Chapter thirty - five

474 47 1
                                    

Washe garin ranar, Samha tana zaune cikin daki tana shafa mai a jikinta don bata jima da fitowa daga wanka ba.

Wayarta ce ta soma ringing, ta dauko taga sunan Sabah a rubuce a jikin screen din.

Nan da nan ta daga ta kara kunnenta, don rabon data jishi ko ta sanya shi a idanu tun jiya a gidansu.

Dadaden muryan shi mai sanyaya mata rai ako da yaushe idan taji ne ya doki kunnenta yana fadin "Kanwata?"

"Na'am?"

"Ki fito yanzu, gani a kofar gida".

"Ban gane ba, wani kofan gida kuma?"

" oho, in zaki fito ki fito". Yana gama fadin haka ya katse kiran.

Dago wayar tayi daga kunnenta tana kare ma screen din kallo.
Anya kuwa da gaske yake? To meya hanashi shigowa, ya tsaya a waje? Ta soma tambayar kanta.

Nan kuma ta soma tuno da abubuwan da suka faru a jiyan. Jiki a sanyaye ta soma sa kaya tayi shirinta tsab cikin wata doguwar riga Ash da kuma black veil, power tadan shafa a fuskarta da dan shafa man baki, sa'anan ta dauko turaruka ta feshe duk ilahirin jikinta dashi, ta fito daga dakin ta sauko kasa, tana isa kofar gida ta hango shi tsaye ya jingina da jikin motarsa.

Sanye yake cikin black jeans da black tshirt sai black face cap.
Komai na jikinsa black ne harta, motarsa ma baka ce.

A hankali Samha ta tako har inda yake tsaye jingine a jikin mota. Yasa hanunsa duka biyu rungume bisa kirjinsa ya kura mata ido har tazo ta tsaya a gabansa.

Itama ido ta kura masa, tasa hannunta duka biyu ta rungume bisa kirjinta kamar yanda yayi ta tsaya tana kallonsa.

Sai da suka kalla juna har na kusan minti biyar, kowa da yanda yakeji game da dan uwansa.

Barin ma Samha, wanda ganinshi yanzu yasa ta kara jin wani irin sanyi a ranta. Anya kuwa zata iya rayuwa babu Sabah? Don sonshi a yanzu ya gama kama duk gabobin jikinta, da sonshi take kwana da sonshi kuma take tashi a kullum.

Jiki a sanyaye ta kira sunansa a hankali ta soma fadin " Sabah.....bansan yanda zanyi ba, na kasance inada zuciyar da take matukar sonka Sabah. Kuma banjin zata iya daina sonka." Ta fada mishi kwalla na ciko mata cikin idanu. Don a yanzu haka tausayin kanta takeji.

Bata tsaya nan ba, ta cigaba da fadin "a kullum sonka dadda karuwa takeyi cikin zuciyata, Amma a duk sanda na kalli ammi na sai naji kamar banida kirki bai kamata ace na fada tarkon son dan' wanda zata aura ba. Gani nakeyi kwata kwata ban kyautata mata ba. Da wani ido zan kalli ammi idan ta gano haka? Wani irin kallo mutane zasu dinga mana? Ni nasan bazan taba daina sonka ba Sabah, nasan kanada burden sosai a rayuwarka wanda ba kowa bane yasan dashi ba, ni kaina i'm feeling helpless gani nakeyi I won't be enough for you. Ban cancanci ace ni ce nafi kowa muhimanci a cikin rayuwarka ba" Samha ta fada tana rushewa da wani irin kuka mai tsuma rai.

Wani irin tausayinta ne ya lulube Sabah yaji gabadaya shima jikinsa yayi sanyi. Hannu yasa ya janyota kusa dashi ya soma rarashinta yana fadin " shhh ki daina wanan kukan kanwata, kuma waya fada miki cewa kinfi kowa muhimanci a rayuwata?" Ya tamabayeta cike da zolaya yana mata murmushi.

Itama murmushin ta dan sake tana sheshekar kuka tace "ban sani ba. It's just that i like you too much, i want to say it out loud, kowa ma yaji".

"Then say it! Nasha fada miki ki daina bari tunanin abunda mutane zasu fadi ya dameki. Don ni a shirye nake da kowa ma ya sani". Ya fada mata yana kallon cikin kwayar idanunta.

Hannu yasa ya soma share mata hawayen dake gangarowa bisa kuncinta ya cigaba da rarashinta.

Basu sani ba, Jabbar zaune yake ta daga can kasan layi cikin motarsa yayi parking hanunsa rike da camera yayi zooming sai faman musu video yakeyi. Tun daga fitowarta, da maganganun da sukeyi, da kuma rarashinta da Sabah ya dinga yi yana share mata hawaye duk yayi recording.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now