Chapter seventen

566 69 0
                                    

Amjad yana zuwa dab da inda sabah ke tsaye ya wuce shi bai ce masa kala ba, su Khadie dake tsaye a bakin kofa suka bishi da kallo har ya fice daga library din.

Samha na tsaye duk tabi ta firgita hawaye ne keta faman gangarowa bisa kuncinta.
Sabah ya karaso inda take tsaye yazo ya tsaya a gabanta yana kallonta daga bisani ya soma fadin " ga abinci nan a takeaway abba ya aiko dashi na ajiye miki a cikin locker na ajinku".

Kamar ba magana yakeyi ba don samha ko dagowa batayi ta kalle shi ba.

"Magana fa nake miki, ko baki ji ne?". Shiru ta masa bata ce mishi komai ba, dataga kukan yana neman yaci karfinta ta kwasa a guje ta fice daga library din.

Gudu take ta faman yi bata tsaya ko ina ba sai departmental garden dinsu, taje ta tsaya a gindin wata bishiya sai faman haki takeyi saboda gudun data sha.
Su khadija suka biyo bayanta. Khadija ce a gaba amina na binta a baya sukazo suka tsaya dab da ita. Khadija ta dubi samha ta soma fadin " kiyi hakuri samha munzo mun katse miki maganar da kukeyi keda amjad, wlh sabah ne yazo ya takura mana yace sai lallai mun fada mishi inda kike. Amma karki damu keda amjad zaku sake samun wani lokaci kuyi magana kinji".

Samha ta katse ta tana fadin " ni bama wanan bane Ke damuna, nama ji dadin zuwanku a wanan lokacin, don amjad na kasa gane kanshi, ya canza mun gabadaya kamar bashi ba. A lokacin kuma sai naji duk son da nake mishi a baya na nemeshi na rasa. Gabadaya naji ya sane mun a rai, banjin zan iya kasancewa tare dashi kuma, danaga sabah ya zo sai naji wani irin sanyi a raina" ta karasa maganar tana dubansu.

Amina da khadija binta da kallo kawai sukeyi, khadija wacce ranta a bace yake ta bude baki ta soma fadin "amma samha kina bani mamaki, kema kin san abunda kika fadawa amjad baki kyauta ba, ai ba haka ake soyayya ba. Idan kana tare da mutum dole kayi kishinsa, kin san yanda amjad ya dinga ji kuwa game dake da sabah? Yanzu samha kinyi daidai kenan? Abunda zaki sakawa amjad dashi kenan? Duk so da kaunar daya dinga nuna miki? Meyasa zaki mishi haka samha, ni yanzu ma gabadaya ina nadamar taimaka miki dana dingayi tun farko akan amjad din, dana san haka zakiyi masa daban sa baki ba tun farko!"
Tana gama fadin haka ta juya cikin sauri ta soma barin wajen. Amina ce ta juyo ta dinga kwada mata kira amma khadie ko juyowa batayi ba ta tafi ta barsu a wajen. Samha tana tsaye tayi shiru abubuwa duk sun mata yawa ta rasa inda zata sa kanta.

Washe gari da safe a gym amjad ne tsaye yayi zurfi cikin tunani don tun daya shigo yan team players dinsa suka rasa gane kansa don sai tsawa yake dakawa duk wanda yazo ya tunkareshi. Gabdayansu sai baya baya sukeyi dashi don basu san meke damunsa ba.

Sabah ne ya shigo cikin gym din ya hango amjad a tsaye shi kadai yayi shuru yayi zurfi cikin tunani. cike da karfin hali irin nasa ya karaso ya tsaya inda amjad yake ya soma fadin "amjad kenan, idan kanada abunda zaka fada mun gani nan na kawo kaina sai ka fada mun bawai ka tsaya kana wani ci cin magani ba idan kaga mutane".

Amjad yayi shuru bai tanka masa ba amma Zuciyarsa sai faman tafarfasa yakeyi.

"Magana nake maka kayi shuru kana jina. Tunda samha bata nan sai ka daina wanan pretending din da kakeyi don ni na rigada nagama karantarka."

"Me kace?" Amjad ya juyo yana dubansa.
"Cewa nayi gwanda ka ajiye wanan pret..."
Amjad bai bari ya karasa maganar ba ya kai mishi naushi a baki. Sabah yayi tangar tangar kamar zai fadi kasa amma sai ya rike kansa.
Sauran yan kwallon da suke sama suna ganin abunda ke faruwa suka sauko a guje don su rabasu.

Sabah ya mike tsaye yana murmushi gefen lips dinsa ya fashe jini ya soma gangarowa.

A tswace amjad ya soma fadin " kana ganin zan naushe ka amma ka tsaya baka kauce ba ka tsaya kana mun dariya, meye matsalarka?!"

Sabah murmushi kawai ya cigaba dayi yace "bakomai banga daman kaucewa bane, kawai inason ganinka cikin irin wanan yanayin ne. Kafi kyau a hakan"

"Kana tunanin banida hankali ne ko meye, duk abunda kakeyi ina lura dakai, duk inda mukaje da samha kana nan biye damu ka hana mu sukuni, dabadin kai ba da har yanzu ina tare da ita".

"Au wanan itace damuwarka? Ai nasha fada maka cewa samha tawace ko ban fada maka ba?"

