Chapter fifty-eight

421 49 1
                                    

Sabah yana ganin Anty fanneh yayi zumbur ya mike.

Itama Samha mikewa tayi kirjinta na wani irin mahaukacin bugu.

"Innalillahi wa ina illahi raji'un! Shikenan yau kashinmu ya bushe. Ammi ta gano mu" samha ta fada can kasan ranta, zufa na karyo mata ta ko ina.

Ammi ta tsaya tayi shiru tana kallonsu, Kirjinta ne yake bugawa da karfi tana kokarin ta fahimce abunda ke faruwa.

Sabah ya Kirkiro murmushin karfin hali yana da'an sosa kai yace " Ammi kin dawo?".

Anty fanneh ta dubesu cike da tuhuma tace "Sabah, samha... meke faruwa anan?"

Kame kame Samha ta somayi jikinta na bari tace "bb..komai Ammi kawai tsokanata yakeyi".

"Anty kijawa Samha kunne, rashin kunya take mun, ni kuma a matsayina na yayanta bazan bari tanai mun rashin kunya haka in kyaleta ba".

Anty Fanneh tayi shiru tana kallonsu don tama rasa mai zata ce. Tunaninta ne yake kokarin zuwa wani direction na daban amma tayi saurin kaudawa, don tasan akwai shakuwa sosai tsakaninsu kuma tasan yar'nata bazata taba aikata abunda zuciyarta take hasko mata ba. Amma still yanayin data zo ta gansu bai mata ba don haka ta dau alwashin zata zaunar dasu tayi musu fada akan irin wasan da sukeyi, bai dace ba.

A hankali ta karasa shigowa parlourn, hannunta rike da ledan cefanen datayi.

Samha ta karaso zata karba ledan daga hannunta, Ammi ta dakatar da ita.

Haka ta ja gefe ta tsaya jiki a sanyaye.

Ammi bata sake ce dasu komai ba ta wuce cikin kitchen.

Samha da Sabah suka kalli junansu cike da fargaba, barin ma Samha wace gabadaya hankalinta a tashe yake.

Suna tsaye a hakan Samha taji an kwada mata kira daga kitchen.

Jiki na bari ta karasa kitchen din, Anty fanneh tace "kizo ki tayani yanka vegetables dinan, inason na hada mana miyan nan kafin Abbanku ya dawo".

Samha tace "toh Ammi". Taje ta dauko wuka ta fito da vegetables din ta soma yankawa.

Bayan shigan Samha kitchen, Sabah ya juya ya haura sama zuwa dakinsa. Zuciyarsa fal da tunani. Babu abunda yake masa yawo a ka illa yanayin da Anty fanneh tazo ta riske su, da kuma reaction dinta. Dukda dai baya shakkan kowa kuma baiki kowa ma ya sani ba amma yana tunanin yanda iyayyen nasu zasu dauki abun don shidai a gaskiya yana  bala'in son Samha, baijin zai iya rayuwa da wata ya' mace idan ba ita ba, don kullum sonta dadda karuwa yake cikin zuciyarsa har baya iya controlling kansa idan ya ganta.

Yana cikin wanan tunanin wayarsa ta soma ringing yasa hannu ya dauko. Number daya gani a rubuce jikin screen dinne yasa shi jan tsaki ya wular da wayar gefe. Ba kowa bane illa Shafa, kwana biyun nan ta dauko wani saran kiransa ne da bai gane ba. Akalla a rana daya sai tayi mishi miss calls kusan sau hamsin ko sama da haka.

Sai da wayar tayi ringing kusan sau tara tukana ya daga ransa a bace. Zata soma yi masa magana, ya dakatar da ita yace " wai ke shafah, wace irin mayyar yarinya ce ke? Ana so dole ne? Ki rabu dani mana! Nace bana sonki. Wallahi idan na sake ganin kiranki a wayata sai nazo har gida nayi miki dukan fitan hankali. Shasha kawai mara kunya! Wai har ni zaki duba tsabar idona kice kina sona. Yaushe aka haifeki kika girma da har kika san wani abu wai shi so?"

Cikin muryan kuka Shafa ta soma fadin "wlh yaya Sabah ka yarda dani ina sonka. Banjin akwai wata macen da zata soka kamar yanda nake sonka. Wai meye aibuna da bazaka soni ba? Me na rasa?"

"Tambayata ma kikeyi? Toh idan soyayya ce nace bana yi! Kuma daga yau sai yau kinji nayi miki last warning kenan. Karki sake yunkurin kirana kice zaki fada mun wanan shirmen. Shashasha mara hankali kawai".

Yana gama fadin haka ya katse kiran, ya kashe wayar ma gabadaya.

Wani irin haushi yakeji, gabadaya shafah tazo ta sake dagula masa lissafi.

Mikewa yayi ya fada bayi ya watsa ruwa a jikinsa sa'anan ya dauro alwala ya fito ya tada sallar magrib.

Yana idarwa ya mike, yaje wardrobe dinsa ya fito da comfy wears dinsa, white tshirt da black trousers ya sanya.

