Chapter fourty- six

442 43 4
                                    

"Samha ya mahaifiyarki da fatan dai tana nan lafiya?" Sameer ya tambayeta.

"Ammi tana nan lafiya".

"Insha Allah zan samu lokaci nazo har gida mu gaisa. Amma samha na samu labari cewa Amminki ta kara aure."

"Eh kwanan nan tayi auren, Ta auri VC na makarantan nan. Bakaga yanda yake kulawa da Ammi ba yaya sameer, Abba yanada kirki sosai."

Sameer ya danyi jimm sa'anan yace "kefa is he good to you? Yana kulawa dake?"

Samha tayi sauri ta gyada masa kanta tace "ai Abba ya dauke ni tamkar yar' cikinsa. Yana nuna mana so da kulawa sosai".

Sameer ya jinjina kai yace "Toh masha Allah, haka akeso ai. After all these years, gaskiya ina taya Amminki murna, Allah ya basu zaman lafiya. Kema gashi kin girma kina jammi'a abunki, abu yayi kyau sosai". ya karasa maganar yana murmushi.

Itama Samha murmushi ta sakar masa sa'anan tace "Nagode sosai da kulawar daka dinga bamu shekaru baya da suka wuce. Ai kayi mana kokari sosai yaya Sameer, Allah ya saka".

Sameer still yana murmushi yace "ameen"

Nan suka soma tuna baya wanda ya dangana da tun lokacin Samha tana karama mahaifinta nada rai sameer yana zuwa karban karatu. Yanda kuma Sameer duk sanda zai zo sai ya kawo mata abubuwan makulashe tayi ta murna tana tsale, duk waenan abubuwan sai da suka tuno. Sai faman hira suke cike da anashuwa suna dariya.

Ashe suk wanan hiran da sukeyi oga Sabah yana tsaye ta daga can gefe yana kallonsu.

Samha dinsa ne yake gani tana zance da wani hankali kwance sai faman kyalkyale dariya takeyi babu abunda ya dameta? Wani irin tafarfasa zuciyarsa ke masa nan take yaji kamar yaje ya shake sameer ko zai samu sasauci cikin zuciyarsa.

Shi kansa yasan yanada mugun tsananin kishi akanta duk da dai baya nuna mata hakan. Kwata kwata baya son abunda zai hadata da wani da' namiji da zai kai ga har su tsaya suna zance.

Yana bala'in sonta kuma Baya son taso kowa sai shi kadai, haka zalika baya son yaga ta damu da kowa sai shi...

Don haka jikinsa ne ya dau rawa, kokarin controlling din kansa ya somayi kar yaje ya aikata wani abun da bai kamata ba, don haka ya tsaya yayi shiru yana kallonsu. Har suka gama zancen sukayi sallama, idanunsa na kanta. Gani yayi ta juya ta soma tafiya ita kadai tayi hanyar barin cikin makaranta, shima ya bi bayanta.
Sai da sukayi tafiya na kusan 20 minutes bata ma san yana binta ba.

Gani yayi ta shiga layinsu na'da, bata tsaya ko ina ba sai daidai bakin gate din tsohon gidansu, yaga ta tsaya ta kurawa gidan ido.

Ita kam Samha tunda sukayi hira da Sameer taji gabadaya kewan gidan nasu ya kamata, wani irin nostalgic feeling ta dinga ji, bata ankara ba ta tsinta kanta a kofar gidansu.

Kamar daga sama taji murya a gefenta ana fadin "waye shi?".

Gabanta ne ya tsinke ya fadi ta juyo cikin sauri taga Sabah tsaye yana kallonta fuskansa a daure tamau.

"Lah Sabah wlh ka tsorata ni". Ta fada tana dafe kirji.

A hankali ya karaso har yazo ya tsaya dab da ita, cikin kausashen murya yace "baki ansa tambayata ba. nace waye shi?"

"Ban gane ba? Wa kake nufi?"

"Wanda na ganki dazu a gaban department kuna hira dashi". Ya fada mata kai tsaye.

Gabanta ne ya sake faduwa tace "daman ka gan mu?"

"Who is he Samha?" Ya kara tambayarta.

"Wani family friend dinmu ne, mun jima bamu hadu ba sai yau na ganshi a school".

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now