Chapter sixty-eight

411 44 2
                                    

Kunya ne ya lulube Samha ta sunkuyar da kanta kasa.

Sabah ya matsa baya ya jingina da jikin kujera ya lumshe idanunshi yana sauke ajiyar zuciya a hankali yace "kanwata....."

Da kyar Samha ta iya dago kanta ta zuba mishi manyan idanunta, kura mishi ido tayi tana kallon flawless face dinsa wanda idanunshi a lumshe yake yana mayar da numfashi a hankali, nan take taji sonsa ya sake mamaye zuciyarsa. Babu macen da zata ga Sabah bataji matsanancin sonshi ya kamata ba, komai nashi daban yake da sauran maza har yau bata ci karo da namiji daya tattara komai irin nasa ba. Tabbas yanzu ta rigada ta gama tabbatar wa kanta cewa bazata iya rayuwa da wani da' namiji in bashi ba, sonsa a jininta yake.

Jin shirun yayi yawa ne yasa ya bude kyawawan idanunsa ya sauke su akanta. Dagowa yayi yana matso kusa da ita ya kamo hannunta cikin nashi yana shafawa a hankali yace " Kanwata yaushe zamuyi aurenmu?"

Shirun dayaji tayi ne yasa ya cigaba da fadin "gaskiya idan Abba ya dawo zan fada mishi ya sanar da Mami, ke nakeso. Kuma a barmu muyi aurenmu".

Zaro ido Samha tayi ta soma girgiza masa kanta tace "No Sabah... we can't. Da wani ido kakeso na kalli Ammi? Kaima kasan bazasu taba amince mana ba".

Sabah yace " Toh sai me in sunki amincewa? I don't care, we'll just do it our own way, aure tsakanina dake ya hallata. Ko sunqi ko sunso ke nakeso kuma ke zan aura, and that's final"

Samha jin maganar nasa tayi kamar daga sama, cike da tashin hankali ta soma girgiza masa kanta tace "bazan iya ba Sabah..."

"Don't say that kanwata...wanan itace kadai mafita a garemu idan har nida ke muna so mu cimma burinmu, nidai kawai amincewarki nake bukata, ki bar komai a hannuna, i'll handle it. Don't you love me?"

Samha rasa me zata ce mishi tayi wasu hawaye masu zafi suka soma zubo mata.

Hankalinsa ne ya soma dagawa ganin yanda take zubda hawaye don haka ya janyota ya matseta gam a jikinsa ya kwantar da ita daidai saitin zuciyarsa dake faman aikin bugawa. Hannu yasa ya soma share mata hawaye yace " ki saurari yanda zuciyata take bugawa akanki kanwata, bazan iya rayuwa babu ke ba, haka nan Allah ya jarabceni da matsanancin sonki, kuma a yanzu haka banida wata buri daya wuce na mallakeki a matsayin matata ta sunnah. Please ki amince zaki aureni".

Suna cikin haka suka soma jin muryan Anty fanneh tana kokarin saukowa kasa. Babu shiri Samha tayi saurin kwace jikinta daga nashi ta mike tsaye kirjinta na harbawa.

Anty fanneh ta karaso ciki fuskarta dauke da murmushi ta nema wuri a gefen dining ta zauna, ta soma bude album din hotunan dake hannunta tana fadin "yau tuna baya za'ayi. Bari muga hotunan birthday girl".

Mikewa Sabah yayi daga inda yake zaune fuskarsa dauke da murmushi ya kashewa Samha ido daya sa'anan ya karasa wurin dining ya janyo kujera daya ya zauna kusa da Anty fanneh, jiki babu kwari itama Samha ta karaso wurin ta tsaya.

Hoto na farko suka soma dubawa inda Samha take rungume jikin mahaifinta suna murmushi, kamarsu daya tamkar an tsaga kara, komai nashi Samha ta dauko.

Anty fanneh ta kurawa hoton ido hawaye na cikko mata idannu amma tayi kokari ta danne tace "zuwan Sameer yasa na tuna abubuwa da dama da suka faru a baya".

Sabah ya kurawa hoton Samha ido yace "ashe daman kanwata tun tana karama takeda kyau haka?"

Cikin sauri Samha ta kai mishi dukan wasa tana mishi alamu da ido da yayi shiru, kirjinta na harbawa don tsoro take karya furta wata magana, Anty fanneh ta soma suspecting.

Amma Anty fanneh kwata kwata ma hankalinta na kan hotunan da suke kallo bata dau maganar nasa da wata manufa ba tayi dariya tace "jiya ba yau ba, kaga yanda kanwar taka ta girma ko Sabah?"

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now