Chapter Fourty - four

450 64 3
                                    

A kwana a tashi, babu wuya wurin Allah, don lokaci har yayi aka sa ranar daurin auren mahaifin Sabah da Anty fanneh.

Ranar daurin auren, mutane kalilan ne suka halarci wurin, sai Yar karamar walima da akayi.

Yan'uwan Anty Fanneh da suke Maiduguri da kuma Bariga duk sun zo.

Dukda dai wanan ba shine aurenta na fari ba, hakan bai hana yan'uwanta yi mata kaya na musamman da kuma abubuwa na gyaran jiki irin na tasu yan' shuwan Maiduguri ba. Anty Fanneh tayi kyau sosai, farar fatar jikinta har fittar da wani irin shekki takeyi da kamshi na musamman.

Akwai wata kanwar Anty Fanneh katibe, da suke uwa daya, uba daya. Kana ganinta da Anty Fanneh kamar an tsaga kara don kamanin nasu ya bace. Sai dai katibe tafi Anty Fanneh dan jiki.

Rabon katibe da Nigeria shekara takwas kenan don ita tunda tayi aure ta koma Dubai da zama saboda aikin mijinta da business dinsa duk yana can. Auren Anty Fanneh ne kawai yazo da ita, tace bari tayi surprising dinta. Ai kuwa ba karamin murna da jin dadi Anty Fanneh taji ba data ga yar'uwarta tazo.
Suna rungume da juna suka fashe da kuka don tuno da mahaifansu da sukayi, daman su uku ne kawai suka rage a duniya, daga su sai babban yayansu Alhaji Abubakar Abiso amma shi yana zama tare da iyalensa a Maiduguri. Ba karamin murna sukayi ba son sake ganin junansu da sukayi.

Autan katibe namiji mai suna Azirak ne kawai tazo da, sauran yaran guda biyu namiji dana mace wato Abubakar wanda suke kiransa da Amire sai kuma Habboba wace take binsa, duk sun girma sunyi wayo don Amire shekaransa bakwai ita kuma Habbo shekaranta biyar, sai kuma Azirak mai shekara biyu.

Ai tunda Samha ta daura idanunta kan Azirak taji gabadaya son yaron ya shiga ranta. Gashi kyayawa sosai kuma fari don kamaninsa daya da uwarsa, very cute baby dashi. shima dayake bayida kiyuwa, yanada son mutane yasa nan da nan suka saba da Samha, duk inda zata tare suke zuwa. Yawanci tambayarta akeyi ko kaninta ne saboda dan kamanin dake tsakaninsu abunka da jini.

Washe garin daurin aure, Anty Fanneh ta tare a gidan mijinta.

A Sabon gidan Alhaji daya siya a Liverpool ta tare, tsayawa describing gidan ga mai karatu tamkar bata lokaci ne, don duk Apapa GRA babu gidan daya kaita.

Drivers guda uku aka zube, ya kara hiring bodyguards na musamman da zasu dinga kula da komai na shiga da fitan gidan.

Yar aikinsu guda daya ce wace daman ta jima tana aiki tare dasu ta biyo su don Anty Fanneh tace bata son yan'aiki dayawa.

Anty Lami ma, tsohuwar yar'aikinta nada ta salameta, tayi mata abun arziki sosai don matan tayi mata kokari sosai kuma sun jima tare.

A daren ranar da kyar Samha ta runtsa don ba karamin kuka taci ba don tunawa da mahaifinta datayi.

Anty Fanneh ce ta dinga rarashinta itama tana kuka har suka hakura suka share hawayen junansu.

Bayan kwana biyu da auren, katibe ta shirya zata Maiduguri don tasa anyi mata booking flight na rana, tana son taje ta gaida sauran Yan'uwa don ta jima rabonta data gansu.

Samha tace mata ta bar mata Azirak har taje ta dawo, Anty Fanneh tace a'a gwanda a tafi dashi, yan'uwa su ganshi.

Samha har da dan kukanta don anki barin mata Azirak.
Katibe tayi dariya tace ai bazasu jima ba sati daya kawai zasuyi su dawo.

Da kyar dai Samha ta hakura haka suka tafi da alkawarin dawowa next week.

*****************************

Yau sati daya da kwana uku kenan da tarewan su Samha gidansu Sabah.

Tunda suka zo gidan Samha bata cika ganin Shi ba, don sai suyi kwana biyu bata sanya shi a ido ba, sai dai da safe in ya fito zaiyi breakfast. Shima wanan nan da nan yake kamalawa ya wuce makaranta abunsa. A school ma, most of the time yana tare dasu Shinoh.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now