Chapter sixty-seven

445 50 0
                                    

Yau kwana biyu kenan da tafiyar Madina.

Amjad, Zack, Aliyah da khadie zaune suke a cikin class suna tataunawa.

Zack yace "tab daman Teacher Sameer da Samha sunyin sharing irin wanan past din? Amma Amjad, kace Khaleesat din tanada kyau sosai?" Ya karasa maganar yana murmushi yana shafa sajensa.

Harara Aliyah ta watsa mishi tace "meye haka kuma?"

Hakuri ya soma bata yana sosa kai.

Tsaki ta buga mishi sa'anan ta dawo da dubanta ga khadie tace "khadija ya kike tunanin za'ayi kenan?"

Zack yace "ya kamata mu taya khaleesat kwato soyayyarta daga wurin teacher sameer, ko ya kuka ce?"

Dukkansu suka gyada kai suka yarda da wanan shawaran.

Sameer kuwa yana cikin office dinsa sai faman trying  number khaleesat yakeyi amma sai yaji a kashe. Gabadaya hankalinsa a tashe yake ya gagara samun sukuni.

Yana zaune yaji anyi masa knocking a kofa, dagowa yayi yana duban kofar sa'anan ya bada izinin shigowa.

Su Zack ne yaga sun shigo suka soma gaishe shi, ya nuna musu wurin zama.

"Ya lafiya?" Ya tambayesu.

Khadie tace "munzo ganinka ne Teacher Sameer".

"Akan batun Khaleesat ne". Aliyah ta fada mishi kai tsaye.

Wani irin jimm yayi ya kawar da fuskarsa gefe.

Khadie ta cigaba da fadin "gaskiya teacher Sameer you need to do something about this, karka bari Khaleesat ta kubuce maka. Tun wuri gwanda kasan abunyi".

Ajiyar zuciyar Sameer ya sake sa'anan yace " banjin zata saurareni kuma, i've disappointed her too much".

Aliyah tace "karka manta Teacher Sameer, khaleesat ta baka tsawon hour ashirin da hudu ka nemeta, kaga you still have time to go after her, don't give up"

Khadie tace "yau ne birthday din Samha, kaga daga yanzu zuwa gobe ya kamata kayi fighting love din dake tsakaninka da khaleesat".

Shiru yayi yana sauraronsu daga bisani yace "toh shikenan. I'll give it a try".

Godiya yayi musu sosai da sukazo suka bashi wanan shawaran da karfin gwuiwan.

Sameer yana tashi daga school straight gidansu Samha ya nufa don ya bata birthday gift dinta.

Daman ya kira Anty Fanneh a waya ya sanar da ita zuwansa.

Cike da fara'a Anty Fanneh tarbe shi a parlour suka zauna.

Bayan sun gaisa, ta soma tambayarshi ya makaranta. Yace mata lafiya lau alhamdulillah".

"Samha fa?" Ya tambayeta.

"Wlh dazun ta fita na aiketa, amma bazata jima ba yanzu zata dawo".

Sameer yace "okay daman na kawo mata sakonta ne na birthday".

Anty fanneh tace "oh ni, Sameer kai dai baka gajiya".

Dariya kawai Sameer yayi, Anty fanneh ta mike tace mishi tana zuwa sa'anan ta karasa kitchen.

Bangaren Su Samha kuwa, tsaye suke ita da Sabah a cikin SuperSaver supermarket, Sabah yana kokarin yiwa matar dake tsaye a gaban counter din magana yace mata sunzo karban cakes din da akayi order.

Matar tace "birthday cakes ne?"

Sabah yace mata "eh".

"Toh shikenan, bari nasa ayi muku boxing dinsu".

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now