Chapter six

717 69 1
                                    

Washe gari da safe samha ta tashi, Yau kam batada lectures sai zuwa karfe biyu na rana. Bayan ta shiga bayi ta wanke bakinta ta fito taje dakin anty fanneh don ta gaisheta, ta sameta tana faman shirin zuwa aiki.
"Ammi ina kwana" ta gaishe ta.
"Lafiya lau baby, kin kwana lafiya? ya ciwon kan yanzu. Hope dai ya lafa miki?" Anty fanneh ta tambayi diyarta.
Samha ta bata ansa da eh ya lafa mata.

"Toh nasan yau bakida lecturers da wuri, zan baki dan kudi keda lami zuwa anjima kuje kasuwar kingsway ku danyi mun cefene. Kinsan munada bako yau zai zo, so inason a dan dafa mishi delicacies."

"Kai ammi wai dan Allah dan yaron mutumin nan zai zo zaki wani ba kanki wahala kiyi girki? Sai kace wani babban bako zamuyi. Ai ko snacks da ruwa aka bashi idan yazo sun isheshi."

" Kuji mun yarinyar, dan nashi kike ce ma yaro? Toh ashekaru dai ya girme ki nesa ba kusa ba don har shekara hudu ya baki da zaki ce mishi wani yaro. Kinga idan Allah ya yarda ma very soon shima zai zama dana. Kinga zaki samu yayah namiji da zai dinga kula da ke ballanta ma kinga makarantar ku daya. Bayan haka Kumma samha, ance bakonka annabin ka. Kema kinsan duk bakon da zamuyi a gidan nan sai mun mushi tarba mai kyau. So bana son wani surutu, ga kudin nan anjima in kin shirya kuje mun kasuwa".

Dariya samha tayi tace " Toh ammi yi hakuri, na tabo miki da. Bazan sake kiranshi yaro ba daga yanzu ma yayah zan dinga ce mishi"

anty fanneh tace " wanan kuma keh kika sani,in kinga dama ki kirashi da kaninki, wanan ya rage tsakaninku. Ungo ki karba, ni kinga tafiyata ban so nayi late." Anty fanneh ta mika mata kudin, ta karba sukayi sallama ta wuce aiki.

Samha na shiga dakinta tadda wayarta nata faman ringing akan gado. Da sauri ta karasa ta dauki wayar, sunan amjad ta ganni a rubuce a wayar ta daga.

Muryanan nashi mai dadin sauraro kuma mai kashe mata jiki taji ya doke kunnenta. " hello samha, good morning ya kike?

Lumshe idanunta tayi kamar yana gabanta sa'anan tace mishi "lafiya lau"

"Da fatan kin tashi lafiya?" ya tambayeta.

" Lafiya lau, ya gida?" ta tambayeshi.
Nan shima ya bata ansa. Ya fara tambayarta karfe nawa zata shigo makaranta yau. Tace mishi kafin karfe biyu.
"Zan iya biyowa ta gidanku sai mu wuce school tare? Ya tambayeta.

Cike da zumudi ta bashi ansa da eh yabiyo ta gidan nasu. Yace ta turo mishi da address. Tace toh zata turo mai sukayi sallama.

Tsalle ta dinga yi tanata faman murna. Ji takeyi kamar a mafarki. Wai yau amjad ne zai zo har gida ya dauketa su tafi makaranta tare?.
Duba lokaci tayi taga har sha daya ta kusan yi. A gurguje ta fada bayi tayi wanka ta fito ta shirya, ta kira lami suka tafi kasuwa. Driver din gidan ne ya kaisu, Nan suka tsaya sukayi cefanen da anty fanneh ta aikesu. A hanyar dawowarsu ma suka dan samu go slow a hanya. Barin ka lagos da hanyoyinta bata taba rabuwa da traffic.
Ko da suka dawo gida ma lokaci har ya tafi don karfe daya har ta gota. Ta haura sama ta fara shirinta zuwa makaranta.

A gaban mudubi ta zauna bayan ta fito daga wanka ta fara caba kwaliya. Dayake bata wani saba yin make up ba, tana gamawa taga ta canza kamar ba ita ba. Doguwar sumar ta data sha gyara sai shekki takeyi ta fara tajewa. Sa'anan ta dauko Ribbon ta tufke gashin a tsakiyar kanta. Samha bata cika yin kitso ba saboda laushin gashinta, ko tayi warwarewa take. Shiyasa rai da rai zaka ga sumar kanta babu kitso.
Doguwar abaya ta ciro ta saka, ya zauna a jikinta cib cib kamar an gwadata akayi dinki. Ta dauko gyalen abayar tayi wrap round dashi. Turaruka ta debo ta fefesa gabadaya jikinta. Tana cikin haka wayarta ta fara ringing ta daga. Amjad ne ya sanar da ita yana kofar gidansu. Tace mishi gatanan yanzu zata fito. Yace toh sai ya ganta.
Bakin takalmi ta ciro ta sanya a kafanta sa'anan ta dau jakar makarantarta ta fito.
A nan kofar gida ta tadda dashi yayi parking motarsa. Bude kofar seat din gaba tayi hade da sallama ta shiga ta zauna.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now