Chapter Thirty - Nine

426 51 1
                                    

Samha tana isa broadway high school taja ta tsaya tana karewa makarantar kallo. Baban makaranta ce sosai kusan 4storey buildings kusurwa kusurwa. Ga ko ina anyi shuke shuken flowers da bishiyoyi, makarantar tayi kyau sosai, kuma daga gani private school ce.

Tana tsaye dai dai wajen shiga gate din makarantar kusan minti biyar sai ga Jabbar nan ya fito shi kadai rataye da jakan makaranta a kafadarsa.

Samha tana ganinshi da uniform din makaranta mamaki ne ya cikata, sai taga yayi mata kankanta compare to lokacin da take ganinshi cikin manya kaya a school.

cikin sauri ta karasa taje ta tadda shi ta soma fadin "Jabbar daman high school kake zuwa?"

Jabbar yana jin muryanta ya tsaya cak, bai juyo ya kalleta ba, ya bata ansa da " Toh sai meye? Sabah ne ya fada miki?"

"A'a, Ai ban fada mishi batun ka ba".

Jabbar yana jin haka ya kama hanya zai cigaba da tafiya, Samha ta dakatar dashi tana fadin "Sabah shima yayi attending wanan makarantar, anan ya gama high school dinshi. Meye halakar ka dashi ne wai? Don yanzu na gane duk saboda Sabah kaketa faman adaban rayuwata. What's the connection between you two?"

"Meyasa bakije kin sameshi kin tambayeshi ba? Kinzo kina tambayata?" Shima ya jefo mata tambaya. Yana gama fadin haka yayi gaba ya tafi ya barta tsaye a wajen. Samha bata ce komai ba ta tsaya tana bin bayansa da kallo.

Har yayi nisa, from nowhere wasu guys guda uku suka bullo suka sha gabansa, suma sanye suke da uniform irin na jikinsa.

Daya daga cikinsu ne ya hankade shi ya fadi a kasa. Jabbar ya zaro ido cike da takaici ya soma tambayarsu " what do you want now. Me na muku?"

Wanda ya tureshi ne ya soma tafa hannu ya tsuguna daidai inda Jabbar yake zaune yana fadin "wow, tambayarmu ma kakeyi me muke so?. Ashe kanada rabon cin duka kenan" ya karasa maganar yana kokarin nade hanun rigarsa.

Samha dake tsaye daga can gefe tana kallonsu, hankalinta ne ya tashi data guys din suna nade hanun rigarsu alamun suna so suyiwa Jabbar duka, babu shiri ta karaso inda suke cikin sauri tana fadin " meye haka? meya muku da zaku taru mishi haka? Jibeku fa, ko kunya baku ji".

Wanda yake tsugune kusa da Jabbar ne ya dago yana dubanta sa'anan ya bata ansa da "ke kuma ina ruwanki? Bamu san shishigi fa, nan makarantar mu ne kuma duk abunda muka ga dama zamuyi kuma babu wanda ya isa ya hanamu".

Yana gama fadin haka ya dawo da dubansa ga Jabbar yasa hannu ya soma dan marinsa a fuska yace "kai wanan guy din kana so kayi amfani da tashen da Sabah yayi a makarantar nan a da don kayi suna koh? Toh bari kaji mu gaya maka, baka isa ba indai muna makarantar nan, sai mun taka maka birki."

Hannu yasa ya soma wasa da tie din wuyan Jabbar sa'anan ya cigaba da fadin "wai tsaya ma tukuna anya kuwa Sabah Yayanka ne yanda kake kirari?"

Samha ce ta zaro ido jin abunda guy din ya fadi "Sabah ne yayan Jabbar?"

Jabbar ne ya fusata ya basu ansa da "wallahi ku jira ku gani, wata rana sai yasa kun dandana abunda kuka mun, ranan tana nan zuwa".

Dariya suka sake suna fadin "wata rana? Wace rana kenan. Muna nan jiran ranan tazo".

Jabbar bai sake cewa komai ba, mikewa yayi ya soma tafiya, da'ya daga cikinsu ne yasa hannu ya zungure mishi kai. Samha na ganin haka ta zaro ido tana kallon abunda yake faruwa a gabanta cike da mamaki.

Jabbar bai juyo ya tanka musu ba ya cigaba da tafiya. Guys din suma tsaki suka ja suka kama hanyarsu.

Jabbar har ya danyi nisa, Samha ta soma bin bayanshi cikin sauri tana kiran sunansa amma bai juyo ya tanka mata ba ya cigaba da tafiyansa.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now