Chapter thirty - six

455 48 1
                                    

Bangaren su Samha kuwa, tsaye take da Jabbar a cikin restroom hanunsa rike da camera din yana cigaba da mata video.

Wani irin dariya ya sake yana fadin "Samha, Samha kenan, wato ina ajiye miki sakon kin zata shine, kika zo jikinki na bari? Ya tambayeta yana wani irin dariya.

Samha ta hada rai sai faman zabga mishi harara takeyi "Haba ki dan saki fuskarki mana, kinsan kinfi kyau idan kina fara'a". Ya karasa maganar yana cigaba da mata dariya.

Samha ta dago paper dake hanunta ta soma tambayarshi "Daman kaine ka rubuta wanan sakon ka ajiye mun?"

"Correct!" Ya bata ansa yana cigaba da murmushi.

"Ai inata tunanin yanda zanyi na janyo hankalinki zuwa gareni. Shine nace bari nayi amfani da sunan Sabah. Sai gashi nan kinyi tsuntsu kinzo". Ya fada yana dariya.

"Dakata mallam! Wanan wani irin shashanci da rainin hankali ne? Eh!"
Samha ta fada mishi a tsawace. Nan kuma hankalinta ya dawo kan camera dake hanunsa yana mata video.

Cikin sauri ta kawar da fuskanta gefe tana fadin "me kuma kake kokarin yi? Lafiyan ka kuwa Jabbar? video din me kake mun?"

"Haba sweetheart, meye a ciki kuma dan na dauki video din wace nake so? Ai banga wani aibu a ciki ba". Ya fada yana cigaba da mata video din.

Zuciya ne ya dibi Samha, cikin sauri ta karaso inda yake tsaye tazo ta bige camera din daga hanunsa, ya fadi a kasa tana fadin "So nawa zan gaya maka cewa bana sonka jabbar! Ka fita daga harkata! Don ko meye zakayi bazan taba sonka ba!" Ta fada mishi a tsawace.

Nan da nan murmushin dake fuskar jabbar ta bace, ya kurawa cameransa daya fadi a kasa ido. Tsugunawa yayi yana tattaro camera din ya soma fadin "Saboda ke fa naje na siyo wanan tsaddadiyar camera din, shine zaki yar mun da ita a kasa?".

Samha bata saurareshi ba ta cigaba da fadin "wallahi wallahi kaji nayi maka rantsuwar musulmi ko Jabbar, ka fita daga ido na na rufe, in ba haka ba sai na sa an sasaba maka a cikin makarantar nan". Tana gama fadin haka ta juya zata tafi, har ta danyi nisa ta tsaya cak, don jin muryarta datayi cikin recording tana kuka tana fadin cewa tan son Sabah.

Gabanta ne ya tsinke ya fadi data soma jin muryan Sabah shima yana magana, waigowa tayi cikin sauri taga ya daura Camera din kan table yana playing video, gata a manne a gefen Sabah tana sheshekan kuka.

Tafi Jabbar ya soma yi da hanayensa yana fadin "wow, Samha ban san kin iya acting haka ba, jibi yanda kike zubda hawaye, yanzu duk wanda ya gani yasan da gaske kikeyi. Na daga miki hannu,kuma naji dadi danayi capturing din wanan moments din tsakaninki da Sabah".

Samha a fusace ta katse shi tana fadin " wai me kakeso ne Jabbar? Why are you doing all this?"

"So nake ki kyale Sabah ki dawo gareni". Ya fada yana matsowa kusa da ita.

"Tausayinki nakeji Samha, bana so kiyi soyayya da yayanki don babu abunda hakan zai janyo sai baccin rai da raba zumunci. Ki yarda dani Samha, ni mai son farin cikin ki ne. Wanan sirrin naki zan boye miki shi babu wanda zai sani, don haka ki kyale Sabah ki dawo gareni". Ya karasa maganar yana kokarin talabo fuskarta.

Wani irin wawan mari Samha ta kai mishi a fuska tana fadin "Bakada hankali, an gaya maka ko giya nasha zan tsaya na saurareka ne ballantana na amince nayi soyayya da kai? An gaya maka haka ake soyyaya, kazo ka adabi rayuwata sai faman threatening dina kakeyi. Kana tunanin zan taba son mutum irinka ne?!" Ta fada mishi a tsawace.

Jabbar yasa hannu ya shafo inda ta mareshi yace "ni kika mara Samha?" Murmushi ya sake sa'anan ya cigaba da fadin " wai ke yanzu gani na kikeyi a matsayin makiyinki ne koh meye? toh bari kiji in gaya miki, tunda kinki ki saurareni, ki jira ki gani duk abunda ya same Sabah nan gaba ke kika jawo."

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now