chapter one

3.2K 116 3
                                    

Samha Abdullahi Bamanga, zaune take cikin aji a seat din dake row na biyu da littatafai zube a gabanta. Sanye take cikin kananan kaya. Bakar riga da pink skirt ne a jikinta kuma kayan sun amshe karamin jikin ta, sai dan karamin bakin dankwalin data daura a kanta. Gyara zaman glasses din dake manne bisa fuskarta tayi, tana cizon murfin biro dinta a hankali kamar yanda ya zame mata jiki. Gabadaya tunaninta baya kan abunda ake koyarwa. Hankalinta da tunaninta sun karkata zuwa ga Amjad Tafida dake zaune a seat din gaba, kurawa gefen fuskar sa ido tayi, koh kyaftawa batayi, fuskarsa take tabi da kallo tana jin kamar ta janyo shi kusa da ita tasa hannu ta shafo kyakyawar fuskarsa ko zata samu sassauci a zuciyarta. Gangar jikinta ne yake ajin amma ruhinta gaba daya ta tafi da tunanin Amjad. Tana wata uwa duniyar tunaninshi.

Ba karamin crushing Samha takeyi akan Amjad ba don tun suna aji daya ta kamu da sonshi. Amjad kyakyawa ne sosai kuma na ajin farko, kasancewarsa Hausa Fulani. Gashi shuru shuru bashida hayaniya. Yana daya daga cikin dalibai masu kokari sosai a department din. Duk ajinsu babu wanda yakeda GPA daya kamo nashi. First class student ne shi.

Lecture hall din Maths301 yayi shiru. Babu abunda kakeji sai muryar Professor Adeyinka Bayode wace take ta faman yi musu bayani. Bayaerabiya ce matar kuma ta dan jima tana koyar da maths a department din saboda kwarewarta a course din. Rubutu ta farayi da marker a board Ga projector a gefenta yana haskaka musu duka course outline din.Daliban da suke cikin ajin sun kai kusan sittin da wani abu, Kowa ya nutsu yayi shiru ana sauraron ta.

Seat mate din Samha, khadija yakasai wace ta kasance aminiyar ta dan taba ta fara magana a hankali yanda Proff Adeyinka bazata ji su ba.
" keh , proff fa na kallon ki, samha....
Amma inaaa samha bata ajin. Proff Adeyinka kamar ance ta juyo sai idanuwanta suka sauka kan Samha dake ta faman kallon Amjad. Ranta ne ya bace, don ita bata son tana koyarwa taga ba a mayar da hankali. Kiran sunan Samha tayi tace ta tashi tsaye. Shuru kakeji, har yan aji suka juyo suka fara kallonta. Amma ita kam bata ma San sunayi ba. Zuwa inda take zaune Proff Adeyinka tayi ta buga desk din dake gabanta da karfi, firgigit Samha tayi ta farfado daga duniyar tunaninta.

Dariya yan ajin suka fara yi. Don yanda ta firgita har ta kusan fadowa daga kan kujeran zamanta.

" stand up my friend!, ina koyarwa kina wani abu daban koh, you're very stupid. Proff Adeyinka ta fada a tsawace.

Mikewa samha tayi jikin ta na rawa, gaba daya kunya ya rufe ta, musamman yanda taga kowa na mata dariya. Amjad ma ya jiyo amma shi Kura mata ido kawai yayi yana kallonta. Ji tayi kamar kasa ta bude ta shige ciki.

" I'll deal with you later, meet me in my office after this class. Proff Adeyinka ta fada mata sa'anan ta barta a tsaye ta cigaba da koyar da class din.

Bayan an gama class samha tabi Proff office dinta kamar yanda ta umarce ta. Anan tayi ta faman yi mata fada, akan rashin mayar da hankalinta da takeyi kan karatu, nasiha tayi mata sosai sa'anan ta sallameta.

Tana fitowa daga office din akayi ringing siren na makarantar allamar za ayi short break kafun next lecture.

Staircase ta fara haurawa don komawa aji sai ta hadu da khadija wace itama ta sauko kenan zata je cafetaria. Khadija tana ganinta nan take ta fara mata fada tana fadin " Haba samha why will you always allow this to happen, nasan kina son amjad amma sai kinyi har mutane sun gano hakan? Idan har yan aji suka gano wlh Zaki zama topic har zaman ajin ya gagaremu daga ni har ke da Amina".

Ajiyar zuciya samha tayi tace " naji besty, amma bazaki gane baneh, idan na ga amjad gabadaya rasa yanda zanyi nakeji. I can't seem to control my feelings over him".

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now