Chapter Ten

682 74 0
                                    

Su sabah suka hadu da amjad suka fara practice dinsu. Bayan sun buga na kusan hour daya. Sabah ya nema wuri ya zauna, cike da dagin murya ya kira sunan manager. Badan taso ba haka samha tazo ta sameshi inda yake zaune, turo dan karamin bakinta tayi tana galla masa harara. "Meye kuma naji ka kirani?" Ta tambayeshi.

"Manager aikin ki shine ki dinga kula da lamarin masu buga kwallo, duk wani bukatarsu yana rataye a kanki kuma dole ki tabbatar da sun samu. Don haka kije ki kawo mun ruwa nasha, kishi nakeji" ya fada mata.

Wani irin kallo da bishi dashi sa'anan tace " ban gane in kawo maka ruwa kasha ba, meya samu kafafunka" Ta tambayeshi.

Ji tayi ya daga murya yana fadin "captain, wanan manager din fa bata san aikinta ba. Ya kamata mu canza ta!"

Samha najin ya ambato sunan amjad, ta zaro ido. Babu shiri ta bar wurin taje nemo masa ruwan da zai sha don bata san amjad yaga gazawarta wurin aikinta na manager.
Cikin yan mintuna kadan sai gata da bottle water ta kawo mishi. Karfa yayi daga hanunta ya bude ya fara sha. Zata juya ta tafi kenan taji ya sake fadin " ki kawo mun towel da kuma juice".

Cike da takaici ta sake juyawa taje ta nemo masa juice da towel ta kawo masa. Karfan towel din yayi daga hanunta sa'anan yace ta bude masa juice din. Babu yanda ta iya haka ta sa hanu ta girgiza kwalin juice din sa'anan ta bude masa ya karfa ya fara sha.

Kafun ta tafi ya dakatar da ita yace mata saura abu daya. Zuciyarta ne ya soma tafarfasa don taga rainin hankalin nasa ya soma wuce tunani, kuma gani takeyi don ya sameta ne shiyasa yake mata duk abunda yaga dama.
Cike da takaici ta juyo tana dubansa. " me kuma zan maka" ta tambayeshi.

Gira daya ya daga mata yana dubanta. kyakyawar fuskarsa dauke da murmushin makirci wanda yasa har dimple dinsa guda biyu dake gefen fuskarsa suka bayana, bude baki yayi yace " Abu daya ne ya rage miki kanwata, tausah nake so ki mun, gaba daya jikina ya mutu daga wasan nan da muka gama bugawa".

" wa zai maka tausah? Ni din ce zan maka tausah?"ta fada tana nuna kanta.
Gyada mata kai yayi, ya cigaba da kallonta.

"Amma sabah rainin hankalinka yayi yawa wlh amma ba laifinka bane. Laifi nane dana baka chance kake mun duk abunda kaga dama." Tana gama fadin haka ta ja tsaki ta tafi ta barshi a wajen.
Shikam dariya ya sake yana girgiza kai, kishingida yayi akan kujera dayake zaune akai ya lumshe idanunsa kamar mai bacci.

Samha ta samu wuri ta zauna tayi tagumi, haushi da takaicin sabah duk ya adabe ta. Tana cikin tunaninta su khadie suka karaso suka zo suka sameta.
Amina ce ta tambayeta " samha ya na ganki haka duk a hargitse? Ina amjad din kun samu kun kebe kuwa yau dinan?"

"Ina fah, kina tunanin hakan zai yu ne idan wancan iblees din yana nan?"

Amina ta girgiza kai sa'anan tace " samha ya kamata ki dage da aikin ki a matsayin manager na wanan team din fa"

"Ban gane ba, me kike nufi?" Samha ta tambayeta.

"Na samu labari sabah tun yana secondary school yake buga basketball ball, kuma ya kware sosai, a lokacin dai bansan meye ya hadashi da coach dinsu ba, sabah ya mishi dukan tsiya, shiyasa ma aka koreshi daga team din, har suspending dinshi daga makaranta akayi a wanan lokacin." Amina ta sanar da ita.

" wato har dukan coach din secondary school dinsu yayi? Kunga halin nasa ba?" Samha ta fada tana girgiza kai.

"Toh ai dayake family dinsa suna da kudi sosai, shiyasa ma ba koreshi daga makarantar ba, suspending dinsa kawai akayi aka share maganar."

"Akwai gyara a maganarki, ba haka abun ya faru ba" suka ji magana kamar daga sama. Juyawa sukayi sukaga zakari wato zack abokin sabah a bayansu. Wuri ya samu ya zauna a gefe ya kishingida sa'anan ya cigaba da fadin.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now