Amjad a fusace ya taho ya sake kai mishi wani naushin a ciki ya tureshi ya fadi a kasa. Sabah kamar bashi amjad ya gama kaiwa naushi ba ya dago yana dubansa still fuskarsa na dauke da murmushi

"Haba amjad, ai da nazata ka fi haka karfi, ya ka tsaya?" Ya tambayeshi. Amjad zuciya ta sake debansa ya nufo shi gadan gadan zai sake kai mishi wani naushin sai ga sauran yan team din sun karaso suka ririkeshi, sabah ya tashi yana dariya yana girgiza kai yazo ya tsaya dab dashi yana fadin " Nasan ka jima kana son ka aikata hakan, da fatan ka samu nutsuwa a zuciyarka yanzu. Nidai bazan taba baka hakuri ba don nasan ban aikata laifin komai ba gareka". yana gama fadin haka ya dafe kafadar amjad kamar wani karamin yaro ya tafi ya barshi a wajen.

Da yamma misalin karfe biyar samha na zaune kan daya daga cikin kujerun shakatawa na garden din gidansu sabah. Ta daura kanta bisa cinyarta sai faman kuka takeyi. Kamar daga sama taji takun mutun yazo ya tsaya a gabanta. Ko bata dago ba tasan wanda yazo ya tsaya don kamshin turarensa daban yake, a duk inda taji wanan daddaden kamshin tasan nashi ne. A hankali ta dago kanta tana dubansa, fuskarta duk ta bace da hawaye. Kyawawan idanunsa ya zube cikin nata yana kallonta. Sanye yake cikin farar tshirt da bakin wando, sumar kansa ta kwanta luu luu akansa daga gani bai jima da fitowa daga wanka ba. Kallon junasu suka dingayi na kusan minti biyar daga bisani ya bude baki ya soma fadin "wai ke wace irin mutum ce? kin wani zo kin zauna anan ke kadai kina kuka?"

Samha shuru tayi tana kallonsa bata bashi ansa ba.
"Kukan meye kikeyi?" Ya sake jefo mata tambaya.

"Ba kuka nakeyi ba".

"Karki maidani makaho mana, ba kuka na taddaki kinayi ba?"
"Na fada maka ba kuka nakeyi ba" ta fada tana turo masa dan karamin bakinta.

"Kuka kikeyi".
"Ba kuka nakeyi ba" ta sake bashi ansa.

Shuru yayi yana dubanta daga bisani ya cigaba da fadin. " kukan nan da kikeyi, ya danganceni ne?

A'a, wanan kuma ba matsalarka bace, matsalata ce." Ta fada tana sunkuyar da kanta. Shuru tayi daga bisani ta cigaba da fadin  " sabah ban san yanda akayi na zama haka ba, garin na kare kaina gashi na batawa wasu  na jefa su cikin wani hali. Harta kawayena ma yanzu sun juya mun baya. Na kasance mara kirki ko sabah? Ta fada tana dubanshi. Shiru kawai yayi yana dubanta.

"Meyasa zakiyi wanan tunanin? Kawayenki suna sonki mana".

Gigiza masa kanta tayi tace "a da kenan, amma yanzu sun daina".

"Idan suna zaune tare da ke tsakani da Allah suma zasu gano cewa ba haka kike ba, life is full of ups and downs, kuma kin san dan adam tara yake bai cika goma ba. So ki kwantar da hankalinki. Zasu sauko".

Samha da danji sanyi a ranta game da kalamansa, sai taji damuwar nata ya dan ragu.

"Sabah kazo nan don ka kwantar mun da hanakali ne ko?" Ta fada tana dubansa.

Nan da nan kuma taga ya bata fuska ya mike yana fadin "haba sai kace banida aikin yi? Daman abba ne yace nazo na kiraki kishigo ciki ki samu kici abinci kisha magani"

Samha Murmushi kawai takeyi tana dubansa bata ce komai ba.
" murmushin me kuma kikeyi sai kace kinyi tsintuwa? Mallama ki tashi mu tafi karki bata mun lokaci. Nima nan yunwa nakeji. Abba na jiranmu". Yana gama fadin haka ya soma kokarin barin wajen.

samha girgiza kai kawai tayi ta mike tabi bayanshi tana murmushi suka shige ciki.
Suna shiga ciki suka tadda abba na zaune kan dining an jera abincin da zasu ci yana jiran su shigo. Suna shigowa suka zauna tare suka fara cin abinci. Suna gama ci Abba ya musu sallama ya haura sama zuwa dakinsa. Shima sabah yabi bayansa ya wuce dakinsa. Samha kadai aka bari a fallon tana zaune tana kallon wani programme da ake nunawa a tv. Tayi kallon na kusan minti 30 sa'anan taji idanunta sun soma mata nauyi alamun bacci. Ta kashe tv ta mike ta haura sama. Tazo dab da inda zata shiga dakinta sai ga sabah nan ya fito daga dakinsa zai sauka kasa. Sanye yake cikin kayan bacci riga da wando pyjamas. Gabanta ya fadi ta kawar da kanta gefe. Takowa yayi har ya karaso inda take tsaye ya kura mata ido yana kallonta, ita kam ta kasa dagowa ta kalleshi ta kawar da kanta gefe " keh meye haka kinayi abu kamar wata mara gaskiya?" Ya jefo mata tambaya.

"Babu komai" ta bashi ansa tana kokarin bude kofar ta shiga ciki. Kafa daya yasa ya rike kofar, ya ruko hanunta ya juyo da ita tana fuskantarshi.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now