gaban Samha ne, kuma ta shaqa sosai sai faman hararar Yarinyar takeyi wace bata ma lura da ita a wajen ba don gabadaya hankalinta ya karkata zuwa ga Sabah. Cike da ba'rin jiki taje dauko masa magungunan.

Sabah ya lura da komai amma yayi shiru bai ce komai ba har sai da yarinyar taje ta debo masa magungunan ta kawo.

"Nawa kenan?" Ya tamabyeta.

Muryanta kasa kasa ta sanar dashi kudin. Babu musu Sabah ya zira hanunsa cikin aljihu ya ciro wallet dinsa sa'anan ya mika mata debit card dinsa ta karba tasa a POS machine. Bayan ta cire kudin ta mika masa Card din hade da reciept taje ta soma hada masa magungunan cikin leda tana masa bayanin yanda za'a sha. Tafi 10 minutes tana masa bayani sai faman kararaya take tana noke murya. Hakan kuwa ya kara kular da Samha, wani irin kishi ne taji ya ciyo ta bata san sanda ta mike ta karaso wurin hannunta rungume da kirji tazo ta tsaya a gefen Sabah tana gyaran murya idanunta kyam akan pharmacist din tana aika mata da wani irin kallo.

Ganin Samha tazo ta tsaya ne yasa pharmacist din ta dakatar da maganar da takeyi ta juyo tana kallonta.

"Mallama sauri mukeyi ki hada mana magungunan mu tafi". Samha ta fada tana hararnta

Kallon Samha tayi sa'anan ta dawo da dubanta ga Sabah wanda yayi shiru, nan da nan kuma brain dinta ya hasko mata cewa bashi kadai yazo ba, toh wacece wanan? Kodai matarsa ce?Amma anya kuwa matarsa ce don they're both looking very young. Kilan budurwarsa ce wata zuciyar ta sanar da ita. Bata kuma cewa komai ba ta tattara musu magungunan ta mika musu sa'anan sukayi gaba, har suka fice daga cikin pharmacy din idanun yarinyar na kan Sabah tana binshi da kallo tamkar zata cinyeshi.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now