Chapter fifty-nine

390 53 0
                                    

Sabah yayi shiru bai sake cewa komai ba, har Abba ya gama maganar da zaiyi ya dasa aya.

Haka suka karasa dinner dinan, parlourn tsit, babu wanda ya sake cewa komai. kowa da abunda yake masa yawo a ka.

Bayan sun gama cin abinci, Sabah ya mike zai haura sama, Anty fanneh ta dakatar dashi tace ya tsaya tana son magana dashi.

Sabah ya dawo ya zauna, bayan su Abba sun haura sama, Anty fanneh ta juyo tana dubansa tace "Sabah, inaso ka saurareni da kyau. Wanana maganar da mahaifinka ya gama yi inaso ka dauki maganar da muhimanci. Gobe ka shirya kaje gidansu yarinyar nan ku gaisa ku soma sabawa da juna. Bana son naji wani musu".

Jiki a sanyaye Sabah yace "toh Ammi". Badan yaso ba don dai kawai yana jin nauyin Anty fanneh bazai iya mata musu ba.

Mikewa yayi ya mata sai da safe sa'anan ya haura sama zuwa dakinsa zuciyarsa na masa tafarfasa.

Ita kam samha tunda ta haura sama zuwa dakinta ta nema nutsuwarta ta rasa. Sai faman zarya takeyi a dakin tana kaiwa da kawowa. Yanzu Daddy da gaske yake zai daurawa Sabah aure da Madinah? Ya zatayi kenan? Ina suke tunanin zata jefa kanta, don tasan bazata taba iya rabuwa da Sabah ba. Wani irin dishi dishi ta soma gani, ta nema wuri a gefen gado ta zauna.

Wayarta ta janyo ta soma nemansa a layi taji a kashe don haka ta mike ta dauko hijab dinta ta zira sa'anan ta fito daga dakin ta nufa bangarensa.

Tana isa kofar dakinsa ta tsaya ta soma bugawa a hankali, sai datayi knocking kusan sau goma bazo an bude ba sai ta soma tunanin ko yayi bacci ne? Wata zuciyar tace mata inaa, Sabah ai baya bacci da wuri, wani sa'in ma yana fitowa yaje fridge din kasa ya nema dan abun motsa baki Don haka wuri ta nema a kusa da step ta zauna ta zabga uban tagumi.

Sabah a tunaninsa duk mai buga masa kofa ya rigada ya tafi yasa yazo ya bude kofar a fusace.

Juyawan da zaiyi ya ganta a zaune ta zabga uban tagumi.

Kallonta yayi na yan sekoni sa'anan yace "ke zaman me kikeyi anan? Dare bai miki bane?".

Samha ta dago tana dubansa ta da'an turo baki tace "jiranka nakeyi ka fito".

Ajiyar zuciya Sabah ya sake sa'anan yazo ya nema wuri kusa da ita ya zauna.

Daddaden kamshin turarensa ne taji duk ya bibiyeta, ta lumshe idanunta a hankali don ji tayi tamkar ta daura kanta bisa kafardarsa su dore a hakan.

A hankali ta bude baki ta soma fadin "Sabah bana son ganinka cikin damuwa. A duk sanda na ganka haka hankalina baya kwanciya".

Sabah ya dubeta yace "ce miki nayi ina cikin damuwa?".

"Basai ka fada mun ba. Zuciyata da naka tamkar daya suke yanzu, idan kana cikin farin ciki ina sani haka zalika idan kana cikin bakin ciki duk ina ji a jikina".

Murmushi Sabah ya da'an sakar mata sa'anan yace "toh shi Sameer fa? Baki sanin farin cikinsa ko walwalansa?"

Samha ta girgiza masa kanta tace "koh daya kai kadai ne a zuciyar Samha. Kai kadai zuciyar Samha take so".

Sabah ya da'an wasa mata hararan wasa yace "toh ni kuma i saw something different a diary dinki. Inda kike kwararo masa zuciyarki akan yanda kike sonsa. Wai tun yaushe kika soma rubutu a diary dinan? Tun kina jss1?"

Zaro ido Samha tayi tace "Sabah ina kaga diary dina ka karanta?"

"Oho tsinta nayi".

Mikewa tayi tsaye hankalinta a matukar tashe kamar zatayi masa kuka don tasan irin kwabe da yarantar data dinga zubawa a cikin diary dinan.

Sabah ya mike tsaye shima, Samha ta kamo jelar rigarsa tana fadin "ka bani diary dina Sabah, akan me zaka dauko mun diary ka karanta. Ka bani kayana ko na sa maka ihu yanzu kowa ya fito".

"Baza bada ba, kiyi ihun mana".

