Chapter Eight

727 87 1
                                    

Washe gari da safe samha ta farka zuciyarta fess cike da dokin zuwa makaranta don ta samu taga ruhinta. A gurguje ta gama shirinta ta fito tana jiran anty fanneh. Abun ya bawa anty fanneh mamaki don so tari ita take jiran samha ta gama shiri kafun ta fito don wani sai'in ita ke janyo mata zuwa aiki late, samha gabadaya abubuwanta yinsu takeyi cikin sanyi jiki don batada zafin nama.

Suna barin gida kai tsaye anty fanneh ta ajiyeta a makaranta sa'anan ta wuce aiki. Tana shiga department bafi minti goma ba sai ga kiran Amjad nan ya shigo wayarta ta daga " baby kina ina, kin baro gida ko kina school?

"Ina school" ta bashi ansa.
Yace toh shima gashinan zuwa yana hanya ya katse wayar.
Bafi minti goma ba Amjad ya shigo cikin aji, kasancewar yau Friday sanye yake cikin manya kaya, kaftan ya saka da hula wace tayi matching din kaftan dinsa. Yayi kyau sosai sai daukan ido yakeyi.

Samha na ganinshi kasa dauke idanunta tayi daga gareshi don yayi mata kyau sosai. Karasowa yayi yazo ya zauna kusa da ita yana murmushi.
"Wanan kallon fa?" Ya tambayeta.
" laifi nayi don na kalla sweetheart dina?" . Wani irin dadi yaji ya ratsa shi daya ji ta kirashi da sweetheart dinta.
"A'a, ina ke ina yin laifi. Ai ke yanzu sarauniya ce a cikin zuciyata kin wuce yin laifi". Ya fada mata. Ita kam dariya kawai ta sake.
Shiru yayi ya kare mata kallo sa'anan yace "kinyi kyau fa yau baby. Ban san meyasa kullum idan na ganki sai naga kin kara mun kyau"

Dariya samha tayi sa'anan tace "wato dan kar in cike kayi kyau shine ka rigani fada koh?"

"Ah haba wane ni, ina ni ina kyau anan bayan gaki kusa dani. Ke ai first class beauty ce samha. Baki ji sunan ki ba. Me ake nufi da samha in ba kyau ba?"

"Kinga idan na sameki a matsayin matata ba karamin kyau yaranmu zasuyi ba musamman idan suka dauko wanan cute baby face naki"
Dariya sukayi tare tana girgiza kai. "Amjad kenan
" Atoh meye, gaskiya na fadi ai". Dariya ta sakeyi nan ya cigaba da zolayan ta. Suna cikin hirarsu sai gasu khadija sun shigo ajin ita da Amina. Don a lokacin sauran dalibai duk sun shigo sun za zauna ana jiran lecturer din ya shigo.

Khadija ce ta kashe wa samha ido daya suna murmushi sa'anan suka nema wuri a seat din baya suka zauna. Cikin dan kankanin lokaci lecturer dinsu ya shigo ya fara musu lectures. Bayan sun gama lectures, Amjad yace suje cafetaria su dan ci wani abu. Samha ta juyo zatayi wa su amina magana, Khadija ta girgiza mata kai ta mata alamun da su tafi kawai zasu zo daga baya. Haka suka fita suka bar ajin idanun kowa nan kansu, don yan ajin har yanzu mamakin ganinsu sukeyi tare musaman amjad da basu taba ganinshi da wata ya mace ba sai wanan karan.

Suna isa cafeteria, Amjad yayi musu order abinci suka je suka zauna, ba jima ba aka kawo musu abincin aka jera a gabansu. Nan suka fara ci suna hira suna dariya cike da so da kaunar junansu.
Suna cikin cin abinci kamar ance samha ta dago, sai tayi ido biyu da Sabah, shima yayi ordering abinci kenan zai ci.

Suna hada ido ya sakar mata murmushi daga inda yake ita kuma ta galla masa harara Kirjinta na bugawa da sauri da taga ya soma nufowa inda suke zaune. Girgiza masa kanta ta soma alamun kar ya kuskura ya karaso inda suke, shareta yayi fuskarsa dauke da murmushi kamar ko wani lokaci ya fara takowa har ya karaso inda suke. Samha ta dube Amjad taga bai ma lura da abunda yake faruwa ba, don ya ciro wayarsa yana danawa, hankalinsa baya wajen.
Sabah yana karasowa yazo ya tsaya dab da table dinsu, idanunsa kyam a kanta ko kyaftawa bayayi. Daddaden kamshin turarensa duk ya bibiye inda suka zaune.

Amjad jin tsayuwar mutum a kansu ne yasa ya dago, Sabah ya gani tsaye sai faman bin samha yake da kallo. Amjad ya kalli Samha sa'anan ya sake dawo da dubansa ga Sabah "ya mallam lafiya kazo ka tsaya mana a ka haka?"

Samha ta bude baki zatayi magana kenan Sabah ya riga ta yace " Nasan baka wayeni ba, sunana Sabah, nine yayan Samha" ya fadawa Amjad yana murmushi.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now