Chapter Fifty- five

438 51 2
                                    

Bangaren su Samha kuwa. Bayan ita da Madina sunje sun siyo wa yan team abunda zasu ci.

Zaune suke daidai bakin wani ruwa dake cikin wurin suna dan taba hira.

Samha ta dubi Madina tace " Madina, ranan kince kinada wanda kikeso. Waye shi?"

Madina ta da'an saki murmushi sa'anan tace " eh inada wanda nakeso, saboda a lokacin dana fara haduwa dashi, sai da zuciyata ta buga, don ban taba jin haka a game da wani da namiji shiyasa nan da nan i fell for him".

Samha tayi murmushi sa'anan tace " so ya kuke dashi yanzu, kuna dating ne?"

Madina ta da'an girgiza mata kanta tace "a'a nifa yanzu haka ban ma san inda yake ba. Ko kamaninshi ma ban gama tabbatar wa ba"

Cike da mamaki Samha ta soma kallonta tace "kai Madina, ban gane ba".

"Kinsan inada heavy eye glass prescribtion. Bana gani sosai sai da taimakon wanan eye glass din"

Cikin sauri Samha ta mike, tazo ta tsuguna dab da Madina tana kallon cikin kwayar idanunta cike da mamaki tace "yanzu kina nufin baki ganina da kyau kenan?"

dariya madina tayi sa'anan tace " ina gani mana, yanzu haka sanye nake da contact lens cikin idanuna. Bari kiji yanda haduwar namu ta kasance. A ranar na fito cikin layin mu ina tafiya ni kadai kenan ban ankara ba motarsa tazo saura kadan ya kadeni don na shiga hanya kai tsaye ne ban lura ba, a sanadiyan haka ne na fadi glasses dinsa suka fashe, shine ya fito ya taimakamun har ya kaini eye clinic aka mun wasu, daba din shi ba ban san ya zanyi ba a ranar. He rescued me like a knight in shining armour".

Samha ta jinjina mata kai tace "wow, yanzu kina nufin guy dinan is a total stranger to you kenan? Baki san sa ba, Kuma a hakan kike sonsa?"

"Kwarai kuwa. Sonshi nake sosai kuma kullum addu'ata da fatana bai wuce Allah ya kara hadani dashi ba. Banyi loosing hope ba Big sis, don har yanzu inaji a jikina cewa nan bada jimawa ba zan kara ganinshi, kuma idan na ganshi babu abunda zai raba ni dashi insha Allah".

Samha tayi shiru tana kallonta, jikinta ne kara yin sanyi ganin yanda Madina taketa faman zuba akan wanda ma bata sanshi ba, bai ma san tanayi ba. "She's just like the old me, living in a world of fanatsy, creating an idealized person. Love only exists in her imagination". Samha ta fada can kasan ranta tana kallon Madina.

"Wato wanda Madina ta dage tana kirarin cewa tanada wanda takeso ba komai bane illa fantasy?" Suka ji muryan Aliyah a bayansu.

Tare suka jiyo suka ganta tsaye tayi folding hanayenta bisa kirjinta tana kallonsu. Ashe duk maganar da sukeyi tana tsaye tana jinsu bata ce komai ba.

Karasowa tayi inda suke zaune sa'anan ta cigaba da fadin "wanan unrealistic love din dakikeyi har ina zata kaiki? kuma har yaushe za tayi miki lasting? baki tunanin wata rana waenan feelings din zasu iya transferring zuwa ga wani?" Ta karasa maganar tana kallon Samha.

Nan da nan Samha ta gano abunda take nufi, wato Feelings din madina zai iya canzawa zuwa ga Sabah kenan?

Cike da tashin hankali Samah ta soma kallonta.

Madina ta mike tana murmushi tace "kinji maganar da mukeyi kenan?"

Aliyah kallonta tayi na da'an wani lokaci sa'anan ta dawo da dubanta ga Samha sa'anan ta soma magana cikin harshen turanci tace "Samha there's one kind of rival that is hardest to beat, and that is without you realizing, she's already between you two. And when you look at her innocent expression, you can't condemn her".

Samha shiru tayi tana jinta cike da tashin hankali don tasan warning kawai Aliyah take mata akan Madina tayi taka tsantsan da ita don komai zai iya faruwa.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now