Chapter seven

716 103 2
                                    

Samha bata ce komai ba illa wani irin kallo data dinga binshi dashi. Anty fanneh ta karaso dashi cikin fallo tana mishi sannu da zuwa nuni ta mishi da kujera daya zauna. Sabah cikin girmamawa ya samu wuri ya zauna sa'anan ya gaisheta. Cike da fara'a anty fanneh ta ansa mishi
tana tambayarsa mutanen gida. Ya bata ansa da duk suna nan lafiya. Bayan sun gama gaisawa ta mike tace tana zuwa ta shiga kitchen. Ya rage daga samha sai shi.
Harara ta galla masa sa'anan ta bude baki tana fadin " meya kawoka gidan mu? Ko ka biyo ni har gida ne kaga ka kara musguna wa rayuwata?" Ta jefo mai tambayar.

Shima harara ya galla mata hade da jan tsaki sa'anan yace " keh fa kin cika daukan kanki da muhimanci dayawa. An gaya miki nasan cewa nan ne gidanku? Ai dana san zan ci karo dake a gidan nan bazan ma bata lokacina nazo ba"

"Toh ai yanzu ma bata bace ba, zaka iya tashi kayi tafiyarka tunda lokaci bai kure maka ba" Ta gaya mishi hade da daga murya.

Anty fanneh da take kitchen tana kokarin hada mai kayan lemun da zai sha ta jiyo samha tana faman daga murya. Da sauri ta baro kitchen din ta shigo fallon taga samha ta bata rai kamar zata rufeshi da duka" wai samha akwai abunda yake damunki ne yau dinan. Bakon namu ne kike yiwa tsawa haka? Meye haka?" Ta tambayeta.

Samha turo baki tayi tana galla masa harara. Shi kam murmushin mugunta ya sakar mata ta bayan anty fanneh. Ai kam nan da nan ta cika tayi fumm cike da fushi ta mike fuuuu tayi hanyar sama ta shige dakinta.
Anty fanneh ta bita da kallon mamaki, toh wai me ke faruwa ne. Don bata san dalilin dayasa samha take haka ba. kirkiro murmushi tayi tana duban sabah wanda kanshi a sunkuye yake cike da jin kunyar anty fanneh. Hakuri ta sake bashi akan abunda samha ta mishi, yace mata babu komai. Lami ta kira tace mata ta kawo mishi kayan motsa baki. Lami ta shiga kitchen ta debo lemun sanyi ta fara ajiye mishi akan table dake gabansa. Daga bisani ta koma ta debo mishi abinci ta kawo mishi. Lemun kawai sabah yasha , suka sake gaisawa da anty fanneh. Nan suka dan taba hira tana mishi tambayoyi game da karantunsa da sauransu. Anty fanneh taji sabah ya shiga mata rai farar daya, ko don kamar dataga yanayi da mahaifinsa ne. Gashi kuma tana ganin bazasu samu matsala ba don ta lura kamar yaron yanada hankali. Suna cikin maganarsu sai ga kiran mahaifin sabah nan ya shigo wayarta ta daga. Bayan sun gaisa ya fara tambayarta ko sabah ya zo tace mishi eh gashi nan ma suna tare. Yace to yayi kyau sai zuwa anjima sai sake kiranta. Sukayi sallama ta kashe wayar. Suka cigaba da maganansu. Dayake anty fanneh batada matsala nan da nan ta fara janshi a jiki kamar wani danta har ta samu ya sake jiki sunata faman hira.
Bayan kusan minti talatin sabah ya duba lokaci yace zai wuce, bai son dare ya masa. Anty fanneh tace toh ya dan jirata tana zuwa. Nan ta haura sama ta debo mishi kaya kala kala ta zuba cikin jaka ta sauko kasa ta mika mishi tace gashi ya kaiwa kakarsa hajiya bilkisu. Godiya ya mata yace zai mika sakonta.

" toh sai yaushe kenan sabah".

"Insha Allah nan bada jimawa zaki sake ganina Anty" ya bata ansa.

Taji dadi tace "toh shikenan nagode sosai sabah sai ka sake zuwa, ka gaishe mun da mahaifinka da mutanen gida"

Yace toh zasu ji sukayi sallama yaje inda yayi parking motarsa yaja ya tafi.

Sabah yana barin gidan, anty fanneh ta haura sama cikin sauri ta nufi hanyar dakin samha ranta a bace. Tana shiga ciki ta tadda ta zaune a kan gado gabadaya tayi wani iri sai faman hucci takeyi.

Nan take Anty fanneh ta fara mata fada ta inda take shiga ba tanan take fita ba, har bata san sanda ta fashe da kuka ba don abunda samha tayi ya mata ciwo don tana ganin kamar bata son ta sake wanan auren ne shiyasa tayiwa sabah haka. Samha tana ganin ammi ta fashe da kuka hankalinta ya tashi ta matso kusa da ita ta fara bata hakuri tana rarashinta.

Cikin sheshekar kuka ammi take fadin "yanzu samha don baki son na sake wani auren shiyasa kikayi wa yaron mutuminan wulakanci dazu? Ai da kin fito filli kince mun baki san wanan auren ba sai kin fake da wulakanci ba, halin da ban sanki dashi ba. Wallahi kin bani mamaki. Yanzu idan yaje gida ya fadawa mahaifinsa da wani ido zai kalleni eh samha. Kin wulakanta ni yau wlh. Amma babu komai."

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now