Chapter sixty - six

448 47 4
                                    

Bangaren Samha kuwa gabadaya hankalinta a tashe yake. Gudu takeyi har bata iya ganin gabanta, babu abunda yake mata yawo aka illa tunanin rashin adalcin da take ganin sun yiwa Madina na barinta cikin duhu.

Bata tsaya ko ina ba sai can saman benen building dinsu. Tana isa saman benen ta rushe da wani irin kuka mai tsuma rai.

Sabah sai faman gudu yakeyi har ya iso wurin building din department dinsu, zack na ganshi ya soma kokarin masa magana, Amma ko tsayawa Sabah baiyi ba ya saurareshi ya hankadeshi gefe.

Su shinoh ya tadda a gaba suma suna tahowa ya hankadesu gefe ya wuce.

Cike da mamaki suka soma binsa da kallo, Zack ne suka gani yazo yabi bayan Sabah cikin sauri. Suma basu tsaya wata wata ba suka mara mai baya.

Can saman benen Sabah ya haura, sai faman hakki yake yana ajiyar numfashi tsabar gudun dayasha.

Waige waige ya soma yi, nan ya hangota zaune ita kadai a can gefe ta kifa kanta cikin gwuiwowinta tanata faman sheshekar kuka.

Wani irin tightness ne yaji har cikin tsokan dake makale cikin zuciyarsa ganin rabin ransa a zaune cikin irin wanan yanayin.

A hankali ya soma takowa har ya karaso inda take zaune yazo ya tsuguna a gabanta yana fadin "Samha kukan me kikeyi anan?"

Samha bata dago ta kalleshi ba ta girgiza masa kai tace babu komai sa'anan ta cigaba da kukan da takeyi.

"Magana fa nake miki kina girgiza mun kai".

Cikin sheshekar kuka muryanta na rawa tace "nna...na rasa yanda zanyi ne Sabah. Ban san inda zansa raina ba na samu saukin radadin da take mun. A dalilin sonka gashi ina hurting mutane da dama. Wai laifi ne don zuciyata ta kasance tana sonka?".

A fusace Sabah yace " I don't care who i hurt indai akan sonki ne, ke kadai nakeso kuma ke kadai zuciyata takeso kuma take  burin ta karasa sauran rayuwa da. Idan bake ba, I don't want anybody else".

Jin kalamansa ne yasa bata san sanda ta mike ta fado kansa ba ta rungumeshi tsam a jikinta har suna faduwa a kasa tare.

Jewelry box din dake dauke da zoben da Madina ta bata ne ya fadi ya tarwatse a kasa.

Idanun Sabah suka sauka kan zoben a gefe, dagota yayi daga jinkinsa ya dauko  zoben yana kare mata kallo yace "wanan zoben fa, a ina kika ganta?"

"Madina ce ta tsinta tace na kawo maka".

Kamo hanunta yayi cikin nasa ya zira zoben a yatsanta na dama yace "no need, daman saboda ke na siya. Na siyo miki ne a matsayin birthday gift dinki. Ki tabbatar kina sata kullum".

Gyada masa kanta Samha tayi tana murmushi cike da tsantsa farin ciki, Sabah ya janyota ya rungumeta tsam a jikinsa yana ajiyar numfashi. Wani irin sanyi ya dinga ji yana ratsa duk ilahirin jikinsa.

Tafin da aka somayi ne yasa Samha tayi saurin kwace jikinta daga nashi tana kokarin mikewa.

Su Zack ne suka karaso suna tafi suna shewa, ita kam Samha kamar kasa ta bude ta shige ciki tsabar kunyar da takeji.

Sabah daure fuska yayi yace "yan sa ido me kuma ya kawo ku nan?"

"A'a mayar da wukan, munzo wucewa ne kawai muka ce bari mu tsaya muga draman dake wakana".

Shinoh ne ya soma kwaiwaiyon muryan Sabah inda yake fadin cewa "ke kadai nakeso kuma ke kadai nakeso na karasa sauran rayuwata da".

Su zack ne suka tuntsure da dariya suna fadin "ashe daman SB haka ka iya soyayya bamu sani ba".

Dariya suka cigaba da masa, a guje ya karaso zaiyi ta kansu, suma suka kwasa a guje suka bar wajen sunai masa dariya.
Guje guje suka somayi kamar wasu kana nan yara.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now