Chapter Eighteen

583 72 2
                                    

"Meye haka sabah? Ka cika mun hannu na shiga ciki." Ta fada tana watsa mishi wani irin kallo. Kirjinta sai faman bugu yakeyi don jin lalausar hanunsa ya riko nata.

"In naki fa? Me zakiyi?" Ya jefo mata tambayar yana kallon cikin kwayar idanunta.

"Wlh sai in sa ihu a gidan nan kowa ya fito. Harta abba ma sai ya jimu dakai".

Murmushi kawai ya sakar mata wanda yasa dimples dinsa suka bayana " kanwata kenan. Toh bazan sakar miki hanun ba kiyi ihun muji"

"Oh haka kace? Bazaka sakar mun hannu ba?"

"Eh naki bazan sakar ba." ya bata ansa.

"Toh wlh zan baka mamaki a gidan nan" tana gama fadin haka ta bude baki zata sa ihu yayi sauri yasa dayar hanunsa ya toshe mata baki yana girgiza mata kansa alamun karta kuskura. Saukan cizon dayaji a tafin hanunsa ne yasa yayi saurin janyewa yana yarfa hanunsa. Tana ganin ya saketa tayi sauri ta shige dakin tasa key a kofar ta kulle tana Ajiyar zuciya. Juyawa tayi ta jingina a jikin kofar. Nan take kuma taji wani irin feelings na taso mata game dashi. Lumshe idanunta tayi har lokacin tana iya hango kyakyawar fuskarsa. Ji tayi kamar ta bude kofar ta fito ko zata sake ganinsa. Amma kuma sai ta sauya tunani. Ta rasa gane meke damunta kwana biyun nan don batada wani tunani sai na sabah. Murmushi ta sake ta bude idanunta a hankali ta daga jinginan datayi a jikin kofa ta karasa cikin bayi ta dauro alwala tazo ta tadda sallah. Bayan ta idar ta bi lafiyar gado, ta kwanta cike da tunaninsa.

shikam sabah bayan shigewarta daki yayi shuru yana bin kofar da kallo daga bisani ya girgiza kai ya dauki hanyar matakala ya sauka kasa ya dauko robar ruwa ya bude ya soma sha. Daman abunda ya fito dashi kenan. Yana gama shan ruwan ya sake haurawa sama ya shige cikin dakinsa.

Washe gari da safe samha da tunanin amjad ta shiga cikin makaranta ta soma neman sa don tana ganin lokaci yayi daya kamata su warware komai dake tsakaninsu. Ana gama lectures zasu fita daga cikin aji ta tsayar dashi a lokacin dayake kokarin fita shima. Juyowa yayi yana dubanta. "Amjad idan bazaka damu ba, inason na danyi magana da kai". Bai ce mata komai ba ya tsaya yana kallonta. Gefe taja shi don yawancin daluban da suka fito daga cikin ajin suma sun juyo suna kallonsu. Amina na ganin abunda ke shirin faruwa ta bar wurin cikin sauri taje neman khadie ta sanar da ita.

Amjad ne ya bude baki yana fadin "ina jinki, wani magana kikeso ki fada mun?"

Samha ta dago tana dubansa daga bisani ta bude baki ta soma fadin "Amjad kayi hakuri ka yafeni. Nasan ban kyautata maka ba, banida kirki kuma na tafka babbar kuskure a gareka. Shiyasa naga bai kamata mu cigaba da kasancewa tare da juna ba don idan muka cigaba a hakan, ba abunda zan dinga janyo maka ila bakin ciki."

Amjad kamar saukar guduma yaji a kirjinsa game da kalamanta. Wani irin faduwar gaba ne yaji ya ziyarci zuciyarsa dayaji tace su rabu.

Samha bata tsaya nan ba ta cigaba da fadin " duk abubuwan da suka dinga faruwa cikin yan kwanakin nan duk laifi nane. Amjad bazan boye maka ba a yanzu haka na kamu da son wani, akwai wanda zuciyata take so. Kuma ba wani bane ila sabah. Na waye gari na tsinci kaina da matsanancin sonsa. Kayi hakuri amjad da waenan kalamun dakaji suna fitowa daga bakina. Naga ya kamata ka sani ne, banson na yaudareka. Kuma ina maka fatan alkhair Allah ya baka wace ta fini."
Ba amjad kadai ba hatta su khadie da suka labe a jikin kofa suna sauraransu jin maganar sukayi kamar a mafarki.
Sabah da samha?
Anya kuwa samha na cikin hayacinta take waenan maganganun? Su khadie suka tambayi kansu.

Amjad yayi shuru yana dubanta. Shi kadai yasan yanda yakeji a lokacin don maganganunta sun rigada sun gama hargitsa masa tunani. Bai ce mata kala ba a hankali ya soma kokarin barin wajen yana tafiya kamar wanda kwai ya fashe masa a ciki. Har ya kai wajen sauka daga matakala ya kirkiro murmushin karfin hali ya juyo yana dubanta sa'anan yace " karki damu wanan ba matsala bace, saboda nima naji son naki ya fita daga cikin zuciyata". yana gama fadin haka ya juya yayi tafiyarsa. Nan ya barta tsaya hawaye na gangaro mata bisa kuncin.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now