Chapter fifty-one

540 43 3
                                    

Sabah yana ganin Sameer ya karaso inda suke yayi fuska ya kawar da kansa gefe .

Samha kame kame ta soma yi, Sameer wanda baiji dadin yanayin daya zo ya gansu su bane yace "Samha meke faruwa. What's going on?"

Cike da jin kunyarsa tace "nazo ina posting flyers ne, shine na fadi".

Sameer kallonta yayi fuskarsa cike da tuhuma don bai gamsu da abunda ta fadi ba.

Dawo da dubansa yayi ga Sabah wanda ya cika yayi fum. Sai faman harare harare yakeyi.

Ganin Sameer ya kurawa Sabah ido ne yasa tace " Sameer wanan shine yayana Sabah, wanda na...."

"Na sani. Bashi ne yaron VC ba?"

Wani irin kallo Sabah ya watsa mishi yace " toh sai me?"

Gaban Samha ne ya tsinke ya fadi jin maganar da Sabah ya fadawa Sameer don haka ta shiga bawa sameer hakuri.

Sameer murmushi kawai yayi yace " karki damu Samha, your brother seems interesting".

Wani irin kallo Sabah ya sake watsa mishi sa'anan ya kawar da kansa gefe, daga nan bai sake cewa komai ba.

Suna cikin haka sai ga miss sophie, daya daga cikin junior lecturers na department din tazo tace "Mr Sameer, dean yana nemanka a office".

Sameer yace "Alright, gani nan zuwa".

Sallama sukayi shi da Samha sa'anan ya juya suka bar wurin shi da miss sophie.

Samha tana tsaye, gabadaya jikinta yayi sanyi kirjinta sai faman bugawa yake, juyowa tayi tana duban Sabah tace " Allah yasa bai gano cewa akwai wani abu tsakanin mu ba"

"Ban gane ba, me kike nufi? His suspicion is correct because definitely akwai wani abu tskanin mu. Gwanda ma tun wuri yasan da hakan". Sabah ya fada mata ransa a bace. Shi daman tun ranar daya fara ganin Sameer yaji gabadaya guy din bai kwanta mishi ba musamman yanda yaga Samha ta sake jiki dashi sunata hira. Wani irin kishi ne yaji yana cinsa cikin kokon zuciyarsa.

Samha data lura da yanayinsa cewa kishi ne karara ke cinsa, yasa taja bakinta tayi shiru. Tasan tana fadin wani abu yanzun nan zasuyi fada.

Sameer kuwa suna cikin tafiya, miss sophie ta dubeshi tace " daman kasan yaron VC ne?"

Sameer yace mata "noo, ban sanshi ba. Yarinyar dake tsaye kusa dashi ne na sani. Itace yarinyar mentor dina"

Miss sophie ta gyada kai tace "okay na gane".

Haka suka karasa wurin office din dean din tare.

*******************

Zack, shinoh, Abbah suna zaune a inda suka saba kebewa bayan lectures wato restroom dinsu.

Zack ne yaketa faman musu da Shinoh akan wani game da suke bugawa.

Suna cikin maganarsu sukaji wani dadaden kamshin turare ya buge hancinsu hade da wata zazakar murya tayi musu sallama ta shigo.

Tare suka dago kai suka ansa sallamar, ai kuwa Sake baki sukayi a tare ganin wata kyakyawar yarinya fara sol tsaye a bakin kofa tana kallonsu da shanyanyun idanunta. Sanye take cikin doguwar riga blue mai ratsin fararen flowers. Sai dan karamin farin gyale data yafa.

Fuskarta babu makeup amma tayi kyau sosai, don kallo daya zaka mata ka gane cewa daga gidan hutu ta fito.

Su Zack ne da Abba suka shagala da kallonta. Shinoh ya bude baki yace "Masha Allah, kunga abunda idanuna suke gane mun kuwa?".

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now