Chapter fifty- six

386 53 1
                                    

Bugun kirjin Samha ne ya karu, nan take taji bazata iya kara koda minti daya a wajen ba don haka kafun su ganta, ta juya ta soma tafiya jikinta a mugun sanyaye.

Sabah ne ya juyo yana duban Madina wace taketa faman murna kamar zata hadiye shi. Ya dawo da dubansa ga hannunta inda ta  rikeshi gam yace "mallama ya haka? Cika mun hannu mana".

Madina ta sakar masa hannu, tana murmushi cike da zumudi ta soma fadin " Kaga yanda Allah yake tsara abunsa ko, we are really connected and destined for each other Sabah, ranan dana fadi kan hanya har glasses dina suka fashe kaine ka taimaka mun, tun daga lokacin naketa mafarkin Allah ya sake hadani dakai. Ban taba tunanin kaine wanda daddy na yakeso ya hadani aure da ba."

Sabah d yayi shiru yana kallonta ya saki ajiyar zuciya yace "i thought i made myself clear ranan, it doesn't matter ko kece yarinyar dana taimakawa ranan  ko kuma yarinyar da tsofin mu suke son su hadani aure da. I'm not interested in you, bana sonki". Ya fada mata kai tsaye.

Wani irin zafi Madina taji a cikin kirjinta dajin kalamansa ta marairaice fuska tace  "Sabah please don't do this to me, tunda nake ban taba jin zuciyata ta buga akan wani da' namiji ba sai akanka. Inasonka, pls Ka dan bani dama mu fahimci juna, kilan na samu gurbi a cikin zuciyarka".

"Bazai yu ba". Ya sake fada mata kai tsaye.

"It's okay, I don't want to give up don akan sonka zan iya yin komai" Madina ta fada mishi tana kallon cikin kwayar idanunsa.

Sabah shiru yayi yana kallonta bai sake cewa komai ba.

Samha tana karasawa ta nema wuri ta zauna jikinta a matukar sanyaye. Aliyah ce ta bita da kallo tana mamakin ganinta haka.

Samha har tayi zurfi cikin tunani sai ga Sameer nan ya karaso inda suke yazo ya tsuguna a gabanta yana tambayarta abunda yake damunta.

Har ta bude baki zata bashi ansa, sai ga Sabah nan ya taho, Madina tana biye dashi.

Tsayawa yayi ciruss yana kallon yanda Sameer ya tsuguna a gaban Samha, nan take yaji kishin ya sake taso masa sabo. Zuciyarsa na masa tafarfasa, Har wani dishi dishi ya soma gani tsabar kishin da yake cinsa.

Itama Samha juyowa tayi tana kallonsa, sa'anan ta dawo da dubanta ga Madina dake tsaye kusa dashi. Nan take itama taji wani irin kishi ya rufeta ta kawar da kanta gefe.

Sameer shima shiru yayi yana kallonsu don yama rasa me zai ce.

Suna cikin haka, sai ga sauran yan team nan sun karaso, Gabadayansu a gajiye suke don ba karamin training suka sha ba.

Samha da Aliyah ne suka mike suka soma serving dinsu abinci, itama Madina tazo ta sa musu hannu.

Nan hira ta barke tsakaninsu, sunata raha akan training din da suka sha yau.

Shikam Sabah wuri ya samu a gefe ya zauna, ya cika yayi fumm, yaki kula kowa zuciyarsa sai faman tafarfasa yakeyi. Samha tazo tana kokarin yi masa magana ma yayi banza da ita yaki kulata har ta gaji ta kyaleshi.

Madina ta dago tana dubansa, itama tana so tayi masa magana amma tana shakka don taga yanayin nasa ne sai a hankali.

Hannu tasa cikin jakarta ta ciro chocolates ta soma rabawa kowa a wajen.

Aliyah dake zaune kusa da zack ta watsa wa Madina wani irin kallo tace "wlh na tsani ganin yarinyar nan, kwata kwata ban kaunar ganinta, ko dayake kune kuka janyota ai, daman ku maza haka kuke ba daman kuga farar mace".

Zack ya dubeta yace " kuma ai mata kunfison irin kalan namijin da zaiyita wahalar daku".

Harara Aliyah ta watsa mishi don tasan da ita yake kuma tasan inda maganar nasa ya dosa don haka ta mike ranta a bace tace "wai zack meke damunka ne yau?! Tun muna hanya kaketa wasu maganganun da ban gane kansu ba".

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now