Chapter Twenty-Two

543 67 0
                                    

Da kallo na kisa da tuni samha ta hankada lahira don wani irin banzar kallo Aliyah ta dinga watsa mata.

Samha ta mike daga inda take tsugune jiki babu kwari don gabadaya jikinta ya rigada ya gama yin sanyi. Wani tunanin ne yazo mata nan ta kudiri niyan bazata bari Aliyah ta samu nasaran kwace mata sabah ba kuma dole tayi accepting din soyayyar dake tsakaninta da sabah.

Wanan tunanin ne ya bata karfin gwuiwa, zuwa tayi ta dauko towel din fuskarta dauke da murmushi ta soma takowa a hankali har tazo ta tsaya a gaban sabah ta mika mishi towel din.

Sabah murmushi ya sake ya karba towel din sa'anan yace " kanwata yau babu rigima kenan, an sauko ana bada hadin kai"

Samha murmushi ta sakar masa tana binsa da kallo cike da so da kauna, ita kadai tasan yanda take jinsa a cikin zuciyarta.

Bayan an gama practice, Samha ta fito daga cikin gym din zata sauka kasa, kamar daga sama taji murya Aliyah na fadin "keh dinan naga alama kinada taurin kai har yanzu kin kasa sanin matsayinki, bayan duk kashedin dana dinga miki."

Samha ce ta juyo tana dubanta daga bisani ta bude baki tace "Amma wlh ke dinan kinada katuwar matsala, wai me na miki a rayuwar nan da zaki saka ni a gaba haka?"

"Ni din ce keda katuwar matsala? Tukuna, Ai baki ga komai ba, indai akan prince ne babu abunda bazan aikata ba, so tun wuri ina kara miki kashedi, idan kina son kanki sa zaman lafiya ki fita daga harkarsa kuma ki tsaya a matsayinki na kanwarsa". Ta bata ansa kai tsaye.

Samha ce ta dan nesa sa'anan ta cigaba da fadin " nikam ban ma san mezan ce miki ba amma ina son ki san wani abu guda daya, kinga wanan kiyayyar da kike nuna mun bashi zai sa na daina son sabah ba"

Wani irin dariya Aliyah ta sake tana duban samha sa'anan tace " Har kin bani dariya amma idan baki manta ba nasha fada miki ke dinan abar wasa ce wurin prince, idan ya gaji zai rabu dake ne don banga abunda zai saka shi ya so yarinya kucaka irinki ba, me zai ci dake"

Cike da jin haushi samha tace " Ban gane ba. Me kike nufi".

Aliyah ta bata ansa da " Bakisan cewa komai wuya komin runtsi prince yana tare dani ba. Sa ido kiyi kallo saboda a karshe ni dinan da kike gani ni zai zaba". Aliyah ta karasa maganar tana aika mata da wani irin shu'umin murmushi, tana gama fadin haka, ta kada kai tayi gaba ta bar samha tsaye a wurin.

Aliyah bata yi nisa ba, samha na tsaye tana bin bayanta da kallo cike da takaicin kalamanta. Kamar daga sama taga wasu yan mata sun bullo from nowhere sun sha gaban Aliyah. Daya daga cikinsu ce ta daga hannu ta wanke Aliyah da wata irin wawan mari tana fadin " keh jahilar banza jahilar wofi, yau Allah ya kamaki, sai munyi maganani wanan shegiyar bakin naki da kike yiwa mutane tsiwa dashi, daman mun jima muna timing dinki cikin makarantar nan, yau dubun ki ya cika"

Daya daga cikin yan matan ne ta kamo kan Aliyah ta hade da jikin bango, wani irin jiri ne ya dibi Aliyah ta fadi a kasa, nan da nan yan matan suka rufu a kanta, naushi da duka suke ta sakar mata ta ko ina, tana ihu.

Samha ganin abunda ke faruwa tazo a guje tana kokarin ta kwace Aliyah daga dukan da yan' matan ke mata.

Daya daga cikin yan' matan ta ture samha gefe tana fadin "keh mallama ki kauce mana a nan ki bamu wuri don ba dake muke ba"

Samha dataga da gaske suke kuma bazata iya kwatar Aliyah ba, yasa ta kwasa a guje ta bar wurin ta koma cikin gym don ta kira su sabah. Bata tsaya ko'ina ba sai inda ta barsu kafin ta fito, nan ta ganshi tsaye tare da zack suna magana. A guje ta karasa gabansu tana haki tana fadin "sabah kuzo ku ceci Aliyah, ga wasu yan'mata a waje sun kamata da duka".

Sabah yana jin wasu yan'mata sun kama Aliyah da duka bai tsaya yaji sauran maganganunta ba ya kwasa a guje yayi hanyar fita daga cikin gym din. Gudu yakeyi zack na biye dashi a baya. Itama samha bin bayansu tayi tana gudu. Basu tsaya ko'ina ba sai wajen gym din, nan ya hango inda yan'matan suka rufu akan Aliyah sai faman bugunta sukeyi.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now