Chapter Twenty-seven

533 57 0
                                    

Samha murmushin yake ta sake, ganin da gaske yake bazai kyaleta ba yasa ta soma lissafo mishi sunayen mutane "kaga akwai Zack, ga kuma Aliyah" sai kuma tayi shiru tana dubansa.

Sabah ya girgiza mata kansa sa'anan yace "mutane biyu ne kacal kowa?

"Eh toh kaga ga shinoh, Abba, da kuma Abbanka" samha ta karasa maganr tana masa kirge da hanunta.

"Saura mutum daya" ya fada yana kafeta da kyawawan idanunsa.

Samha ta bishi da kallo kirjinta ne ya fara bugu. Lalausar murmushi ya sakar mata wanda yasa dimple dinsa suka lotsa ya sake bayanar da ainin baiwar kyau da Allah yayi masa.

"Kin gama kirgen da hanun damanki, amma har yanzu banji kin lissafo suna guda daya ba, sai ki cigaba dana hagun, ina so naji waenada suke sona a nan"

Samha shiru tayi tana kallonsa da dara daran idanunta cike da karfin hali yaga ta daga hanun nata sama ta soma fadin " Harda ni ma, Samha itama tana son Sabah!" ta karasa maganar tana runtse idanunta gam

Sabah baki ya sake yana kallonta cike da mamakin kalamanta don bai taba zaton zata bude baki ta fada mishi haka ba, bai san sanda dariya ta kubuce masa yanda yaga taci serious da idanunta a rufe.

Jin dariyan daya soma yi ne yasa Samha ta bude idanunta taga sai faman dariya yake mata "wallahi kin ban dariya, ban taba ganin mutum ya daga hannu don ya fadi haka ba" ya karasa maganar yana rike cikinsa yana dariya.

Samha tayi kicin kicin da fuska ta soma turo masa dan karamin bakinta tana fadin "Shine zaka dinga mun dariya, dana sani ma da ban fada ba" ta karasa maganar tana watsa mishi harara ta soma kokarin sauke hanunta kasa.

Sabah yana ganin zata ajiye hanunta, yayi sauri yasa hanunsa ya cafke, a hankali ya soma gangaro da yatsun sa har yazo ya hade da tafin hanunta ya rike gam, yana kallon cikin kwayar idanunta.

Samha wani irin yarr taji a jikinta ta dago tana duban hanunsu daya hade wuri daya sa'anan ta dawo da dubanta gareshi, kallonta yakeyi kyawawan idanunsa na fito da wani irin sirri na daban cike da tarrin sonta, ya lumshe su a hankali ya sake budesu ya zube cikin nata. Wani irin murmushi Samha ta sakar masa, tana kallon handsome face dinsa mai mugun tafiy da imaninta a duk sanda ta kalleshi, zuciyarta fal da farin ciki ta cigaba da kallonsa tana murmushi, Sabah shima murmushin ya sakar mata ya sake matso ta kusa dashi ta fada bisa fafadar kirjinsa, yana shakkar daddar kamshin jiknta sa'anan ya rada mata cikin kunne a hankali "kanwata, naji dadin wanan kalaman naki, don sun sani farin ciki. Your like makes me the happiest". Ya karasa maganar cike da farin ciki, Samha murmushin jin dadi ta sake tana ajiyar zuciya.

Washe garin ranar ta kasance weekend basuda lectures, Samha tana zaune a dakinta tare dasu Khady da Amina waenda suka kawo mata ziyara don tunda ta kirasu a waya ta soma zayane musu yanda abubuwa suka kaya tsakaninta da Sabah suka ce sai sun zo har gida zasu ji labarin da kyau, don wanan ba labarin waya bane.

Samha zaune take a bakin gado tayi zurfi cikin tunani, babu abunda take tunani in banda Sabah da kuma kalamansa na jiya, wani irin feelings ne taji yana kara taso mata game dashi, nan take kuma taji tana missing dinshi.

Khady dake zaune kan carpet ta jingina da jikin gadon tana faman latsa wayarta ta dago ta dubi Samha wace gabadaya hankalinta baya tare dasu,  ta dawo da dubanta ga Amina suka hada ido sa'anan suka girgiza kansu a tare suna kallon Samha. Khady ta mike tazo ta zauna kusa da Samha a gado tana fadin "Kawata wanan murmushin da kike ta faman yi ke kadai fa?"

"Wai duk tunanin Sabah dine ko me?" Amina itama ta jefo mata nata tambayar tana kashe mata ido daya.

Samha gabadaya ji tayi kunya ya rufeta ta kasa cewa komai sai faman mutsu mustu takeyi kamar wace batada gaskiya.

🥀ZABIN SAMHA🌹(YAYA ko MIJI)?Where stories live. Discover now