Chapter forty - three

449 51 2
                                    

Samha farkawa tayi ya tsinci kanta cikin parlourn gidansu, lulube take cikin bargo, tana kwance kan daya daga cikin three seaters din parlourn. Mika ta soma yi tana salati.

Tana Juyowa sukayi ido hudu da Sabah dake tsugune a gefenta, ya kura mata ido, fuskar nan tasa a tamke kamar bai taba dariya ba.

Gaban Samha ne ya tsinke ya fadi cikin sauri ta mike ta yaye bargon dake jikinta tana fadin "Na shiga uku, Sabah meye haka,  kar dai..."

Sabah yayi saurin katse mata maganar da take kokarin yi yace "ban gane kin shiga uku ba? Ina tunanin naki yake zuwa?"

Samha shiru tayi bata ce komai ba ta soma turo dan karamin bakin tace " ina Ammi?"

"Bata nan, nazo na tarar da gidan babu kowa sai mai gadi. Ina yar aikin gidan naku take?" Ya tambayeta.

"Anty lami bata nan, ta tafi gida wai danta babu lafiya".

Sabah ya dan tabe baki yayi shiru sa'anan yace " wai Shekarar ki nawa ne da har zaki dinga suma wa mutane saboda gajiya? Jibeta, tsohuwa kawai". Ya karasa maganar yana hararar ta.

Samha kara cinno bakinta tayi gaba ta sunkuyar da kanta kasa tana fadin " bazaka gane bane, wlh cikin yan kwanakin nan, zuciyata ta kasa samun sukuni. Bana iya bacci saboda tsanani tunani da tashin hankali"

Sabah shiru yayi yana kallonta, jikinsa ne yayi sanyi ya sunkuyar da kansa kasa, zuciyarsa na masa wani irin soyuwa dajin maganganunta.

Samha ta cigaba da fadin " zuciyata batada wani tunani illa naka dana dan uwanka Jabbar da kuma aikin project dinka da aka bata maka... da kuma......" sai kuma tayi shiru tana kallonsa sa'anan tace "wai tsaya tukuna Sabah, kaine ka dauko ni ka kawo ni gida?" Ta karasa maganar tana zaro ido.

Cikin sauri Sabah ya dago yana dubanta sa'anan yace "haba sai kace wani majiyin karfi? Taya zan dauko ki na kawo ki gida tun daga asibiti?"

" Ba haka nake nufi ba, kawai fa tambayarka nake ko......."

Murmushi Sabah ya sake ya katse ta da " iyakacin daukan dana miki shine, daga mota zuwa kan kujeran nan don haka kima kawar da wanan tunanin da kikeyi".

Samha bata ce mishi komai ba sai faman turo baki takeyi tana kunkuni.

Sabah bai tanka mata, fine eyes dinsa ya kura mata yana kare mata kallo sama da kasa sa'anan yace "Da inai miki kallon karama karama, ashe kinada nauyi haka ban sani ba?".

A harzuke Samha ta juyo zata bashi ansa yayi saurin kamota ya kwantar da ita bisa kan three seater din.

Ajiyar numfashi suka sauke a tare, Sabah ya kuro mata kyawawan idanunsa. Itama shiru tayi tana kallonsa.

Idanunsa ne suka bar cikin nata suka sauka kan karamin soft lips dinta, ya kura musu ido.

A hankali ya soma matsowa da fuskarsa zuwa dab da nata har suna iya shakkar numfashin junansu.

Samha wani irin feelings ne takeji yana tasomata a lokacin. Ga kamshin dadaden turensa daya mamayeta.

Kirjinta ne ya soma bugun uku uku, don a lokacin wani irin tsoro ne ya soma ziyarta ta saboda yanda take ji a game da Sabah a lokacin, She can't seem to control those feelings towards him don ya rigada ya zame mata tamkar jinin jikinta dashi take rayuwa. Ji take idan babu Sabah a yanzu bazata iya rayuwa ba.

Sabah lumshe idanunsa yayi a hankali sa'anan ya budesu ya zubesu cikin nata, yana kallonta ya hango tsoro da fargaba karara a idanunta.

Murmushi ya sake sa'anan ya kai lips dinsa ya manna bisa goshinta yayi mata soft kiss a wajen sa'anan ya dago yana dubanta yace " ki samu ki huta, ina zuwa". Yana gama fadin haka ya juya ya bar parlourn.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now