Chapter Nineteen

562 68 0
                                    

Zuwa karfe shida na yamma abba ya kira sabah a waye, yace ya samesu a new castle, suna can shi da anty fanneh. Sabah yace mishi toh gasu nan zuwa. Nan ya sallame su shinoh shida samha suka shiga cikin mota. Ya ja suka tafi.

New castle babban wurin shakatawa ne mai dauke da dinbin jama'a da suke zuwa da iyalensu domin shakatawa.
Musaman abba yasa akayi musu reservation na VIP wanda daga shi sai family dinsa zasu kasance a wurin. Abba da anty fanneh suna zaune suna hira, sai faman janta da wasa yakeyi kamar wani sabon saurayi da budurwa. Anty fanneh itama sai faman murmushi takeyi. Su sabbah suka shigo suka tadda su. Sabah Tabe baki yayi ganin yanda mahaifin nashi yake wani barin jiki kaman wani karamin yaro. Karasowa yayi ya gaishe su ciki ciki ya nema wuri ya zauna. Ita kam samha cike da farin ciki tazo ta rungume amminta tana mata sannu da zuwa, bayan sun gaisa ta nema wuri itama ta zauna. Nan hira ta barke tsakaninsu. Sabah bai sa musu baki ba sai wani ci cin magani yakeyi. Samha ce ta dan buge shi ta gefe tana masa alamu daya sake jiki mana ayi hira dashi, yayi kamar bai jita ba. Har abba ma yayi kokarin janshi da hira ya basar, haka suka kyaleshi.
Daga baya ne ya dan sake ya soma sa baki jifa jifa cikin maganarsu amma yanwanci maganar da yakeyi da samha yakeyinta.
Anty fanneh ta dube abba tana fadin " kaga abu yayi kyau koh, yara sun hada kansu gaskiya naji dadi, Allah yasa ku dore a hakan. Ta karasa maganar tana dubansu. Abba yace Ameen shima ya nuna jindadinsa.

"Karki damu ammi, Insha Allah zamu cigaba da hada kanmu". Samha ta fada mata

Sabah ne ya juyo yana kallonta fuskarsa dauke da murmushi ya soma magana kasa kasa yanda ita kadai ce zata iya jiyo maganarsa " karki damu kanwata, ai nan gaba zamu shirya sosai fiyye da yanda kike tunani don Ke kanki ma abun sai ya baki tsoro." Ya karasa maganan yana daga mata gira daya.

Samha kirkiro murmushin karfin hali tayi bata ce masa komai ba ila hararar data watsa mishi ta gefen ido don tasan halin shi sarai, idan ta tanka masa zai iya furta wata magana wanda bata shirya ji ba a gaban su Ammi. Haka suka cigaba da hirarsu cike da jindadi da anashuwa.

Aliya tsaye take a wajen reservation din VIP ta kura wa su sabah ido. Yanda suke hira cike da anashuwa da jindadi ba karamin kona mata rai yakeyi ba. Wayarta ta ciro daga cikin aljihu tayi saitin daidai table dinsu inda suke zaune ta daukesu hoto. Tana gama daukan hoton ta kama hanya tayi tafiyarta. Su sabah suna zaune basu ma san abunda ke faruwa ba. Haka suka cigaba da hirarsu har lokaci yayi suka tashi suka wuce gida.

Washe gari da safe su samha suna cikin lab inda ake ajiye computers zasuyi daya daga cikin courses din dasuka dauka daga computer science wanda ya zame musu core course. Lecturer din na gama yi musu bayani yace su fara practical. Suna cikin practical din amina ta tabo samha tana kokarin nuna mata abu cikin wayarta da aka turo a group din ajinsu. Samha ta matso don taga abunda take kokarin nuna mata, hotonsu ta gani ita da sabah da mahaifin sabah da kuma mahaifiyarta a cikin wayar. Daga ganin hoton kasan jiya da dare ne aka yita da sukaje new castle. Samha tana ganin hoton bata san lokacin data mike tsaye a razane ba har yan ajin suka juyo suna kallonta. Ashe ba amina ba harta sauran yan ajin sun ga hoton a group, suna kallon cikin wayarsu kuma suna kallonta suna gulma kasa kasa. Lecturer dinsu ne ya dube ta yana fadin " keh meye haka? Idan baki shirya yin practical din ba, ki fita ki bar mun aji".
Samha sunkuyar da kanta tayi cike da jin kunya ta bashi hakuri ta nema wuri ta zauna.
"Waye ya turo da hoton cikin group?" ta tambayi amina muryarta kasa kasa.

Amina ta bata ansa da " naga kamar wata ta rubuto a group din wai wata Aliya ce daga mass com department ta turo.

Samha najin aliyah ce nan da nan ta mike tacewa amina tana zuwa, nan taje ta dauki excuse a wurin lecturer ta bar ajin sai hanyar mass com department. Tana zuwa 400 level class ta soma tambayar daluban ciki ko Aliyah tana nan. Sukayi mata nuni da can karshen ajin inda take zaune ta hakimce kan kujera kamar wata sarauniya. Aliya tana ganin samha fuskarta ta barke da murmushin makirci, don tasan abunda ya kawota. Mikewa tayi daga inda take zaune tazo ta tsaya dab da inda samah ke tsaye.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now