Chapter fourty- eight

413 51 4
                                    

Sabah yana barin wajen, straight gida ya wuce, har ya manta ma da abunda ya faru.

Yana shiga cikin parlour ya tadda Samha tana kokarin shirya dining itada sophie.

Ya mika mata ledodin daya ruko yace "ina d'an naki yake?".

Tace mishi "yana can daki tare da mamansa".

Yace "toh gashi nan sai ki kai masa".

Samha ta karba ledan tayi masa godiya, shi kuma ya haura sama zuwa dakinsa.

A kwana a tashi sai dasu Anty katibe sukayi kusan sati biyu tukuna tace zasu koma dubai.

Samha kam harda kuka don za rabata da Azirak. Amma anty katibe tace zasu zake zuwa idan an samu wani hutun insha Allah.

Haka kwanaki suka shude, yanzu suna neman kusan wata daya kenan da aure, zama suke hankali kwance babu wani tashin hankali sai ma peace of mind da anashuwa da ake dadda samu a cikin gidan.

Samha da Sabah still suna soyayyarsu amma koda wasa basu taba barin iyayyensu sun gane hakan ba.

Ita kam bangaren su Mami daman yau ta shirya zata je gidan d'an nata don tunda akayi biki bata samu taje gidan ba. Ta kirasu a waya ta sanar dasu batun zuwan ta. Sukace sai tazo Allah ya kawota lafiya.

Tacewa Shafa ta shirya zata rakata zuwa gidan. Haba murna kuwa a wajen shafa kamar meye.

Yau finally, at long last zata je taga ruhin rayuwarta.

Murna da tsale ta dinga yi sai faman rawar jiki takeyi. Mami ta dubeta tace "idan baki daina wanan rawan jikin da kikeyi ba, babu inda zani dake.".

Cike da shagwaba shafa tazo ta zauna kusa da ita tana fadin "kai Mami, yanzu me nayi kuma? Dan na nuna farin cikina akan zamu je gidansu yaya Sabah shine wani aibu?"

"Nidai na gaya miki, kuma ki cigaba ki gani".

Turo baki shafa ta soma yi, ta mike ta haura sama zuwa dakinta taje ta soma shiri.

Misalin karfe uku na rana suka dau hanya, drivern gidan nasu ne ya jasu a mota suka tafi.

Dayake daga lekki zuwa Apapa akwai d'an nisa gashi kuma ranar an zuba go-slow ba kadan ba. Ba Su da isa Apapa sai karfe shida na yamma.

Anty fanneh ce tazo ta tarbe su tanai musu sannu da zuwa cike da fara'a tace "sannunku da zuwa Mami, kunsha hanya".

Mami tace "wlh unguwan naku ne akwai nisa, ga go-slow da muka tadda a hanya. Abun dai ba cewa komai". Anty faneh ta karba jakan mami daga hannunta suka karaso cikin parlourn tare, suka nema wuri suka zauna.

Shafa ce ta soma gaisheta tace "Anty ina wuni".

Anty faneh tace "ina gajiya. Ya gida?"

"Lafiya kalau". Shafa ta bata ansa. 

Anty fanneh ta dawo da dubanta ga Mami tace "sannu Mami kunsha hanya, bari a kawo muku abu mai sanyi kusha " tana gama fadin haka ta mike ta shiga kitchen taje ta lebo musu lemuka masu sanyi, ta kawo ta jera musu a gabansu, Sai faman yi musu sannu da zuwa takeyi.

Mami taji dadi sosai da yanda Anty fanneh ta tarbe su.

Shafa kuwa sai faman karewa ko'ina na gidan kallo takeyi don bata taba zuwa wanan sabon gidan ba. Sai taga wanan gidan ma ya ninka nada a kyau.

Sai faman baza idanu takeyi ko zata ga sanyin idaniyanta amma bata ganshi ba. Gashi babu daman tambaya.

Bayan sun gaisa Mami ta dubi Anty fanneh fuskarta dauke da murmushi tace "da fatan dai mun sameku lafiya? ya zaman gidan ina fatan babu wata damuwa ko matsala?"

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now