Chapter - seventy eight

659 64 5
                                    

Cikin dare zafin jikin Samha ne ya farkar da Sabah, a hankali ya soma jin zafin jikin na ratsa jikinsa. Ya bude tsumammun idanunsa ya da'go yana dubanta yaga sai faman kwasar baccinta take.

"Subhanallah" ya fada can kasan ransa hade da shafo fuskarta. "Da alamun kamar zazabi kesan ya lulubeta kamar na daren farkonsu. To meya sameta kuma?" Ya tambayi kanshi.

Shiru yayi ya kura mata idanu yana tunanin abun yi. Da kamar ya tashe ta sai kuma ya fasa aikata hakan ya sake janyota jikinsa ya matse gam, har suna iya shakar numfashin juna. Within minutes zafin jikin nata ya soma rabar jikinsa. A hankali ta bude idanunta wanda ke cike da giyar bacci ta soma kallonsa.

Jin ta farka ne ya da'go yana dubanta yace "Baby what's wrong? bakida lafiya ne, ya naji jikinki da zafi haka?"

Da'an bata fuska tayi sa'anan tace "lfy na kalau, please kishi nakeji ka kawo mun ruwa nasha"

Mikewa Sabah yayi yaje ya dauko mata bottle water dake wajen dressing mirror dinta sa'anan ya kawo mata ta karba ta soma sha. Tana gama sha ta mika masa robar ya ajiye. Kafun ya juyo har ta koma baccin. Kura mata ido yayi yana kallonta sa'anan ya duba lokaci yaga hudu da rabi na asuba ya soma tunanin ko zai iya tafiya ya barta cikin wanan halin amma sai yaga ta cigaba da baccin nata ko a jikinta. Yafi 10 mins yana wanan tunanin ya sake kai hannunsa ya tabata yaji zafin ya da'an sauka sosai.

Ajiyar zuciya ya sake sa'anan ya mike ya fice daga dakin ya koma dakinsa, bai koma bacci ba yaje ya dauro alwala yazo yayi rakatainul fajr Sai da gari ya kusan wayewa tukuna ya mike ya fada bayi yaje ya watsa ruwa a jikinsa ya fito. Yana kokarin sa kaya ya soma jin sautin muryan Anty fanneh. Cikin sauri ya iddasa sa kayan nasa ya fito yabi inda yakejin sautin muryanta na fitowa. Daga direction din dakin Samha ne yasa ya karasa cikin sauri ya shiga dakin ganin Anty Fanneh yayi tanata faman ririke Samha daketa faman kwara amai tamkar zata amayo da kayan cikinta. A firgice yake binsu da kallo don yanda taketa faman yunkurin aman yayi mugun tadda masa hankali. Bai san sanda ya karaso shima ya riketa ba yana mata sannu, gabadaya ta fita hayacinta. Sai da asuban nan Zazzabin ya ciyota da karfi hade da azababen ciwon kai. Da kyar dai aman ya samu ya lafa mata, Anty Fanne da Sabah suka taimaka mata tazo ta zauna a gefen gado nan take ta fashe kuka "wayyo Allah Ammi, kaina, jikina duk ciwo".

Hankalin Anty fanneh a tashe ta taba wuyanta taji zafi radau ta da'go ta soma fadin "oh Allah nidai na gaji da kananan zazzabi zazzabin nan da kikeyi Samha. Anya ba malaria bane ke damunki? Sabah ko zaka kira mana doctor fahad ne yazo ya dubata ayi treating abun nan once and for all?"

Babu musu Sabah ya fice daga dakin hankalinsa a matukar tashe yaje kiran doctor Fahad. Bugu daya Dr Fahad ya da'ga Sabah yayi mishi bayani yace toh gashi nan zuwa dayake family doctor ne kuma ya taba duba Samha tun kafun Anty Fanneh ta auri Abba.

Within 20 minutes sai gashi nan yazo da kayan aikinsa, suka gaisa da Sabah sa'anan ya haura dashi sama zuwa dakinta. Tana kwance Anty fanneh na gefenta suna faman mata sannu. Nan take likitan ya soma tambayarsu abunda ke damunta Anty Fanneh ta soma mishi bayani likitan yace zai debi jininta yaje yayi mata test tukuna a gano meke damunta. Haka dr Fahad ya deba jinin nata yace zaije ya dawo. Bayan barin likita gidan Anty Fanneh ta kira Abba a waya tana sanar da shi cewa zazzabi na damun Samha. Hankalinshi ne ya da'aga yace a kaita asibiti mana. Anty fanneh tace ai likita yazo ya dubata har ya deba jininta za'ayi mata test. Abba yace toh shikenan Allah ya bata lafiya shima gashinan kusa da gida. Ba'a jima ba sai ga Abba nan ya shigo shima ya soma mata sannu, yana karasowa inda take kamshin turarensa ya bugi hancinta nan take ta kuma yunkura cikin sauri ta mike ta fada bayi sai amai, sallati Abba ya soma yi yana mata sannu Anty fanneh taje ta riketa, tun tana yunkurin amman har tazo ta kasa saboda babu komai a cikinta. Duk jikinta yayi weak. Kasa juriyar ganinta a hakan Sabah ya juya ya bar musu dakin ya koma dakinsa hankalinsa a matukar tashe.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now