Chapter four

718 67 0
                                    

Samha tana barin su Sabah kai tsaye tayi hanyar  departmental garden dinsu ta samu wuri ta zauna tayi tagumi tana tunanin mafita daga lamarin sabah.

Wayar ta ce ta fara ringing ta katse mata tunani, ta ciro daga cikin Jakarta. Sunan khady ta gani a rubuce a screen din wayar, dagawa tayi ta kara a kunnenta.

Khady ce ta fara tambayarta inda take don har sun gama lectures suna so su wuce gida. Kai tsaye tace su tafi kawai ita ba yanzu zata tafi gida ba akwai abun da zata tsaya yi su hadu gobe. Tace toh shikenan sai Allah ya kaimu. Sukayi sallama ta katse wayar.

Ajiye wayar tayi kusa da ita tana dafe kanta don har ciwon kai ta fara ji a lokacin. Bata son su hadu dasu khady su fuskanci damuwarta shiyasa tace musu su wuce kawai.

Amjad ya fito daga library kenan zai wuce sai ya hangota zaune ita kadai ta dafe kai alamun tana cikin damuwa. Karasawa yayi inda take zaune ya tsaya.

Ita samha jin tsayuwar mutum a kanta ne yasa ta dago da Sauri a zatonta Sabah ne yazo zai mata rashin mutunci sai taga akasin haka. Amjad ta gani tsaye a gabanta kamar a mafarki.

Nan take bugun zuciyar ta ta karu, mamaki ya cika ta. Don bata taba zaton zata ga Amjad tsaye a gabanta haka ba.

Murmushi ya sakar mata Wanda ya kara bayana kyawunsa ya mata sallama ta ansa mishi. Hanunshi duka biyu ya tura cikin aljihu. Yayi shiru yana kallonta sa'anan yace.

" sorry hope ban takura miki ba nazo wucewa ne naga kamar kina cikin damuwa shine nace let me check on you, hope dai komai lafiya?". Ya tambayeta.

Murmushi ta sakar masa sa'anan tace mishi " yes I'm fine wlh, I'm just trying to concentrate ne, nazo waje shan iska ne".

Sai yace "okay, sunana amjad, last time da muka hadu a kan stairs ina Sauri naje office din Dr kabir ne shiyasa ban tsaya munyi magana sosai ba, nasan sunanki samha koh? If I'm right. Ina yawan ganin ki a class amma magana bata taba hada mu ba".

" haka ne sunana samha. Kuma you are right magana bata taba hada mu ba kam. Nice to meet you amjad ta fada mishi" fuskar ta still dauke da murmushi.

" it's a pleasure. ni na gama lectures dina zan wuce yanzu. I'll see you some other time ko". ya fada mata
Tace toh shikenan. sallama sukayi ya bar wurin.

Samha ji tayi kamar ta tashi tayi tsalle tsabar farin ciki. Nan da nan ta nema bakin cikin da take ciki ta rasa. Daukar Jakarta tayi ta bar wurin sai fara'a take kamar wace aka mallaka mata gida a aljannah.

Bata sani ba ashe duk abun da ke wakana tsakinta da Amjad Sabah yana tsaye ya na kallon su.
Wani irin tukukin bakin ciki ne ya rufe shi daya gansu tare. Nan take haushin dayake ji alokacin ta karu dari bisa dari.
Nan kuma ya fara tambayar kansa toh haushin su na me yakeji? Kodai kishi yake ji? Nan take kuma ya kawar da wanan tunanin don yasan so ne ke kawo kishi,shi kuma yasan ba son samha yake yi ba. Kawai dai ya mayar da ita abar wasansa ne don samun nishadi. Tsaki yaja ya bar wurin.

Samha tana isa gida a ranan ta wuce daki tayi wanka tayi sallolinta sa'anan ta kwanta a gado tana ta faman tunanin amjad har bacci ya dauke ta. Ita kanta ammi ta lura da changes a tare da diyartata yau dinan yanda ta ga tana cikin farin ciki tun suna hanya har suka iso gida.
Bayan samha ta haura sama, shiru shiru Anty fanneh tana jiran taga saukowarta, bata ganta ba. Sai ta haura sama ta nufi dakinta. Tana bude kofa taga tayi rasherashe akan gado sai faman bacci takeyi. Girgiza kai ammi tayi ta fita daga dakin tana fadin baby kenan.

An kusan kiran sallar magrib samha ta farka ta tashi ta shiga bayi ta wanke bakinta sa'anan ta dauro alwala. Ana kiran sallah tayi sallanta. Tana zaune kan sallaya taji wayarta ta fara ringing akan gado .Mikewa tayi ta dauko wayar taga ammi ke kiranta, ta daga. " Toh sarkin bacci sai ayi kokari a tashi ayi sallah.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now