Chapter fifty - three

407 46 0
                                    

Washe gari da safe misalin 11:30 pm, Samha tsaye take tare da sauran yan basketball team nasu.

Yau ta kasance ranar da zasuje hiking, kuma wanan hiking din ta zamewa yan team din ta'ada, ko wani lokaci idan competition tana gabatowa sai sunje sunyi wanan hiking din don su motsa jiki kuma su samu intense practice a wajen.

Ko wani team member sanye yake cikin track suit, black and white.

Samha da Aliyah kuwa, a matsayinsu na team managers suma sanye suke cikin track suit dinsu black and white, sai yar karamar gyale da samha ta yafa, ita kam Aliyah p cap dinta ta sanya abunta don babu ruwanta.

Suna tsaye suna jiran team captain dinsu wato Amjad ya karaso, don shi kadai kawai ake jira sai Sabah. Already coaster bus din da zai kaisu yazo yana jiransu.

Bafi minti biyar ba sai ga Amjad nan ya karaso cikin sauri Teacher Sameer yana biye dashi.

Samha tana dagowa sukayi ido biyu da Sameer. Kallonshi takeyi cike da mamaki don batayi expecting zuwansa wajen ba.

Suna karasowa Amjad ya soma basu hakuri akan latin da sukayi kuma tunda makaranta tayi mandating outside school activities dole sai akwai malamin da zaisa ido don haka Sameer yayi volunteering zai bisu kuma ya zama team advisor dinsu.

Zack ne ya taba shinoh yace "kaga wanan malamin wai shinan zaiyi supervising dinmu. Anya zai iya hiking dinan kuwa, kar muje fa ya suma mana a hanya."

"Ai kam gwanda mu gayawa Amjad ya taho mana da stretcher in case". Shinoh ya fada yana dariya.

Amjad ya dubi Samha da Aliyah yace "Team managers, what do you think?"

Murmushi Samha ta sake sa'anan tace "Hakan ma yayi don nasan Sameer sosai a da, yana son sports. Don da saura kadan ya samu shiga wani pro basketball team amma hatsarin daya samu yaji ciwo a kafa ne yasa bai cigaba ba yayi give up. Amma he's very good"

Sameer ya karaso inda take yana murmushi yace "Samha ashe baki manta ba kenan? Kin tuna lokacin da kike karama sai kiyita yiwa amminki magiya akan cewa sai kin bini munje mun buga kwallo?"

Dariya Samha ta sake tana rufe fuskarta cike da jin kunya. Shi kuwa ya cigaba da zolayenta yana tuno mata da yarantar ta.

Basu lura da Sabah ba wanda ya tuko bike dinshi ta daga can gefen titi yayi parking, kura musu ido yayi yana kallon yanda Samha taketa faman murmushi itada Sameer.

Wani irin tafarfasa yaji zuciyarsa na masa nan take yaji wani irin azababen kishi ya lulubeshi.

Samha ce ta fara hango shi, tana dagowa sukayi ido biyu dashi, nan da nan tasha jinin jikinta, murmushin dake manne bisa fuskarta ta dauke. Kirjinta ne ya soma mata wani irin mahaukacin bugu dataga irin kallon da Sabah yakeyi mata da Sameer, don ita kadai tasan ma'anan wanan kallon dayake musu.

Sabah yafi 10 minutes a wajen yana jingine akan bike dinsa idanunsa kyam akansu.

Samha babu shiri tacewa Sameer tana zuwa sa'anan ta karaso inda Sabah yake tsaye ta soma kokarin yi masa magana amma yayi banza da ita. Shidai kawai focus dinshi akan Sameer yake.

Amjad ne yasa sauran team members din suka fara shiga cikin katuwar coaster bus dazai kaisu camp garden.

Bayan kowa ya shiga cikin bus din, Amjad ya karaso shima ya soma kokarin yiwa Sabah magana da akan ya shigo cikin bus din su tafi, don shi kadai ake jira.

Samha ma tasa baki tace "Sabah kazo muje mana".

"Ku rabu dani kuyi tafiyarku, i'm going alone!" Yana gama fadin haka ya juya a fusace zai tayar da bike din nasa.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now