Chapter Thirty- Two

552 51 0
                                    

"Wow, amma gaskiya guy dinan ya hadu".
"Kai he's so handsome, dan Allah waye shi?"

Haka yan'matan department suke ta rububin fadi suna karewa wani hadadden guy daya shigo cikin department dinsu kallo. Ba matan ba harta mazan ma binshi da kallo sukeyi.

Sanye yake cikin wata haddiyar black kaftan anyi mishi dinkin riga da wando. Sumar kansa ta kwanta bisa kanshi. Fari ne sosai yanada haske, kuma yanada madaidacin tsawo bashida jiki. Hancinsa straight ga dara daren idanunsa farare tass dasu sai dan karamin pink lips dinsa. A fuska zaka ganshi kamar yaro yaro amma yanada jikin manya.

Tafiya yakeyi shi kadai handsome face dinshi dauke da murmushi ya soma haurawa staircase din, kowa sai binsa da kallo yakeyi saboda tsabar kyau da kwarjinin da Allah yayi masa.

Har ya haura yazo dab da corridor da zai sadaka da lecturer halls din department din yaja ya tsaya.

Samha ce ya hango tana dab da karasowa, tafiya takeyi kanta a sunkuye cike da tunani da takaicin Sabah hannunta still rike da letters din tana tafiya cikin sauri.

Ganin mutum tsaye a gabanta ne yasa taja birki ta tsaye tana dubansa. Murmushi ya sakar mata yana kallonta. Gabanta ne yayi wani irin mumunar faduwa da idanunta suka ci karo da takardan dayake rike dashi a hanunsa.

"Har da maza ma? Shima so yakeyi na bawa Sabah sako ne ko meye?" Ta tambayi kanta kirjinta na bugawa.

Guy din still yana murmushi ya dago hanunsa ya mika mata letter din yace " This is for you".

Cike da mamaki Samha ta sona binshi da kallo sa'anan tace " Ban gane ba".

Bai tsaya wata wata ba, kai tsaye yace mata "Sonki nakeyi".

Wani irin dummm Samha taji a cikin kirjinta ta bude baki tana kallonsa.

Guy din ya cigaba da fadin "ina sonki Yan'mata". Ya sake maimaitawa Still hanunsa na rike da letter din.

Samha duk tabi ta rikice tunani kala kala suna mata yawo a ka, anya kuwa wanan ba wasa da hankalina yazo yi ba. Yama za'ayi ace yana so na. Ina bazai yu ba". Ta fada a zuciyarta.

Kamar ya jiyo tunanin da takeyi yace "da gaske nakeyi baby girl, ina sonki"

Wani irin kallo ta watsa mishi sama da kasa, nan take tunanin Sabah ya fado mata ta soma fadin " haba mallam,haka kawai ban sanka ba kuma ban taba ganinka ba kazo kace kana sona? An taba soyayya haka? gaskiya bazan iya ba".
Tana gama fadin haka ta kara gaba ta tafi ta barshi tsaye a wajen. Har ta danyi taku biyu ko mai ta tuna? Sai kuma ta sake dawowa tazo tace mishi " kayi hakuri"

Nan kuma ta sakeyin gaba tana tafiya cikin sauri, guy din yana tsaye ya bi bayanta da kallo yana wani irin shu'umin murmushi.

***************

Lecture hall din Cosc403 yayi shiru, babu abunda yake tashi illa karan AC dake zube cikin lecture hall din, sai kuma muryan lecturer din dake tsaye wajen projector yana yiwa students din bayani.

Sabah yana zaune tare dasu shinoh a seat dake row na biyu ya kishingida akan kujeran, hankalinshi a kwance sai faman zabga bacci yakeyi abunsa kai kace yana parlourn gidansu ne.

Lecturer din ya dage yana musu bayani akan cewa yanason students din suyi wata web design amma as a group project, kuma ko wani group za' suyi submitting project dinsu zuwa ga wani babban company toh duk group din da suka ci sa'a, company din ta zabe web design dinsu, company din zata iya awarding dinsu scholarship na zuwa karatun masters.

Surutu da hayaniya ne ya barke tsakin students din kowa yana murna da wanan zancen.

Lecturer din ya cigaba da fadin " kuma wanan project din zai zame muku kamar upgrade ne na wanan semester din. So daga ni har school management din muna fata ko wanen ku zai dage yayi participating akan wanan project din. I hope you won't let us down".

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now