Dayaga tana niyan ta shige dakinsa taje ta dauko, yasa yayi sauri kwacewa daga rikon datayi masa ya shige cikin dakin a guje tana binsa a baya.

Kafun ta isa ya rigada ya garke ya sawa kofar key.

Samha ta soma bubuga kofan tana masa magiyan daya bude ya bata diary dinta.

Bude kofan Sabah yayi ya watsa mata gwallo yana fadin "sai na gama karantawa tass tukuna zanyi deciding kona yaga ko kuma na konata" yana gama fadin haka ya sake garke kofar.

Bugun duniyan nan tayi yaqi budewa haka ta hakura ta koma dakinta zuciyarta na tafarfasa.

Shikam Sabah yana komawa cikin daki, ya dauko diary din ya soma karantawa, ai kuwa zuciyarsa ce ta kusan bugawa don abunda ke rubuce ciki ba karamin tayar masa da hankali yayi ba.

A hankali yake bin pages daya bayan daya yana karantawa, duk page din daya karanta yaga tana faman zazzaga soyayarta akan sameer sai yabi ya yaga. Dayaga ma abun ya isheshi yasa ya yaga diary din gabadaya ya watsar, ya kwanta akan gado yana hucci.

Wayarsa ce ya dauko ya kunna ta, ya shiga snapchat.

Sakkonin Samha ne ya soma cin karo da. Cikin sauri ya shiga snap dinsu ya bude. Wasu hotuna yaga ta turo masa.

Ai kuwa yana downloading bai san sanda dariya ta kubuce masa ba, yanda yaga ta hada rai ta cunkushe da'an karamin hancinta tana turo masa full bottom lip dinta alamun wai ita tana fushi dashi kenan.

Sauran hotuna kuma wasu funny faces takeyi da bai gane kansu ba. Dariya kawai yayi yana girgiza kansa. Komai na Samha burgesa yakeyi, gashi bata fushi. Kotayi kokarin yin fushin ma bata iyayi da kyau. Komai nata, her childish behavior, cute face dinta, everything about her kara dilmiyar dashi yake cikin kogin sonta.

Chatting suka farayi ya soma zolayenta tana masa shagwaba da magiya akan kar ya karanta mata diary shi kuwa yace ya rigada ya gama karantawa. Haka suka cigaba da rigima a chat, har bacci ya samu nasaran daukan su.

********************

Washe gari ta kasance ranar friday, don haka yau shigan manyar kaya yayi. Wata hadadiyar kaftan ya saka Ash colour, kayan sun masa kyau sosai sukayi contrasting da farar fatar jikinsa. Bai saka hula ba don shi ba gwanan son saka hula bane idan ya saka kaftan.

Curly black hair dinsa ta kwanta luuu bisa kansa sai faman fidda shekki takeyi.

Yana saukowa kasa yaci karo da Anty fanneh, bayan sun gaisa ta sake jaddada masa akan ya tabbatar yaje gidansu Madinah yau dinan.
Sabah yace insha Allah zaije.

Bayan sun gama lectures a school, misalin karfe hudu na yamma. Sabah ya fito daga department dinsu kenan yana tafiya shi kadai ya hango Madina tana tafe ita kadai.

Sanye take cikin doguwar abaya baka, tayi wrap round da mayafin. Yau kam sanye take da glasses manne bisa kyakyawar fuskarta.

Madina tana ganinshi ta barke da murmushi, ta soma karasowa inda yake zuciyarta cike da matsanancin farin cikin ganinsa.

Tsayawa tayi a gabansa tana aika masa da tsadadden murmushinta.

Sabah yayi shiru yana kallonta na ya'an sekoni bai ce komai ba.

Tsura mata ido yayi yana kallonta, abubuwa da dama na masa yawo a ka. Shikam yasan Madinah batada wata makusa ko muni a tare da ita da zai kita. Sai dai shi sam kwata kwata baya jin sonta a zuciyarsa. Don matukar Samha tana raye a doron kasa, bazai iya rabar wata mace da sunan soyayya ba ballanta aure. Sunfi tsawon minti goma a hakan suna kallon juna.

Madinah tace "Sabah ka bani number wayarka. Banida ita".

Da zaiqi, sai kuma ya tuna da kashedin da Anty fanneh tayi masa don haka yace "ina zaki?"

"Gida zani, yanzu muka gama lectures". Ta bashi ansa kai tsaye.

Sabah yace "toh muje na kaiki gidan". bai jira yaji ansarta ba ya juya ya soma tafiya.

Jin maganar tayi kamar daga sama don bata taba kawowa a rai cewa zai saurareta ba ballanta yace zai kaita gida. Don haka cikin zumudi tabi bayansa har suka karasa inda yayi parking motarsa.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now