Chapter Sixty-Four

391 50 0
                                    

Bangaren Sabah kuwa shima daidai lokacin ya tuna da zoben da ya yakeso ya bawa Samha nan take ya soma dube dube, jakansa ya bude ya soma dudubawa bai gani ba. Hankalinsa ne ya soma tashi.

Shinoh ne ya karaso inda yake yana fadin " SB wai me kake nema ne?"

Sabah bai tanka masa ba ya cigaba da dube duben da yakeyi.

Aliyah kwace zoben tayi daga hanun Madina ta zira a hannunta tana karewa zoben kallo cike da sha'awa tace "kai, amma zoben nan ya hadu".

Jiki a sanyaye Madina tace "zoben na mata ne ko?"

Juyowa Aliya tayi tana dubanta tace "wani irin tambaya ce wanan, toh da na maza ne?"

Madina ta sunkuyar da kanta kasa muryarta na rawa tace "Aliyah akwai wace Sabah yakeso ne?"

Wani irin freeze Aliyah tayi jin abunda Madina ta fadi.

Madina bata tsaya nan ba ta cigaba da fadin " jiya dayaje sauke ni a gida, ya yarda zoben bai sani ba, kuma ina tunanin ya ajiye zoben ne yanaso ya bawa budurwarsa".

Aliyah tace "kin gano kenan?"

Madina zaro ido tayi kirjinta na harbawa tace "Dan Allah da gaske Sabah yanada wace yakeso? Na santa?"

Shiru Aliyah tayi bata ce komai ba, can kasan ranta tace " tab ai ba a bakina za'aji mutuwan sarki ba".

"Aliyah? Ki fada mun mana". Madina ta fada muryarta na rawa tamkar zatayi kuka.

Suna cikin haka sai ga zack nan ya taho yana kokarin karasowa inda suke. Cikin sauri Aliyah ta ciro zoben daga hannunta ta bude tafin hannun Madina ta danka mata.

Zack yana isowa inda suke cike da zumudi ya soma fadin "Aliyah, ina kika shiga ne tun dazun naketa nemanki, kin manta yau kinyi mun alkawari zamuje muci abinci tare a cafeteria?"

Harara Aliyah ta watsa mishi tace "dallah can, yanzu ba daman mutum ya danyi lati?"

Zack ya soma sosa geyansa yace "kiyi hakuri gimbiyata, ai ko shekara nawa ne zan iya jiranki. Your wish is my command your highness".

Dariya Aliyah ta dan sake, zack ya dubi madina yace "Madina taho muje muci abinci mana".

Madina ta girgiza masa kanta jikinta a sanyaye tace "a'a nagode, nima dazun naci abincin".

Aliyah ta tabe baki tace "naga Alama ba yunwar kukeji ba, ni kunga tafiyata". ta fada ta soma tafiya ta barsu a wajen.

Zack har ya juya zai bi bayanta Madina ta dakatar dashi tana fadin "zack?"

Juyowa yayi yana dubanta yaga ta zira hannunta cikin jaka ta ciro chocolates har wrap uku ta mika mishi.

Kurawa chocolates din ido yayi, madina ta dan matso tayi Kasa da muryanta tace "ka bawa Aliyah".

Murmushi ya da'an sakar mata yana mata Godiya sa'anan ya kara gaba.

Suna isa Cafeteria suka tadda su Shinoh da Abbah zaune a ciki, nan Aliyah ta soma zayano musu yanda sukayi da madina.

Shiru sukayi suna sauraronta kowanansu cike da jimami da tsananin tausayin Madina.

Zack ne yace "Yanzu wazai fada mata kenan?"

Abbah ya girgiza kai yace "badai ni ba don gaskiya bazan iya ba".

Zack yace "amma idan aka cigaba da boye mata she'll be more hurt. Ni a ganina gwanda kawai a fada mata ta sani tun yanzu".

Aliyah tace "gaskiya kam, gwanda chocolate girl ta sani tun wuri kafun abubuwa suyi nisa".

Shinoh yace "tab ace mutum kamar ki mai daskararen zuciya ta garara fada mata ina ga mu?"

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now