Chapter Seventy-Two

642 55 1
                                    

"Abba har ka dawo?"

"Na dawo" Abba ya fada yana kare musu kallo daya bayan daya wanda yasa suka ja jinin jikinsu. Barin ba Samha wace tafi tsorata kirjinta sai buguwa yake da karfin gaske.

"Ya naganku anan haka?"

Sabah ne yayi saurin bashi ansa da "Wlh Abba, gajiya ce. Bansan lokacin da baccin ya tafi damu haka ba"

Shiru Abba yayi bai sake cewa komai ba, yana aiyano abubuwa da dama aransa. Kardai shakuwar dake tsakanin yaran nan ya soma wuce gona da iri. Wata zuciyar ce ta fada mishi "kilan da gaske ne gajiyar ce kawai tasa bacci ya kwashe su a hakan. There's nothing to be worried about" duk da hakan bai gamsu ba ya dubesu yace "kun ci abinci kuwa?"

"Eh munci Abba".

"Okay good. Ni zan haura sama na watsa ruwa tukana na koma asibiti"

Yana gama fadin haka ya juya ya haura sama zuciyarsa fal da damuwa tunani kala kala na masa yawo aka.

Abba na tafiya, Sabah da Samha suka juyo suna kallon junansu. Ganin damuwa rubuce fal a fuskar Samha yasa Sabah ya girgiza mata kansa allamun karta wani da'ga hankalinta.

Cike da sanyin jiki suka haura sama zuwa dakinsu kowa da abunda yake masa yawo aka.

Abba yana haurawa sama ya watsa ruwa a jikinsa ya fito ya sauya kaya sa'anan ya sake komawa asibiti. Yana shiga dakin ya tadda Anty fanneh idanunta biyu. Wuri ya nema ya zauna yayi shiru yana aikin tunani.

"Alhaji lafiya? Ya naganka haka, ka fita da walwala kuma ka dawo ba haka?"

Katuwar numfashi Abba ya sakar sa'anan yace "Fanneh wani abun alajabi na tadda a gida amma bazanyi saurin yanke hukunci ba. Sai nake ganin kamar shakuwar dake tsakanin yaran nan ya soma yin yawa. Gaskiya my mind is not at rest kwata kwata".

Wani irin faduwar gaba ne ya ziyarci anty fanneh nan take abubuwan da Mami ta dinga fada kafun suyi tafiya suka soma dawo mata. Toh zargin mami ya soma zama gaskiya kenan tunda har shi Alhaji dakanshi ya fito yana magana akansu? Cike da fargaba ta dago tana dubansa tace "Toh Alhaji me kake tunani za'ayi kenan game da wanan lamarin? Ni kaina na soma noticing hakan. Shakuwan nasu is getting too much".

"Hmm dazun da rana Sabah ya sameni da wata magana. Yace yana son ya koma gidansa dake can island da zama, i think kawai zanyi granting dinsa wish din kinga from there zamuyi separating dinsu hankali kwance. Sai weekends ya dinga zuwa gida, ballantana ma gidan na kusa da inda Mami take ya dinga zuwa yana dubata, ko ya kika ce?"

"Toh amma gaskiya da zai cigaba da zamansa anan musa musu ido sosai da yafi. Bana son Sabah yayi nesa damu Alhaji".

"Kinsan tunda Sabah ya taso kwata kwata baya son kusanci da mutane, ban taba ganin yaro da baya son ra'buwa da mutane kamarsa ba, harta ni mahaifinsa sai nayi da gaske. ko kaninsa Jabbar baya bari yazo kusa dashi ballantana su samu wani kusanci. Da ina tunanin kewar mahaifiyarsa ne yasa yake haka, amma sai nazo naga akasin haka because without my help Sabah ya girma ya zama mutum mai hangen nesa da sanin ya kamata. Barshi dai da fadin rai da saurin fishi amma Sabah has grown into the man i want him to become and i'm very proud of him, shiyasa koda Mami tayi maganar a damka masa family business a hannu ban musanta ba don nasan he's capable. Zuwan Samha cikin rayuwarsa naga canji da dama kamar yanda kika kawo mun canji cikin rayuwata. Daba din Samha ta rigada ta zama kanwarsa da sai a hadasu aure hankali kwance don sun san halin junansu."

"Hakane Alhaji nima da zan so hakan, dukda dai bani na tsuguna na haifi Sabah ba amma nasan yaro ne mai hankali da sanin ya kamata, zai iya kula da kanwarsa. Amma abun dubawa anan shine maganar mutane da kuma mami, kaima kasan abu da bazai taba yi'uwa bane. Kawai mu bar zancen a hakan."

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now