Sumar kansa wace bata gama bushewa ba ya dauko towel karami ya soma gogewa. Yana gama gogewa ya dauko fav turarensa "storm for men" ya feshe duk ilahirin jikinsa dashi, sa'anan yabi lafiyan gado Ya kwanta yayi shiru yana tunani. Tunanin yanda zasu bullo wa almarin su tunkari iyayensu shida Samha yakeyi, yasan abu ne mai kamar wuya su amince musu.

Yana cikin wanan tunanin yaji an soma kwankwasa kofar. Mikewa yayi yaje ta bude kofar, Samha ce ya gani tsaya a bakin kofar, manyan idanunta masu rikitar masa da lissafi ta zubesu kyam akansa.

Shiru yayi yana kallonta bai ce komai ba.

Samha tace "Sabah ya ka kashe wayarka? Ammi ta kammala girki tace nazo na kiraka. Abba ma ya dawo".

Tana gama fadin haka ta juya zata tafi, Sabah yayi sauri ya kamo hannunta ya janyota cikin dakin.

A firgice take dubansa tace "a'a Sabah, kaga abunda ya faru dazun bana so ya sake faruwa don haka ka sakeni kawai na wuce".

Sabah bai sake mata hannu ba, yayi shiru ya tsura mata ido yana kare mata kallo na da'an wani lokaci, hannu yasa ya soma shafo kyakyawar fuskarta, Samha ta lumshe idanunta a hankali tana jin wani irin feelings na taso mata, jikinta na kara moving akan matsanancin soyayyar da Sabah yake nuna mata.

Saukar numfashin dataji bisa fuskarta ne yasa ta bude idanunta cikin sauri taga fuskarsa dab da nata yana kokarin ya hada bakinsu wuri daya tayi saurin kau da kanta gefe tana fadin "Sabah kayi hakuri, amma bazai yu mu ci gaba da hakan ba. Ina matukar jin tsoro wlh. Kaga dai reaction din Ammi yanda tazo ta riske mu dazun. Bana son hakan ta sake faruwa".

Sabah yayi shiru bai ce komai ba, ajiyar zuciya ya sake sa'anan yasa hannunsa duka biyu ya tallafo gefen fuskarta ya manna mata kiss a goshi sa'anan ya saketa yace "toh shikenan jeki, nima gani nan zuwa".

Jiki a sanyaye ta juya ta fita daga dakin. Sabah yabi bayanta da kallo yana jin wani irin shauki da sonta yana kara fuzgar zuciyarsa.

Komawa yayi ya dauko wayarsa daga kan gado sa'anan ya sauko kasa.

A dining ya tadda suna zaune suna hira. Sabah ya gaishe da Abba sa'anan ya nema wuri ya zauna a gefe.

Anty fanneh ta dauko plate ta soma serving kowa abinci. Already ta rigada ta da'an saki ranta don tun a kitchen suna girki tasa Samha a gaba tanai mata fada. Samha harda da'an hawayenta ta dinga mata magiya tace mata wasa kawai sukeyi itada Sabah amma daga yau bazata sake ba. Fada sosai Anty fanneh tayi mata tace shima Sabah din zata kirashi tayi masa fada.

Suna cikin cin abincin Anty Fanneh ta dubi Samha tace " Samha meyasa baki fada mun ba?"

Gaban Samha ne ya fadi ta dago cikin sauri tana duban Anty Fanneh.

' me kenan Ammi?" Ta tambayeta.

"Batun Sameer, daman yana gari har ma yana koyarwa a makarantar ku shine baki sanar dani ba?"

Sabah da Samha suka kalli junansu.

Abba yace "waye Sameer kuma?

Anty fanneh tana murmushi tace " daya daga cikin daluban marigayi ne. Dazun zanje kasuwa na ganshi. Ai Alhaji yaron nan yanada kirki kuma yanada hankali sosai, tun Samha tana karama take kirarin cewa shi zata aura don sun shakku sosai". Anty fanneh ta karasa maganar tana dariya.

Shima Abba dariya yayi sa'anan yace " toh ai bata bace ba, idan yana so ba sai a hadasu gabadaya har dana su Sabah ba?"

Abba ya juyo yana duban Sabah yace "yauwa Sabah, dazun mukayi magana da mami akan batun aurenka da yarinyar nan, tace tana so a tsayarda magana tunda kai da ita kun samu kun gana, kuma yarinyar ta amince tace tana sonka. Don haka, Inaso cikin weekend dinan ka shirya zamuje gidansu ku gaisa da mahaifinta".

Wani irin haushi ne ya turnike zuciyar Sabah barin ma Samha wace taji kamar ta kurma ihu nan take a wajen.

Anty fanneh ce ta lura da yanayin Sabah taga ya hada rai tamkar hadari, har ya bude baki ransa a bace zaiyi magana Anty fanneh tayi sauri ta girgiza masa kanta allamun karya ce komai yayi abunda mahaifinsa yace.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now