Chapter forty

540 48 11
                                    

Samha zatayi magana ya sake katse ta da "kuma ki daina bin bayan mutane kina tambayoyi da cigiya akansu. Babu kyau".

Samha ranta ne ya soma bacci tace "ba saboda na damu da kai bane yasa kaga nake yin haka. Ban san meya faru tsakaninka dashi a baya ba, kuma bansan me kake tunani ba yanzu nidai kawai nasan you're closing off. You're not allowing anybody in. Ni kuma bazan iya ganinka a haka ba nayi shiru na kyale. Sabah pls ka fada mun meke faruwa tsakaninka da dan'uwanka Jabbar?" Ta tambayeshi cike da damuwa.

Sabah wanda maganganunta sun rigada sun kawo mishi wuya, a fusace ya jefo da ledan chips din gabanta yana fadin "Wai meyasa kikeda shishigi ne haka?! Eh?! Kin sani a gaba, dole ne sai na fada miki?!Nifa bana son irin haka!" Ya fada a tsawace, tsaki yaja ya tafi ya haura sama zuwa dakinsa.

Samha tabi bayanshi da kallon takaici kamar zatayi kuka. Ta rasa gane meyasa Sabah yakeda zuciya da taurin kai haka. Cike da sanyin jiki ta juya ta soma kokarin kamala girkin.

Sabah yana shiga daki, sai faman hucci yakeyi ya cire jakansa yayi flinging dashi a kan gado.

Wuri ya samu a gefen gadon ya zauna ya dora kansa bisa hanayensa. Wani irin Sara yaji kansa na masa, ji yayi abun duniya duk yabi ya isheshi a lokacin.

Dagowa yayi idanunsa suka sauka kan drawer dake kusa da gadonsa. Bude drawer din yayi, ya ciro wani frame ya kura masa ido.

Frame din dauke yake da hotonsa yana karami, ga Jabbar a gefensa shima lokacin yana karami, sai kuma mahaifiyarsu da take rike dasu itama tana murmushi akayi musu hoton.

Kusan minti biyar ya dauka yana karewa hoton kallo, zuciyarsa na masa wani irin kuna. Shi kadai yasan yanda yakeji a duk sanda yaga wanan hoton.

Tunani kala kala ne suka dinga masa yawo a ka, ga Samha daya gama mata ihu a kasa, gabadaya sai yaji duk babu dadi don yasan so kawai take ta sassanta shi da dan uwansa. Tausayinta ne yaji ya kama shi, cikin sauri ya mike ya fito daga dakin ya soma saukowa kasa.

Yana karasowa yazo ya tarar da abinci kan dining an jera da wata yar karamar takarda da akayi rubutu ciki an ajiye a gefen plates.

Kitchen ya leka, nan ma bai ganta ba. Ya dawo wajen dining din ya dauki takardan ya soma karanta abunda aka rubuta ciki kamar haka

"Ni na wuce, ga abincin nan na gama, ka samu kaci da zafinsa".
- Samha

Jikinsa ne ya kara yin Sanyi. Ya tsaya yayi shiru yama rasa abunda zaiyi.

************************

Samha tana isa gida, jiki a sanyaye ta haura sama zuwa dakinta. Kayanta ta cire ta fada bayi tayi wanka ta dauro alwala ta fito tasa kaya tayi Sallah.

Tana idar wa ta mike ta fito, dakin Anty Fanneh taje tayi sallama ta shiga ciki. Anty fanneh dake zaune bisa kan gado tana ninke kaya, ta ansa sallamar tana fadin "Baby har kin dawo?"

"Na dawo Ammi, sannu da gida"

Anty Fanneh ta ansa da "yauwa baby, ya makarantan yau?"

Samha ta ansa da "lafiya lau Ammi. Naga yau kin dawo da wuri".

Anty fanneh tace "wlh kam, babu aiki ne sosai a office, shiyasa".

Samha tace "toh"

Shiru ne ya dan ziyarce su daga bisani Samha ta dago tana duban Anty fanneh tace "Ammi kinsan Abdul-Jabbar kanin Sabah?"

Ammi cike da mamaki ta dago tana dubanta sa'anan tace "kina nufin dayan yaron Alhaji?"

Samha ta gyada mata kai.

Anty fanneh tace "eh, idan zan iya tinawa ya fada mun cewa yanada wani da' sunan shi Abdul-Jabbar. Kamar shekara biyu ne tsakaninshi da Sabah. Rabuwan mahaifiyarsu da Alhaji ne yasa ta dauki Abdul-Jabbar ta tafi dashi tun yana karami"

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now