Chapter seventy-one

556 58 5
                                    

Cike da mamaki Abba yake kallon likitan yace "har 13 weeks?"

"Yes 13 weeks"

Wani irin dadi ne ya rufeshi ya juyo cike da murna yana kallonsu Sabah yace "Sabah! Samha! Kunji Amminku tana dauke da baby". Murna kamar ya kashe Shi sai faman zuba yakeyi.

Su kuwa Sabah da Samha tsaye suke suna kallonshi sun kasa cewa komai don gabadaya jikinsu yayi sanyi.

Godiya Abba ya shiga yiwa likitan, Samha ta tambayi likitan ko zata iya shiga ciki ta ganta. Likitan yace eh zata iya shiga ciki ta duba ta.

Cikin sauri ta karasa cikin dakin da aka kwantar da ita.

Bayan shigan Samha ciki, Sabah ya juyo yana duban mahaifinsa wanda zuciyarsa fal take da farin ciki. Shiru Sabah yayi bai ce komai ba. Abba ya dubeshi yace "Sabah ya?".

Jimm yayi daga bisani yace "Abba idan bazaka damu ba inaso na tare a dayan gidana dake island".

Mamaki ne ya cika Abba ya dago yana dubansa yace " ban gane ba. Wani ya takura zamanka ne anan?"

"A'a Abbah, gani nayi lokaci yayi daya kamata ace nima na samu muhalina nakaina. Kaga yanzu Mami tana magana za'a damka mun kamfanuka na family su dawo hannuna. So i need to settle down"

"Baby boy anya kuwa? Har yanzu fa da sauranka. Zaka iya zama kai kadai cikin wanan makeken gidan? Toh ka bari idan Kanika ya dawo daga hutun dayaje lebanon wurin mahaifiyarku sai ku koma tare".

"Gaskiya Abba nafisan na zauna ni kadai, Jabbar yana iya dawowa gida ku zauna tare a madadina"

Shiru Abba yayi daga bisani yace "toh maganar auren naka fa?"

"Zanyi nan bada jimawa ba insha Allah".

Abbah yace "Toh shikenan. Allah ya nuna mana lafiya. Ka samu ka nutsu ka zabar wa kanka mace ta gari, mai hankali da addini wace tasan ya kamata. kaga Mami itama she's expecting nothing less from you".

"Insha Allah Abbah. Zanyi iya kokarina". Sabah Ya fada sa'anan suka cigaba da tataunawa.

Bangaren Samha kuwa, Tana shiga ta tadda Anty Fanneh kwance akan gado tana ajiyar numfashi, ga ruwan drip an saka mata. A hankali ta karaso tazo ta zauna gefenta ta ruko hannunta tana fadin "Ammi...."

"Na'am Samha na".

Muryan Samha na rawa kwalla suka ciko mata idanu tace "ya jiki Ammi?kiyi hakuri Ammi nasan duk laifinane duk ni na jawo kika shiga wanan halin".

"Shhhh Baby.... karki kuma fadin haka. Nasan stress ne kawai suka mun yawa but insha Allah i'll be fine. Ina Abbanku yake?"

"Suna waje tare da Sabah".

Gyada kai kawai Anty fanneh tayi don gabadaya jikinta yayi weak. Gashi ta rame ta sake yin fari. Fatar jikinta fresh.

Bafi 10 mins ba sai gasu Sabah sunyi sallama sun shigo tare da Abbah. Cike da damuwa Abbah ya karaso wajen da Anty fanneh take kwance ya kamo hannunta yana tambayarta ya jiki. Tace mishi da sauki. Cikin murna ya soma sanar da ita abunda likita yace . Da farko da Anty Fanneh ta dan ji tsoro don bata taba tunanin tanada cigan ciki ba. Abba ne ya soma kwantar mata da hankali yana bata baki.

Har likitan ya kuma shigowa ya dubata. Bayan ya gama, Abbah ya soma tambayarshi ya jikin nata. Likitan yace zata da'an kara kwana biyu a asibitin don tana bukatan bed rest sosai.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now