Chapter sixteen

610 77 0
                                    

Ajiyar zuciya samha tayi ta yaye bargon daya lulubesu dashi sa'anan ta gyara masa kwanciya kan kujeran. Fresh bandage ta dauko ta daure masa ciwon hanunsa dashi.

Tana gamawa ta mike, har ta juya da niyan barin wurin taji abu kamar ya rike mata kafa. Juyowa tayi taga hanun sabah rike da jelar rigarta, dagowa tayi tana dubansa taga still baccinsa yakeyi hankalinsa kwance.

Tayi tayi ta kwace rigarta daga rikkon daya mata ama hakan ya gagara haka ta dawo ta zauna kusa dashi ta kura mishi ido tana kallonsa yana bacci. Baccinsa yakeyi kamar bashida wata damuwa hankalinsa a kwance bazaka ce shine masifafen nan na mai yawan rigima da mutane ba, cigaba tayi da kallon kyakyawar fuskarsa, eyelashes dinsa zara zara dasu ko ita da take mace batada eyelashes masu kyau irin wanan.

Ajiyar zuciya tayi ta kawar da dubanta daga gareshi ta dauko remote ta soma canza tashan tv. Wani programme ake nunawa a telemundo, ta fara bi. Tana cikin kallo itama bata san sanda bacci yayi awon gaba da ita ba tana zaune kan kujerar.

Washe gari da safe cikin bacci ta taji ana fadin "keh sarkin bacci, bazaki tashi bane? Gari fah ya waye".

Cikin baccin ta turo dan karamin bakinta cike da shagwaba tana fadin " Ni gaskiya a kyaleni, bacci nakeji" ta fada tana gyara kwanciyarta.

Ko meye ta tuna, sai kuma ta bude idanunta cikin sauri ta juyo tana kallon wanda yazo yana tashinta. Sabah ta gani a tsaye fuskarsa dauke da murmushi yana kallonta.

Zaro ido tayi ta mike tana salati " nashiga uku, anan muka kwana?" Samha ta tambayeshi tana zaro ido.
Gyada mata kai yana murmushi don gaba daya yanayinta dariya yake bashi musamman yanda duk tabi ta rikice.

"Abba fa? Ina yake karde yazo ya ganmu muna bacci tare a fallo?" Ta tambayeshi hankalinta a tashe.

Murmushi sabah ya cigaba dayi sa'anan ya durkusa daidai saitin kunnenta ya soma fadin "daman haka kike surutu cikin bacci?"

Ido ta zaro tana dubansa " wake surutu cikin bacci".

"Toh in fada miki maganganun da kika dinga yi ne cikin bacci?"

Kallon shi kawai ta cigaba dayi hankalinta a tashe tana zaro ido. " sunana kika dinga ambatowa kina kirarin kina sona" ya fada yana daga mata gira daya fuskarsa dauke da murmushi.

Wata yar kara samha ta sake tana toshe kunnenta da jin kalamansa, hankalinta a tashe ta mike daga kan kujeran ta kwasa a guje tayi sama zuwa dakinta. Bayi ta fada ta fara watsa ruwa a fuskarta. Cike da tashin hankali ta dubi kanta cikin madubin dake cikin bayin tana girgiza kanta kamar zatayi kuka " na shiga uku ya akayi nayi wanan sakacin nabari sabah yaga yanda nake bacci? yanzu nasan ya ji duk surutan dana dingayi cikin baccina. Wayo Allah ya akayi na bari yasamu wanan daman?" Ta tambayi kanta cike da tashin hankali.

Nan kuma kallon daya dinga mata jiya dadare a lokacin da take goge masa ciwo ya dinga dawo mata cikin kwakwalwa. Gabadaya tunaninta ya soma hargitsewa. Meyasa kwana biyun nan idan sabah yana kusa dani sai na dinga jin zuciyata na harbawa, gabadaya sai na nema nutsuwata na rasa" haka ta dinga tambayar kanta amma ta gagara samun ansa.

Ruwa ta watsa a jikinta ta fito ta soma shirin zuwa school. Abba yace idan tasan har yanzu jikinta baiyi kwari ba tayi zamanta a gida, samha taqi kememe tace lafiyarta lau. Sabah tabe baki yayi yana jinsu bai ce musu kalla ba. suna fita harabar gidan wata hadadiyar mota qirar benz ce ke jiransu da driver. Ga wata camry ma dauke da bodyguards guda uku suna tsaye kusa da motan suna jiran fitowarsu. Suna isa wajen motar, daya daga cikin bodyguard din yazo ya budewa Abba seat din baya shi da samha suka shiga ciki. Sabah shi kuma ya zauna a gaba, driver yaja su suka bar gidan. Ko da suka isa makaranta aka juyo ana kallon motoccin dan ba karamin daukan ido suke ba, musamman benz din. Bodyguards dinne suka zo suka bude wa abba kofa ya fito daga cikin motar. Sabah shima ya bude kofar ya fito. Samha na nan zaune cikin motar taki fitowa. Sabah ne ya dube ta yana fadin " wai ke me kike jira? bazaki fito bane? Ya fada yana galla mata harara.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now