Chapter Twenty - Eight

564 74 1
                                    

Cikin zafin nama Amjad ya mike daga inda yake zaune don yasan da gangan Sabah ya jefo musu ball din.

Sabah yana ganin ya mike ya kawar da kansa gefe yana fadin "mayar da wukar, mura nakeyi kuma hanuna ne ya kubuce na wurga ya zo nan".

Amjad cike da masifa ya soma fadin " Bakada lafiya meye na buga kwallo, bazaka je ka zauna kaga yanda ake bugawa ba, sai lallai ka buga?!"

Sabah bai bashi ansa ba, idanunsa ne suka sauka kan cake din daya gama rugujewa a hanun Amjad sa'anan ya dawo da dubansa ga Samha, wani irin kishi ne ya rufeshi bai san sanda ya soma fadin " Toh sai meye don a ruguza maka cake din, nima ai tayi mun nawa cake din. Zan iya baka wanan". Ya karasa maganar yana watsa mishi harara.

Samha tana jin abunda ya fada nan da nan ta cafke tace " toh ai bani na bashi cake din ba, khady ce ta bashi".
Nan da nan Sabah ya zaro ido don a tunaninsa shima Amjad din tayi masa cake din ne ta kawo masa.

Cike da mamaki Amjad ya juyo yana dubanta sa'anan yace " kinyi wa Sabah cake?"

Samha zaro idanu tayi tana kallonsa. Shima Sabah kawar da kansa gefe yayi ya kasa hada ido da Amjad.

Amjad ya matso dab dashi yana kai mishi dukan wasa " wai tsaya tukuna, ba dai kishi nake gani cikin kwayar idanunka ba, kishi kakeyi don kana tunanin Samha ta bani cake?" Amjad ya karasa maganar yana masa dariya.

"Haba Sabah, ban sanka da haka ba". Ya fada yana cigaba da masa dariya.

Sabah kunya ne ya lulubeshi, dayaga dariyar da Amjad yake masa yaki tsayawa yasa ya cire mask din dake fuskarsa ya fara mishi tari a fuska shima.

Amjad nan da nan ya kauce ya bata fuska yana fadin " Meye haka?"

"Oho ba'a sani ba" yana gama fadin haka yaja tsaki ya tafi ya barsu a wajen. Samha da Amjad suka bi bayanshi da kallo.

Samha girgiza kai kawai tayi don inda sabo yanzu ta rigada ta Saba da halin Sabah.

Misalin karfe hudu Samha ta fito daga last lectures dinta kenan, sai ga Aliyah nan tazo, idanunta duk sun shiga ciki har wata yar' rama tayi, fuskan nata a yau babu make up, sai ta zama kamar wata mara lafiya. Aliyah ta tsaya tana kallon Samha da shanyanyun idanunta daga bisani ta bude baki tace "Samha ina so na danyi magana dake idan bazaki damu muje cafeteria".

Samha bata ce mata komai ba haka tabi bayanta suka je cafeteria suka nemi wuri suka zauna. Bayan sun zauna shiru ne ya dan ziyarce su daga bisani Aliyah ta dago tana duban Samha wace ta kura mata ido tayi shiru tana kallonta, Aliyah ta soma fadin " Samha ba komai bane yasa na nema ganinki illa dana baki hakuri akan abunda Zack ya miki, nasan abunda ya aikata yanada muni, bai cancanciyafiya daga gareki ba, amma dukda haka Samha karki tsaneshi, ni yakamata ki tsana ba shi ba don nasan ni kaina nayi miki laifufuka da dama a baya amma yanzu cike nake da nadmar aikata su. Kiyi hakuri". Aliyah ta fada tana sunkuyar da kanta kasa.

Samha cike da mamaki take binta da kallo don bata taba tunanin Aliyah zata kawo kanta tana bata hakuri haka ba, nan kuma tausayin Aliyan ya rufeta, Samha ta bude baki ta soma fadin " karki damu Aliyah babu komai, komai ya wuce insha Allah. Kuma I understand how you feel da shi zack dinma har kanshi, kawai hanya daya bi don ya samo miki farin cikinki ne bai kamata ba, amma banga laifinsa ba, don so babu abunda baya sa mutum yayi".

Aliyah tayi shiru tana dubanta sa'anan ta cigaba da fadin " Shekara bakwai, samha tsawan shekara bakwai kenan na taso ina dawainiya da son Sabah, inason Sabah tamkar raina, kuma har yanzu banjin akwai abunda zai sa naji na daina sonsa, zan cigaba don son Sabah har sai ran dana  ji na daina numfashi a doron kasan nan" Aliyah ta karasa maganar tana rushewa da wani irin kuka.

Wani irin mugun tausayinta ne ya kama Samha, itama kwalla ne suka cika mata idanu. Cikin sauri ta bude jakarta ta ciro yar' karamar hanki ta matso kusa da Aliyah ta mika mata, Aliyah ta karba ta soma goge hawayenta, daga bisani ta dawo da dubanta ga Samha taga itama hawayen takeyi. Harara ta dan watsa wa Samha sa'anan tace "kukan me kuma kikeyi?"

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now