Chapter thirty-one

539 56 1
                                    

Wuri suka samu suka zauna suka yi shiru barin ma khadija da jikinta yayi bala'in sanyi ganin tsohon saurayinta Alamin.

Hawaye masu zafi ne suka soma gangaro mata ta sa hanu ta soma gogewa. Amjad yayi shiru yana kallonta.

Cikin sheshekar kuka ta soma fadin " ban san me nayi dana cancanci haka ba, wai kawata da saurayina suci amanata, musamman Alamin wanda nabashi zuciyata halak malak, meyasa zasu ci amanata haka? Me na musu?. Da acan baya nace bazan kara soyayya ba amma everything changed when i met you Amjad" ta karasa maganar tana rushewa da kuka.

Amjad shiru yayi yana dubanta tana kukanta daga bisani ta cigaba da fadin " nasa rai a wanan fitan namu, komai zai tafi yanda ya kamata, nida kai zamu samu mu fuskanci juna sosai, amma gashi wancan yazo ya bata komai."

Amjad ya cigaba da dubanta daga bisani ya kira sunanta a hankali " khadija...."

Khady ta dago kai tana dubansa da jajayen idanunta still bata daina kukan ba. Amjad yace "ki daina kuka khadija, inaso ki share hawayenki ki manta da komai. Abunda ya faru ya rigada ya faru kinji, i'm glad you've loosened up kuma daga yanzu ni Amjad na miki alkawari zan zame miki madafa a rayuwarki because daga yanzu kin daina fuskantar irin wanan kalubalin a rayuwarki kenan insha Allah, bakisan meye ba, a yanzu haka babu wace nakeso naji na kasance tare da ila khadija". Amjad ya karasa maganar yana sakar mata lalausar murmushi.

Khady wani irin dadi ne taji ya ratsa duk ilahirin jikinta da kalamansa, murmushi itama ta sakar masa tasa hannu ta soma goge hawayenta.

Amjad yana gama fadin haka ya juya ya dauko ledar daya ruko ya ciro wata kwali daga ciki daga bisani ya tsuguna a gabanta yana kokarin bude kwalin takalmin ya soma fadin " takalmanki basu miki daidai ba, meyasa kika tilasta wa kanki sasu?". Ya karasa maganar yana bude kwalin, wasu takalma shigen irin nada ya ciro daga cikin kwalin.

Hannu yasa ya kamo kafanta na dama ya soma saka mata takalmin kafa daya. Khady shiru tayi tana kallonsa tana cigaba da goge hawayen da suketa faman zuba mata bisa fuska.

Bayan ya gama sanya mata takalmin, ya mike yana dubanta sa'anan yace " ki share hawayanki ki daina kuka, insha Allah daga yau kinyi bankwana da heartache don daga yau Amjad ya rigada ya zama naki". Ya karasa maganar yana sakar mata lalausar murmushi.

Wani irin farin ciki ne ya lulube khady, nan take taji duk damuwar dake tattare da ita ya gushe. Ta kura mishi ido tana cigaba da kallonsa dan wani irin sonsa ne ke dadda karuwa cikin zuciyarta.

Bangaren su Sabah kuwa tafiya sukeyi shida Samha tana janshi da wasa tun yana dakewa har yazo ya soma sakin jiki, sunata faman wasa da dariya tare.

Samha ta dubeshi tace "Sabah zo muje mu hau roller coaster."

Sabah ya dubeta yace "Anya kuwa zaki iya? Duba yanda mutane suke faman ihu a ciki."

Samha ta marairace fuska tace "Sabah please, just once kaji muje mu hau".

Sabah Ajiyar zuciya ya sake sa'anan yace "toh shikenan, let's go."

Suna karasawa wajen Sabah ya siya musu tickets na hawa ride din. Suka je suka hau suka zauna a ciki. Ga wasu mutane suma tare da family dinsu suna zaune a sauran seats din dake sama. Amma banda yara don ba'a bari yara su shiga saboda height din roller coaster din, komai zai iya faruwa.

Tunda suka shiga suka zauna jikin Samha ya soma bari, Sabah ya dubeta sa'nan yace   "Idan kin san bazaki iya ba mu sauka".

Samha ta dage tace mishi babu komai zata iya. Can sai ga daya daga cikin masu tayar da engine roller coaster din yazo ya soma duduba karfen da aka rufe seat dinsu dashi ko ya rufu da kyau. Sai daya tabbatar dana kowa a rufe yake tukuna ya koma suka tayar da engine. A hankali roller coaster din ya soma tashi sama dasu.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now