Chapter Twenty -four

487 57 0
                                    

Bangaren su Sabah kuwa, sun shigo cikin gym shida su shinoh da sauran yan' team suna dan motsa jiki da exercise kafun su fara practice. Amjad ne ya shigo, rataye da school bag a bayansa, sanye yake cikin jar sweater da bakin wando, sumar kansa tasha gyara sai shekki da daukar ido takeyi. Karasowa yayi yazo ya tadda su Sabah yana fadin "yau kam zan barku da wuri, zakuyi practice banda ni".

Bayan ya karasa maganar ya juyo yana duban Sabah sa'anan ya cigaba da fadin
"Sabah please tunda kaine team leader, sai ka sa ido sosai akan practice din. Ni sai na dawo".

Sabah ya gyada kai sa'anan ya bashi ansa da "Babu matsala, amma ace Captain guda yana fashin practice, me kenan akayi?"

Amjad shiru yayi ya ma rasa ansar da zai bashi ya juyo yana duban sauran yan' team din yana fadin " me ma nake cewa? Yauwa, kar ku manta in case ban dawo da wuri ba,  idan kun gama practice ku tabbatar kun rufe windows da kofofin gym din, wai tsaya ma tukuna ina managers din suke, ban ji duriyarsu ba?" Ya karasa maganar yana dubansu.

Zack ne ya bude baki ya bashi ansa da " sun dan fita tare ne, amma sunce yanzu zasu dawo".

Sabah ne ya dago yana dubanshi jin yace sun fita tare, tunani kala kala ne suka soma masa yawo a ka. Amjad bai damu ba yace " Toh shikenan babu matsala, ni zan wuce yanzu. Ku kula please". Yana karasa maganar ya juya ya bar wurin.

Bangaren su Samha kuwa tsaye suke suna fuskantar junansu, kowace cike take da jin haushin yar'uwarta. Samha ce ta bude baki ta cigaba da fadin "Amma Aliyah bakida kirki, saboda kinga Sabah yanada tausayi shiyasa kike amfani da wanan damar?"

"Toh wai ni meye naki ne a ciki? Kinzo kin wani tsareni da tambayoyi, kawai dai kina kishi ne don kinga ni yake nunawa kulawa bake ba, yanzu dai kin gane cewa ni ce cikin zuciyar Sabah ba ke ba ko?"

Samha shiru tayi tana kallonta da dara daran idanunta, bata ce mata komai ba.
Wani irin haushi taji yana tasomata da jin maganganunta, don maganganun sun rigada sun kaita bango.

Murmushi Aliyah ta sakar mata sa'anan ta cigaba da fadin " Nasan abun zai baki mamaki, don a ranan kin tafi a guje domin kije ki kirashi, Amma a karshe sai kikaga an manta da ke, Sabah ko ta kanki bai bi ba. Sai kika ji kanki tamkar wata banza an tafi an barki, na tabbata da kinyi kuka koh?" Aliyah ta karasa maganar tana jefo mata murmushin mugunta.

Samha da zuciya ya dibeta bata san sanda ta daga Hannu ta watsa ma Aliyah mari ba. Dai dai lokacin sai ga Sabah da zack sun shigo cikin library din. Aliyah na ganinsu ta fashe da kukan makirci tana dafe kumatunta inda Samha ta mara. Da sauri Zack da Sabah suka karaso suna tambayarta abunda ya faru.

Aliyah ta marairaice fuska cikin muryar kuka ta soma fadin " wlh ban mata komai ba haka kawai ta daga hannu ta watsa min mari" tana karasa maganar ta fashe da wani irin kuka.

Zack ne cikin zafin rai ya kalla Samha ya soma fadin " Me tayi miki da zaki daga hannu ki mareta haka eh?"

Samha kanta duk yabi ya daure, cikin i'ina
ta bude baki tana kokarin ta musu bayani, Sabah ne ya katse a tsawace yana fadin " Da gaske ne kin mareta ba tare da ta miki komai ba?! Ko baki lura da har yanzu tana da raunika a jikinta bane?!"

Aliyah cike da makirci ta matso kusa da Sabah tana fadin "Prince kayi hakuri ka kyaleta hakan, i'm okay babu abunda ya sameni, ka kwantar da hankalinka ". Ta karasa maganar tana sakar masa murmushi.

Sabah wani irin huci yakeyi don gabadaya abunda Samha tayi ya rigada ya gama bata mishi rai. Samha cikin zafin rai ta bude baki ta soma fadin "wato Sabah baza ka tsaya kaji ta bakina ba kenan, why do you always have to protect her? Kana ganin Abubuwan da takeyi marasa kyau, amma kana overlooking, idan ka cigaba da bata wanan daman, it'll only get worse"

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now